Kisan gilla a Gwoza

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKisan gilla a Gwoza

Map
 11°05′36″N 13°49′14″E / 11.0933°N 13.8206°E / 11.0933; 13.8206
Iri aukuwa
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 2 ga Yuni, 2014
Wuri Gwoza
Adadin waɗanda suka rasu 200

Kisan gillar na Gwoza wani lamari ne na ta'addanci da ya faru a ranar 2 ga watan Yuni, shekarar 2014 a karamar hukumar Gwoza, jihar Borno kusa da kan iyakar kasar Najeriya da Kamaru.

Hari[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu ‘yan bindiga (watakila ƴan Boko Haram ne) sanye da kayan sojoji sun kashe ɗaruruwan fararen hula a ƙauyukan; Goshe, Attagara, Agapalwa da Aganjara. Wasu majiyoyi masu inganci sun ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 400 zuwa 500.[1][2]

Wani shugaban al’ummar da ya shaida kisan a ranar Litinin, ya ce mazauna yankin sun roƙi sojoji su taimaka, amma abin bai zo kan lokaci ba. Sai da aka kwashe kwanaki ana jin labarin waɗanda suka tsira kafin su isa babban birnin lardin Maiduguri, saboda hanyoyin na da matukar haɗari, kuma hanyoyin sadarwa ba su da kyau ko kuma babu su, saboda dokar ta-baci da aka kafa a jihar Borno kimanin shekara guda kenan. Mohammed Ali Ndume, Sanata mai wakiltar jihar Borno, kuma garinsa Gwoza ne, da kuma wani babban jami’in tsaro a Maiduguri, wanda ya dage a sakaya sunansa ya tabbatar da kisan.[3]

Rahotanni[gyara sashe | gyara masomin]

Majiyoyi da dama da suka shaida abin da ya faru sun bayyana cewa an kai hari ga yara da samari a waɗannan hare-haren. A cewar wani ganau, "Lokacin da wasu daga cikin mutanen ƙauyen suka tsere, sai aka yi rashin sa'a wasu ƴan bindiga a kan babura suka hango su a wajen kauyukan, inda suka kama yara da matasa maza su ka yanka su, sai kawai mata da yara ƙanana suka ƙyale, su tafi."[4] Wata majiyar kuma ta bayyana cewa iyaye mata an ɗauke musu jariransu maza aka harbe su.[5]

Hakan ya biyo bayan kisan da aka yiwa shugaban musulmi Alhaji Idrissa Timta, Sarkin garin Gwoza, a karshen watan Mayu.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Reports: Boko Haram village raids kill hundreds in Nigeria. By Aminu Abubakar, June 5, 2014.
  2. Bodies litter streets after Boko Haram massacre, 2014-06-06 07:54. News24 Nigeria.
  3. Boko Haram Militants Dressed as Soldiers Slaughter Scores: Witnesses. NBC News website. June 5, 2014, 4:15 AM.
  4. Abdullahi Umar (June 5, 2014). "Nigeria: Gwoza Under Siege - Boko Haram Kills 2000, Wipes Out Three Villages". AllAfrica.com.
  5. Aminu Abubakar (June 5, 2014). "Reports: Boko Haram village raids kill hundreds in Nigeria". CNN.
  6. Grossman, Laura (30 May 2014). "Boko Haram kills local Muslim leader". Long War Journal. Retrieved 31 May 2014.

Coordinates: 11°05′36″N 13°49′14″E / 11.0933°N 13.8206°E / 11.0933; 13.8206