Joshua Mamman Madaki
Joshua Mamman Madaki (an haifeshi ranar 6 ga watan Yuli, 1947) a Manchok, karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.
Farkon rayuwa da Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Joshua a ranar 6 ga watan Yulin shekarar 1947 a manchok, na karamar hukumar kaura ta jihar Kaduna.
Ya halarci Kwalejin St. Paul Wusasa. Bayan ya shiga aikin soja, yana daga cikin na hudu da aka kai makarantar horas da sojoji ta Najeriya.[1]
Aikin Soja
[gyara sashe | gyara masomin]A lokacin juyin mulkin ranar 27 ga watan Agustan 1985, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya karbi mulki, Laftanar Kanar Madaki ya kasance kwamandan bataliya ta 6 ta Guards da ke Bonny Camp. An sanya bataliyarsa a jiran aiki a tsibirin Legas, kuma an bukace shi daya tabbatar da tsaron gabas zuwa tsibirin Victoria Island.
Madaki an ƙara masa girma zuwa kwamandan Brigade of Guard bayan juyin mulkin. Babangida ya karawa Madaki mukamin Kanar.[2]
Gwamnan Bauchi/Jos
[gyara sashe | gyara masomin]Tsahon shugaban kasar Nijeriya Ibrahim Babangida ne ya naɗa shi gwamnan jihar Bauchi a watan Disambar 1987- 1990 Daga nan kuma aka mayar da shi jihar Filato daga watan Agusta 1990 zuwa Janairu 1992.
Rikici
[gyara sashe | gyara masomin]An samu rikici tsakanin al’ummar Dong, Tudun Wada da Kabong a Jos ta Arewa, Jihar Filato a lokacin mulkin. ƙidayar jama'a ta 1991 wanda ya hana ƙidayar waɗannan wuraren. Kanar Madaki ya kafa hukumar shari’a domin tantance mallakar wadannan yankunan.
Ritaya
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan ya yi ritaya daga aikin soja, Madaki ya zama mamba a jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO), kungiyar ‘yan kabilar Yorubu ce mafi yawansu ke matsawa gwamnatin Sani Abacha lamba domin ya dawo mulkin dimokuradiyya.
Shugaban kwallon Rugby
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Agustan 2001 ne aka naɗa Madaki shugaban hukumar kwallon kafa ta Rugby ta Najeriya. A watan Yunin 2002, an yaɗa batun cewa yana shirin tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a watan Afrilun 2003 a jam’iyyar All People’s Party (APP), A watan Oktoba 2002, ya koma Alliance for Democracy (AD).Ya shirya yin takarar gwamnan Kaduna a cikin wannan jam'iyyar.
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Madaki ya rasu ne a wani hatsarin mota a ranar 8 ga watan Mayun 2003, lokacin da daya daga cikin tayoyin da ke jikin motarsa kirar jeep ya fashe. [3]