Jump to content

Kisan kiyashi na Monguno da Nganzai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKisan kiyashi na Monguno da Nganzai
Iri Kisan Kiyashi
Kwanan watan 13 ga Yuni, 2020

A ranar goma Sha uku 13 ga Yuni, 2020, Daular Musulunci – Yammacin Afirka (ISWAP) ta ƙaddamar da hare-hare guda biyar a wasu wurare daban-daban a fadin jihar Borno, Najeriya . Huɗu daga cikin hare-haren an kai su ne a Monguno, ɗaya kuma ya faru ne a kauyen Goni Usmanti da ke ƙaramar hukumar Nganzai, kuma an kashe sama da mutane sittin a hare-haren.

Kwanaki kaɗan kafin hare-haren Monguno da Nganzai, an kashe mutane tamanin da ɗaya a wani kisan gilla da ISWAP ta yi a Gubio a ranar Tara 9 ga watan Yuni. [1] Harin dai na ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni a shekarun baya bayan nan da ƙungiyar Boko Haram ta kai, kuma Abu Musab al-Barnawi, wanda ya ɓalle daga ƙungiyar Boko Haram a baya-bayan nan ya kai ƙungiyar IS daular Islama – yammacin Afrika (ISWAP). [1]

Kisan gilla

[gyara sashe | gyara masomin]

Harin farko ya fara ne a Goni Usmanti, dake ƙaramar hukumar Nganzai, inda mayakan ISWAP suka yi ta harbe-harbe a lokacin da suke shiga cikin birnin. [2] A ƙauyen, mayaƙan sun yi arangama da ƴan banga na yankin, amma da sauri mayaƙan jihadi suka mamaye mutanen yankin. Daga nan ne suka buɗe wuta kan wata babbar motar da ke jigilar ƴan kasuwa, inda suka ƙona motar da mutane da dama a ciki. Mutane biyu ne kawai suka tsira ta hanyar tsalle daga motar. [2] Mayaƙan jihadin sun gudu daga Goni Usmanti lokacin da suka hango jerin gwanon motocin sojojin Najeriya daga Gubio, inda suka far wa ƙauyen Mainmari a lokacin da suke ja da baya. [3] Sun kuma ƙona ƙauyen Mariram. [3] An kashe fararen hula 29 a Goni Usmanti, sannan an kashe wasu goma sha uku a Mainmari. [3]

Da misalin ƙarfe 11:50 na safe, wannan gungun mayaƙan ISWAP sun shiga Monguno ta hanyar shiga Charly 1 da Charly 6, inda suka harba rokoki da harsasai kan masu gadi. [3] An kai hari kan shingayen binciken ababan hawa biyu na sojojin Najeriya a birnin da misalin ƙarfe 12:30 na rana, lamarin da ya kai ga yin artabu tsakanin sojojin hadin gwiwa na MNJTF da mayaƙan jihadi a birnin. Rikicin da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu ya jikkata tare da kashe fararen hula. [3] [4] Sojojin MNJTF sun yi galaba a kansu, kuma mayaƙan ISWAP sun yi ta yawo a Monguno na ‘yan sa’o’i. [4] Mayaƙan jihadi sun isa tsakiyar Monguno da misalin ƙarfe 3:13 na rana, inda suka ƙona wata cibiyar jin ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Monguno, inda suka raba wa fararen hula takardu da ke gargaɗin kada su yi aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu na Yamma.[5][6] Ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya 50 ne ke wurin a yayin harin, amma ba su samu rauni ba. [5] Daga nan ne mayaƙan na ISWAP suka ƙona ofishin ‘yan sanda. [7]

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta ce ta yi nasarar daƙile harin Monguno tare da kashe mayaƙan jihadi ashirin. Ba a ambaci harin da aka kai a ƙaramar hukumar Nganzai ba. A Monguno, an kashe sojojin Najeriya 20 tare da kashe fararen hula aƙalla goma sha biyar. [5] [4] Fararen hula da suka jikkata sun mamaye asibitin da ke Nganzai, inda aka tilastawa wasu kwanciya a wajen asibitin. [5] An kai sha shida 16 daga cikin fararen hula da suka jikkata a Monguno zuwa asibiti a Maiduguri a ranar 16 ga watan Yuni, duk da cewa ɗaya ya rasu a kan hanya. [8]

Majalisar Ɗinkin Duniya ta jajanta wa waɗanda harin ya rutsa da su. [9]

  1. 1.0 1.1 "Fighters kill dozens, raze village in Nigeria's Borno state". Al Jazeera (in Turanci). Retrieved 2024-03-07.
  2. 2.0 2.1 "String of apparent jihadist attacks kills dozens in northeast Nigeria". France 24 (in Turanci). 2020-06-14. Retrieved 2024-03-07.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 "BOKO HARAM/ISWAP - AN IN-DEPTH ANALYSIS OF RECENT CIVILIAN SOFT TARGET ATTACKS". EONS Intelligence (in Turanci). Retrieved 2024-03-07.
  4. 4.0 4.1 4.2 "20 soldiers, 40 civilians killed in attacks Nigeria's Borno state". Al Jazeera (in Turanci). Retrieved 2024-03-07.
  5. 5.0 5.1 5.2 5.3 "Nigeria's Boko Haram crisis: UN 'appalled' by twin jihadist attacks in Borno" (in Turanci). 2020-06-14. Retrieved 2024-03-07.
  6. "BLACK SATURDAY: Boko Haram, ISWAP attacks leave 60 dead in Borno". Vanguard News. June 13, 2020. Retrieved March 7, 2024.
  7. "Militants Kill 20 Soldiers, 40 Civilians in Northeast Nigeria Attacks". Voice of America (in Turanci). 2020-06-13. Retrieved 2024-03-07.
  8. "Operational update on Monguno attack: 16 civilians evacuated to Maiduguri for surgical care". International Committee of the Red Cross (in Turanci). 2020-06-15. Retrieved 2024-03-07.
  9. "Statement attributable to the Spokesman for the Secretary-General - on attacks in Borno State, Northern Nigeria | United Nations Secretary-General". www.un.org. Retrieved 2024-03-07.