Rundunar Haɗin gwiwa ta Ƙasashen Duniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rundunar Haɗin gwiwa ta Ƙasashen Duniya
multinational military coalition (en) Fassara da military task force (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1994
Sunan hukuma Multinational Joint Task Force
Rikici Rikicin Boko Haram
Shafin yanar gizo mnjtffmm.org
Wuri
Map
 12°07′N 15°03′E / 12.11°N 15.05°E / 12.11; 15.05

Rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force ( MNJTF ), runduna ce ta kasa da kasa baki daya, rundunar ta kunshi, galibin sojoji, daga kasashe kamar su; Benin, Kamaru, Cadi, Nijar, da Najeriya. Tana da hedikwata a birnin N'Djamena kuma an ba ta damar kawo karshen ta'addancin Boko Haram.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An fara shirya wannan tawaga ne a matsayin rundunar Najeriya kadai a shekara ta 1994, a lokacin gwamnatin Sani Abacha, domin "binciko ayyukan 'yan fashi da kuma saukaka zirga-zirga" a kan iyakarta ta arewa.[1][2] A cikin shekara ta 1998 an fadada rundunar ta hanyar hada ta da rundunoni daga kasashen Chadi da Nijar da ke makwabtaka da Nijar da nufin tunkarar matsalolin tsaro a yankin tafkin Chadi, wadda ke da hedkwatarta a garin Baga na jihar Borno.[2]

Kungiyoyi masu ikirarin kishin Islama sun girma kuma sun fadada ayyukansu a cikin shekarun 2000s da farkon 2010s. Daman dai tun a shekara ta 2009 ne rikicin Boko Haram ya soma, kuma jami'an tsaro a yankin na kara fuskantar kalubale kai tsaye daga kungiyoyin 'yan jihadin . Kungiyoyin Boko Haram da Ansaru sune suka fi kowa aiki kuma sanannu. A cikin watan Afrilun 2012, an ƙara inganta rundunar ta MNJTF, izuwa ayyukan yaƙi da ta'addanci.[2]

Brig. Gen. Enitan Ransome-Kuti, dan Beko Ransome-Kuti kuma dan wan mawakin nan Fela Kuti ya taba zama kwamandan rundunar a baya.[1]

Ci gaba[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Janairun shekarar 2015 ne hedikwatar MNJTF da ke Baga a Najeriya, mayakan Boko Haram su ka mamaye hedikwatar, inda suka ci gaba da yiwa mazauna yankin kisan kiyashi[2][3] tare da lalata garin, gami da raba mazauna yankin da dama daga matsugunnan su.[4] A lokacin sojojin Najeriya ne kawai suke a hedkwatar a garin. Rahotanni sun ce suma (sojojin) sun tserewa maharan.[5] Wannan lokaci ne na wulakanci ga rundunar MNJTF, da kuma al'ummomin da ke ba da gudummawa. An ba wa tsarin siyasa na fadada MNJTF sabon karfi da kuzari wanda ya haifar da ci gaba cikin sauri, gami da kara adadin sojoji, da mayar da hedikwatar HQ zuwa birnin N'Djamena, na kasar Chadi.[6][7]

Babban sauye-sauyen tsarin MNJTF da aka samu a tarurrukan shekarar 2015 sun hada da karuwar lambobi, da samar da wani sabon ra'ayi na ayyuka karkashin kulawar hukumar kula da tafkin Chadi, da kuma tafiyar da hedikwatar hukumar zuwa N'Djamena. An amince da cewa wani jami'in Najeriya ne zai zama kwamandan rundunar soji na tsawon lokacin aikin yaki da yan kungiyar na Boko Haram, tare da dan Kamaru a matsayin mataimakin kwamanda da kuma babban hafsan sojojin Chadi. An nada Manjo-Janar Tukur Yusuf Buratai (na Najeriya) Kwamandan rundunar ta MNJTF na farko a watan Mayun shekara ta 2015. [8] Sai dai kuma kwamandancin nasa bai dade ba domin a watan Yulin 2015 aka nada shi a matsayin hafsan hafsoshin sojin Najeriya, aka kuma mika mukamin na buratai, ga Manjo-Janar Iliya Abbah (dan Najeriya) a ranar 31 ga Yuli 2015. [9] Manjo-Janar Lamidi Adeosun (dan Najeriya), an nada shi Kwamandan MNJTF a watan Janairun 2016. [10] An maye gurbin Adeosun a matsayin kwamanda da Manjo-Janar Lucky Irabor a watan Mayu 2017. [11] A watan Agusta 2018, Manjo-Janar CO Ude[12] ya maye gurbin Irabor. Manjo Janar IM Yusuf ya karbi mulki daga hannun Ude, yayin da kwamandan na yanzu Maj Gen JJ Ogunlade ya karbi ragamar mulki daga hannun yusuf a ranar 19 ga watan Maris.[13]

An tsara rundunar a sassa hudu na kasa acikin tsarin wasu rukunnai masu zuwa: Sector 1 (Kamaru) mai hedikwata a Mora; Sector 2 (Chadi) mai hedikwata a Baga-Sola; Sashi na uku (Najeriya) dake garin Baga; da kuma Sector 4 (Nijar), dake garin Diffa. [14]

Har yanzu akwai babban shakku a tsakanin kasashen duniya kan cewa sabuwar rundunar za ta iya samar da sakamako mai kyau,[15] kuma za a sanya ido sosai kan nasarar da ta samu ko akasin haka a matsayinta na rundunar kasa da kasa.[16] Shugaban kasar Chadi Idriss Déby, ya bayyana rashin jin dadinsa a cikin kawancen hadin gwiwar saboda daukar nauyin da bai dace ba na yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai tare da sanar da killace ayyukan soji a kan iyakokinta.[17][18]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 Musa, Sagir (7 May 2015). "Multinational Joint Task Forces, BHTs And Host Community". Sahara Reporters. Retrieved 9 January 2015.
 2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "Boko Haram suffers heavy defeat in surprise attack on military base". News Express. 5 January 2015. Archived from the original on 7 August 2017. Retrieved 9 January 2015.
 3. "BBC News - Boko Haram attack: What happened in Baga?". BBC News. 2 February 2015. Retrieved 11 February 2016.
 4. "Boko Haram displaces 1,636 in Baga". News Express. 7 January 2015. Archived from the original on 5 June 2015. Retrieved 9 January 2015.
 5. Roggio, Bill (4 January 2015). "Boko Haram overruns Multinational Joint Task Force base". Long War Journal. Retrieved 8 January 2015.
 6. Tchioffo Kodjo. "Experts Meeting on the elaboration of operational documents for the Multinational Joint Task Force (MNJTF) of the Member States of the Lake Chad Basin Commission and Benin against the Boko Haram terrorist group -African Union - Peace and Security Department". African Union,Peace and Security Department. Retrieved 11 February 2016.
 7. "PSC Report - PSC to approve final plans for the regional fight against Boko Haram". ISS Africa. Archived from the original on 30 June 2015. Retrieved 11 February 2016.
 8. Iroegbu, S. (2015) 'Military General Appointed Commander of the MNJTF', This Day (Lagos), 3 June 2015.
 9. Iroegbu, S. (2015) 'Buratai Hands Over MNJTF Command to Abbah', This Day (Lagos), 1 August 2015.
 10. 'New Commander for Troops Fighting Boko Haram Assumes Duty', Premium Times (Abuja), 4 January 2016.
 11. Omonobi, K., Marama, N. & Erunke, J. (2017) 'Massive Shake-Up in Army', Vanguard (Lagos), 11 May 2017.
 12. Antigha, Timothy (2018-08-19). "General Ude Assumes Duty in MNJTF". PRNigeria News (in Turanci). Retrieved 2018-12-29.
 13. 21.https://globalsentinelng.com/2021/03/19/ogunlade-takes-over-as-mnjtf-commander/
 14. Assanvo, W., Abatan, J.E.A. & Sawadogo, W.A. (2016) Assessing the Multinational Joint Task Force against Boko Haram. West Africa Report issue 19, Institute for Security Studies, Pretoria, https://issafrica.s3.amazonaws.com/site/uploads/war19.pdf
 15. Peter Dörrie (30 January 2015). "The African Union Readies an Army to Fight Boko Haram — War Is Boring". Medium. Retrieved 11 February 2016.
 16. "A Regional Multinational Joint Task Force to Combat Boko Haram". Retrieved 11 February 2016.
 17. "Chad to stop participating in regional fight against armed groups". www.aljazeera.com. Retrieved 2020-04-12.
 18. "Chadian troops 'kill 1,000 Boko Haram fighters' in Lake Chad". www.aljazeera.com. Retrieved 2020-04-12.