Jon Stewart, (An haife shi ranar 28 ga watan Nuwamba, 1962). Ba'amurke ne ɗan wasan barkwanci ne, marubuci, mai shiryawa, mai bada umurni, mai sharhin akan siyasa, ɗan wasan kwaikwayo kuma mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin. Shine mai gabatar da daɗaɗɗen shirin na na The Daily Show na tashar Comedy Central daga shekarar alif ɗari tara da tisi'in da tara zuwa shekara ta dubu biyu da sha biyar Stewart ya koma yin shirin labarai na satirical a shekarar dubu biyu da ashirin da hudu. Ya shirya shirin The Problem with Jon Stewart a tashar Apple TV+ daga shekara ta 2021 zuwa 2023.