Lisabi: Tashin hankali
Lisabi: Tashin Hankali fim ne na wasan kwaikwayo na tarihi na Najeriya na Shekarar 2024 wanda Niyi Akinmolayan ya jagoranta, wanda Adebimpe Oyebade da Victoria Akujobi suka samar, kuma Yinka Olaoye da Niyi Akin molayan ne suka rubuta shi. Ya ƙunshi ƙungiyar da Lateef Adedimeji, Adebimpe Oyebade, Ibrahim Chatta, Jide Awobona, Eniola Ajao , da Olumide Oworu suka jagoranta. Ya samo asali ne daga tarihin Lisabi Rebellion na ƙarshen karni na 18 a Abeokuta, Najeriya, yana ba da labarin Lisabi Agbongbo Akala, jarumin Egba wanda ya jagoranci nasarar taawaye a kan mulkin zalunci na Daular Oyo.
Kirkira
[gyara sashe | gyara masomin]Lisabi, shugaba mai ƙuduri wanda ya tashi cikin tawali'u don jagorantar mutanen Egba a cikin gwagwarmayar da suka yi don samun 'yanci daga mulkin zalunci na Daular Oyo. Labarin ya fara ne da Sarki Olodan, wanda bayan ya ki biyan haraji mai nauyi da Alaafin ya nema, wanda hakan yasa aka mishi duka da kuma jimishi mummunan rauni sa'a nan kuma aka ja shi zuwa fada. Kyauta, wacce ta kunshi kudi da kayan gona, ana karbar su da karfi ne daga kasuwancin da mutane suka samu. Da yake fushi da taawaye na Olodan, Alaafin na Oyo (wanda Odunlade Adekola ya taka rawar), ya ba da umarnin a kashe shi, don hakan ya ama izna ga duk wanda ya yi ƙarfin halin tirjiya.
Songodeyi, shugaban masu karɓar haraji mara tausayi, tare da magoya bayansa akan zalunci, suna tsoratar da Mutanen Egba, duk da biyan bukatun haraji. Rashin tausayin su ba shi da iyaka - suna ɗaukar fiye da abin da suke bi, suna yi wa 'yan mata fyade, kuma su kashe duk wanda ya yi tirjiya akan zaluncin su. Yayin da zaluncin su ke kara muni kowace rana, rayuwa ta yi tsanani ga manoma da mazauna ƙauyen ƙasar Egba.
Oshokenu, babban abokin Lisabi manomi mai aiki tuƙuru, ya shaida wani abin damuwa inda masu karbar haraji, bayan sun kwace duk kuɗin wata 'yar kasuwa, suka ɗauki 'yarta. Fushi da zaluncin su, yasa Oshokenu ya yi tambaya game da rashin adalci, yana tambaya, "Me ya sa kuke ɗaukan mata kawai maza ma su bi su". Don rashin amincewarsa, masu karɓar harajin sun azabtar da shi da zalunci, suna mishi zane a fuskarsa cikin nuni da ikon su a fili.
Ko da yake an san shi da malalacin manomi, Oshokenu yana neman ya auri Abebi (wanda Liquorose ta taka rawar), kyakkyawar mace mai haken launin fata yar Egba. Da taimakon Lisabi, ya sami nasarar samun soyayyar ta, kuma Abebi ta yarda da auren. Amma, Songodeyi da mutanensa, sun ƙudurci aniyar murkushe ruhun Oshokenu, sun dadaici ranar bikin aurensa. Yayin da Abebi ke tafiya zuwa sabon gidanta, Songodeyi ya yi mata kwanton bauna kuma ya yi mata fyade. Cikin bakin cikii da kunya, Abebi ta kashe kanta.
Fushi da makomar Abebi, yasa Oshokenu ya fara aiki don daukan fansa. A cikin gwabzawa mai ban mamaki, ya sami nasarar kashe goma daga cikin masu karɓar haraji kafin aka harbe shi. Yayin da yake kwance yana magagin mutuwa, Lisabi ya isa wurin.,Da numfashinsa na ƙarshe, Oshokenu ya roki abokinsa. Sabida bukatar abokinsa na karshe kafin ya mutu, Lisabi ya dauki nauyin jagorantar mutanen Egba a cikin gwagwarmayarsu don neman adalci. Ya tsara wani shiri ga manoma akan su yi aiki tare a kokarin noma na al'umma, yana ba da gizo na hadin kai da bin doka don kauce wa tuhuma daga sojojin Oyo. Amma fa, a ƙarƙashin wannan shiri, Lisabi yana da babbar kudiri na - haɗa kan mutanen Egba don cikakken tawaye a kan masu zaluntar su.
Da dabarunsa da jagoranci, Lisabi ya kafa kungiyar Aaro, ƙungiyar aiki ta al'umma wacce a asirce ta zama tushen tirjiya. Yayin da aka samu tashin hankali tsakanin Egba da iyayengijinsu na Oyo, Lisabi ta shirya tawaye a ɓoye. Tashin hankali ya kai ga ƙololuwa a cikin jerin yaƙe-yaƙe masu tsanani da ban mamaki, inda Egba ta sami nasarar hambarar da sojojin Oyo, ta tabbatar da 'yancin kai da ake jira.
Tawayen Lisabi ya zama mafarin canji a tarihin Egba, yayin da yake jagorantar mutanensa zuwa nasara da 'yanci daga mulkin Daular Oyo, yana tabbatar da gadonsa a matsayin jarumi da mai 'yanci.
Jarumai
[gyara sashe | gyara masomin]
- Lateef Adedimeji a matsayin Lisabi Agbongbo Akala [1]
- Ibrahim Chatta a matsayin Songodeyi
- Adebowale Adedayo a matsayin Osokenu
- Odunlade Adekola a matsayin Alaafin na Oyo (Oloyo)
- Femi Adebayo a matsayin Olu Olodan
- Roseline Afije "Liquorose" a matsayin Abebi
- Oyebade Adebimpe Adedimeji a matsayin Ikeola
- Ibrahim Yekini Icon a matsayin Salako
- Olarotimi Michael Fakunle a matsayin Ogunlana
- Jide Awobona a matsayin Osobande
- Gabriel Afolayan a matsayin Odunbamitefa
- Kola Ajeyemi a matsayin Akinolu
- Boma Akpore a matsayin Osogbenro
- Olumide Oworu a matsayin Bejide
- Kevin Ikeduba a matsayin Obimodede
- Seun Akindele a matsayin Oduyale
- Muyiwa Ademola a matsayin Alake
- Jide Kosoko a matsayin Onitumọ
- Atobiloye Kelvin a matsayin Akilapa
- Efe Irele a matsayin Idon
- Seun Ajayi a matsayin Olo Olori Ilari
- Damilola Ogunsi a matsayin Jogbo
- Eniola T. Ajao a matsayin Orosola
- Deyemi Okanlawon a matsayin Sabon Janar (Aronimoja)
- Jaiye Kuti a matsayin Edioke
Kira
[gyara sashe | gyara masomin]Kirkirar Lisabi: An Tirjiya a wurare daban-daban a fadin Najeriya, har da Abeokuta da yankunan da ke kewaye da ita. Masu kirar sun ba da fifiko ga ainihin kirkirar yanayi na zamanin kafin Mulkin mallaka na turawa, na kudu maso yammacin Najeriya, ta amfani da kayan da aka tsara da kyau don kaman ceceniya da lokacin tarihi. Darakta Niyi Akinmolayan, wanda aka sani da fina-finai kamar The Wedding Party 2 (2017), Chief Daddy (2018), Prophetess (2021), My Village People (2021), da The Set Up (2019), ya bayyana cewa duk ma'aikatan samarwa sun kunshi 'yan Najeriya. Al Notions Studios da Anthill Studios ne suka samar da fim din, tare da Oyebade Adebimpe Adedimeji, Victoria Akujobi, da Lateef Adedimeji suna aiki a matsayin masu samarwa.[2]
Kamfanin Fim na Najeriya da sauran kungiyoyin al'adu sun goyi bayan fim din da nufin inganta tarihin Najeriya da al'adun ga masu sauraro a duniya.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ BellaNaija.com (21 August 2024). ""Lisabi": Adedimeji Lateef's Star-Studded Biopic Set to Reconnect Audiences with Yoruba Heritage". BellaNaija (in Turanci). Archived from the original on 27 September 2024. Retrieved 28 September 2024.
- ↑ Udugba, Anthony (9 September 2024). "All-Nigerian crew on 'Lisabi' challenges Nollywood's reliance on foreign expertise". Businessday NG (in Turanci). Archived from the original on 19 September 2024. Retrieved 29 September 2024.
- ↑ Ogunnaike, James (17 September 2024). ""Lisabi", A film by ace artiste, Adedimeji sets for premiere Sunday". Archived from the original on 1 October 2024. Retrieved 28 September 2024.