Josiah Sowande

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Josiah Sowande
Rayuwa
Haihuwa Abeokuta, 1858
ƙasa Mallakar Najeriya
Mutuwa 1936
Karatu
Harsuna Yarbanci
Sana'a
Sana'a maiwaƙe da Manoma

Josiah Sobowale Sowande (ca 1858 -1936) wanda aka fi sani da Sobo Arobiodu mawaƙin Yarbawa ne daga Abeokuta, Jihar Ogun wanda ya kasance mawallafi na farko na Ewi, salon waƙar Yarbawa.[1]

Tarbiyar Egba da ayyukan kungiyar mishan na Kirista a Egbaland da kuma rera wakokin Egba sun rinjayi ayyukansa, ayyukansa sun fi mayar da hankali kan tubabbun Kiristocin Egba a matsayin masu sauraro na farko.[2]

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sobowale a Abeokuta, ca 1858. Ya koyi rubutu a cibiyar horar da CMS amma bai kammala karatunsa ba ya samu aiki a matsayin mai gadin gidan yari a gwamnatin Egba. Ya bar mukaminsa na mai gadi ya fara aikin noma da rubutu. Tsakanin shekarun 1905 zuwa 1934, an buga ayyukansa guda goma sha biyu, wasu daga mawallafin gwamnati na Egba inda ɗan’uwansa ya yi aiki.[3]

Ayyukan Sowande sun haɗa da Orin Arungbe, waƙar baka da ƙungiyar daba ke amfani da ita.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Nnodim, Rita (2006). "Configuring Audiences in Yorùbá Novels, Print and Media Poetry". Research in African Literatures. 37 (3): 154–156. ISSN 0034-5210.
  2. Okùnoyè, Oyèníyì (2010). "Ewì, Yorùbá Modernity, and the Public Space". Research in African Literatures. 41 (4): 43–64. doi:10.2979/ral.2010.41.4.43. ISSN 0034-5210.
  3. Babalola, Adeboye (1985). Andrzejewski, B.W.; Piłaszewicz, Stanisłav; Tyloch, Witold (eds.). Literatures in African languages : theoretical issues and sample surveys [Yoruba Literature]. Cambridge: Cambridge University Press. pp. 184–186. ISBN 0-521-25646-1. OCLC 10824164.