Kyautar Jarumin daji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

An kafa lambar yabo ta gwarzon daji na Majalisar Ɗinkin Duniya acikin 2011, shekarar dazuzzuka ta duniya, don karrama mutanen da suka sadaukar da rayuwar su don kare gandun daji. Ana bada kyaututtuka a kowace shekara ga mutum ɗaya, acikin kowane yankuna biyar: Afirka, Asiya da Pacific, Turai, Latin Amurka da Caribbean, da Arewacin Amurka.

2011[gyara sashe | gyara masomin]

An sanar da waɗanda sukayi nasara a 2011 a taron Majalisar Ɗinkin Duniya, kan dazuzzuka na 2012 a New York. Wanda aka zaɓa daga cikin mutane 90 da aka zaɓa a ƙasashe 41, waɗanda suka yi nasara sune:

  • Afirka : Paul Nzegha Mzeka, Kamaru
  • Asiya da Pacific : Shigeatsu Hatakeyama, Japan
  • Turai : Anatoly Lebedev, Rasha
  • Latin Amurka da Caribbean : Paulo Adario, Brazil
  • Arewacin Amurka : Rhiannon Tomtishen da Madison Vorva, Amurka don nasarar yakin da suka yi na cire dabino daga Cookies Scout

An ba da lambar yabo ta musamman ga aikin wasu ma’aurata da suka rasu, José Claudio Ribeiro da Maria do Espírito Santo, Brazil.

2012[gyara sashe | gyara masomin]

Wadanda suka yi nasara a shekarar 2012 sune:

  • Afirka : Rose Mukankomeje, Rwanda
  • Asiya da Pacific : Preecha Siri, Thailand
  • Turai : Hayrettin Karaca, Turkiyya
  • Latin Amurka da Caribbean : Almir Narayamoga Surui, Brazil
  • Arewacin Amurka : Ariel Lugo, Puerto Rico

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Zakarun Duniya
  • Jaruman Muhalli
  • Jerin lambobin yabo na muhalli

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]