Kemi Nelson
Kemi Nelson | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Lagos,, 9 ga Faburairu, 1956 |
Mutuwa | 17 ga Yuli, 2022 |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Olukemi Nelson (an haife ta ranar 9 ga watan Fabrairun 1956).[1] 'yar siyasan Najeriya ce kuma mai son mu'amala da jama'a.[2][3] Ita ce Babbar Darakta ta Asusun Kula da Inshorar Jama'a ta Najeriya (NSTIF).[3][4]
Kuruciya da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Nelson a birnin Legas a ranar 9 ga watan Fabrairun 1956 kuma ta halarci Makarantar Grammar Girls na Anglican, Ijebu-Ode inda tayi karatun ta na sakandare. Dangane da karatun ta na jami'a kuwa, ta halarci makarantar koyon aikin jinya a asibitin kwalejin jami’ar Ibadan inda ta cancanci zama ma’aikaciyar jinya/kula da maras lafiya da ungozoma.[5][6] Ta samu digirin MBA a fannin hada-hadar kuɗi da difloma a fannin shari’a daga Jami’ar Jihar Legas Ojo.[6]
Ayyukan siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin 1980s, Nelson ta shiga tsohuwar jam'iyyar National Republican Convention (NRC) a zamanin mulkin Janar Ibrahim Babangida. Ta kasance ‘yar takarar sanata mai wakiltar Legas ta yamma a shekarar 1992 kuma Bola Ahmed Tinubu ya kayar da ita a zaben.[6]
A shekarar 1998, a lokacin mulkin Janar Abacha, ta tsaya takarar Mazaɓar tarayya ta Ikeja a majalisar dokoki. A wannan karon, a matsayin memba na UNCP. Ita ce ta ci zaben amma mutuwar Janar Abacha ta yasa aka watsar da nasarar.[6]
A shekarar 1999 ta shiga kungiyar Alliance for Democracy (AD) sannan daga 1999 zuwa 2003 ta rike kwamishinan harkokin mata da rage radadin talauci na jihar Legas a zamanin Bola Ahmed Tinubu kuma ta rike mukamin shugabar mata na reshen jihar Legas. Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma daga baya ta zama shugabar matan Kudu maso Yamma a karkashin jam'iyyar APC.[2]
Ita ce kaɗai mace tilo da ke aiki a Majalisar Shawarar Gwamnan Jihar Legas (GAC).[2]
Ita ce Babbar Daraktar Ayyuka ta Asusun Tallafawa Inshorar wato, "Operations of the Nigeria Social Insurance Trust Fund" (NSITF) kuma a baya ta shugabanci ma’aikatar habakawa, horarwa da samar da ayyukan yi (Ministry of Establishment, Training and Job Creation).[1][7][8]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Tana auren Adeyemi Nelson,[9] darekta mai ritaya na ma’aikatar cikin gida ta tarayya. Sun yi aure a shekara ta 1987 kuma sun haifi 'ya'ya uku tare. An san ta da ƙarancin gashi da take yankewa da kayan kwalliyar gashin ta na musamman.[6][10]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Ricketts, Olushola. "Again, Kemi Nelson opts for low-key birthday". The Nation.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Raphael. "Lagos political bigwigs celebrate Kemi Nelson". The Sun (Nigeria).
- ↑ 3.0 3.1 Akinwale, Funsho. "Kemi Nelson gets federal appointment". The Guardian (Nigeria). Retrieved 9 March 2021.
- ↑ "Ojekunle, Aderemi (3 August 2019). "31 of the most high-profile female appointees in Buhari's government". Pulse Nigeria. Retrieved 9 March 2021.
- ↑ "CHIEF (MRS) OLUKEMI NELSON". Pro-Health HMO. Retrieved 6 March 2021.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 6.3 6.4 "Abatti, Tolani (16 February 2016). "Kemi Nelson turns 60, disappoints friends". Encomium. Retrieved 9 March 2021.
- ↑ Oguntoye, Isaac. "Kemi Nelson marks 64th birthday with close friends". Punch Nigeria.
- ↑ "Sessou, Aisha (21 March 2019). "Amazing 31 women who made list in President Buhari's second term". Vanguard (Nigeria). Retrieved 12 March 2021.
- ↑ "When Kemi Nelson's son wedded (2)". Encomium Magazine. 7 December 2013. Retrieved 22 July 2021.
- ↑ "(Video): Buhari pays special tribute to Kemi Nelson in Aso Rock | Express Day". 26 November 2020. Retrieved 9 March 2021.