Kabafest
Appearance
Iri |
maimaita aukuwa biki |
---|---|
Kwanan watan | 2017 – |
Wuri | Jahar Kaduna |
Ƙasa | Najeriya |
Bikin baje kolin Littafai da zane-zane na garin Kaduna da ake kira da Kabafest. Wannan wani biki ne dake gudana a garin Kaduna duk shekara, anfara kaddamar dashi ne a shekarar 2017 a Gusau Institute, inda aka gayyaci shahararrun marubuta daga ko ina a duniya kamar Leila Aboulela, Kinna Likimani, Lola Shoneyin, Kadaria Ahmed, Abubukar Adam dadai sauransu, biki ne mai kayatarwa da wayar dakai musamman akan abubuwan dake kawo cigaban al'umma da ilimi, da al'adu masu amfani. Gwamnatin jihar Kaduna itace ke daukan nauyin bikin tare da kamfanoni wadanda suke taimakawa, hakama uwargidan gwamnan wato Hajiya Hadiza Isma El-Rufai itama tana daga cikin masu ganin cigaban bikin.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.