Tukur Yusuf Buratai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Tukur Yusuf Buratai Laftanar Janar din soja ne a Najariya kuma shugaban sojojin kasan Najeriya, matsayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a 2015.

Tarihin sa da karatun sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Janar Buratai an haifeshi a garin Buratai, karamar hukumar Biu ta jahar Borno. Mahaifinsa Yusuf Buratai ma tshon soja ne na Royal West African Frontier Force da kuma Yakin duniya na biyu inda yayi yaki a kasar Burma. Buratai yayi karatunsa na firamare a garin Buratai daga nan kuma ya samu takarar shiga makarantar horar da malamai ta garin Potiskum dake jahar Yobe, inda ya kammala da kyakkyawab sakamako.

Shiga Aikin Soja[gyara sashe | Gyara masomin]

A watana janairu na 1981, Buaratai ya shiga makarantar horar da sojoji dake garin Kaduna. Sakamakon gwaggwabar nasarar da ya sanu ta kammalawa ne sai ya samu matsayin Laftanar na biyu a ranar 17 ga Disamba na 1983 a cikin Kuratan sojojin Najeriya. Buratai yayi digiri a fannin ilimin tarihi a jami'ar Maiduguri da kuma wani digirin a fannin falsafa daga jami'ar kwararru ta kasar Bangalidash wato Bangladesh University of Professionals, Dhaka. Ya kuma yi karatu a makaranatr National Defence college, Mirpur, duka a kasar ta Bangalidash.

Ya shiga bataliayar matasan sojoji ta 26 a garin Elele dake Fatakwal, sai kuma mai nazari na harkar soja cikin rundunar sojoji ta majalisar dinkin duniya a kasar Angola, daga baya kuma sai yakoma bataliayar sojojin tsaro a 26 a Lagos wato Lagosa Garroson command Camp. Laftanar Janar Buratai kuma ya rike mukamin mai tafiyarwa na gidan yankin jaha a Abuja; wato 82 Motoruzed Batalion; sai 81 Balation, Bakasi Penninsular; Army Headquaters Garrison, Abuja kafin daga baya kuma sai yazama daraktan ma'aikata a kwalejin horon mayan jami'an soja dake Jaji.

Ya kuma rike makamai kamar haka; AHQ Army Policy and Plans, Abuja; Mataimakin Shugaban tsare tsare na al'amuran gudabarwa, HQ Infantry Centre Jaji. Yadai rike mukamai da dama a bangarori daban daban.

Ranakun da ya samu karin girma[gyara sashe | Gyara masomin]

Lambobin yabon daya samu[gyara sashe | Gyara masomin]