Ma'aikatar Aikin Gona ta Tarayyar Najeriya
Ma'aikatar Aikin Gona ta Tarayyar Najeriya | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ministry of agriculture (en) , government agency (en) da corporate body (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Aiki | |
Kayayyaki | |
Subdivisions | |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1967 |
fmard.gov.ng |
Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya Ma’aikatar Gwamnatin Tarayyar Najeriya ce da ke da hurumin tabbatar da wadatar abinci a fannin amfanin gona da kiwo da kamun kifi, da karfafa ayyukan noma da ayyukan yi, da inganta noma da samar da ɗanyen mai ga ‘yan kasuwa da masana'antu da samar da kasuwannin kayayyakin masana'antu da samar da musanya ta kasashen ketare da kuma taimakon raya tattalin arzikin karkara a dukkan fadin tarayyar Najeriya.
Dr. Mohammad Mahmood Abubakar shi ne ministan noma da raya karkara na yanzu[1] Dr. Abubakar ya maye gurbin Sabo Nanono kuma ya karbi ragamar kula da harkokin ma'aikatar noma da raya karkara a watan Satumban 2021], bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tura shi aiki daga ma'aikatar muhalli ta tarayya.
Kafin mayar da shi aiki daga ma'aikatar muhalli da raya karkara, Dr. Abubakar ya samu manya-manyan nasarori ta fuskacin tsaftace yankin Ogoni da yaki da sauyin yanayin da kiyaye namun daji da gyaran yankunan da ya shafa da dai sauransu. Ya kuma kasance shugaban hukumar kula da ilimin bai daya. Gogaggen ɗan siyasa ne kuma ƙwararren masanin ilmin fasaha.[2]
Tarihin Ma'aikatar Gona ta Tarayya.
[gyara sashe | gyara masomin]An samar da Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya ne a shekarar 1967, lokacin da aka samar da Jihohi 12, daga Jihohi 4 na Nijeriya bayan samun ‘yancin kai.[3] Kowace Jiha tana da ma'aikatar noma da albarkatun kasa. Misali jihar Ebonyi tana da nata haka ma sauran Jihohi .[4] A cikin Afrilun shekarar 2010, lokacin da Goodluck Jonathan ya naɗa Sheikh Ahmed Abdullah Ma'aikatar Albarkatun Ruwa ta bambanta da ma'aikatar Noma da Karkara.[5] A baya dai ma'aikatar ta kasance karkashin jagorancin Adamu Bello, Abba Sayyadi Ruma[6] da Sheikh Ahmed Abdullah.
Shugaba Goodluck Jonathan ya naɗa Akinwumi Adesina Ministan Noma da Raya Karkara na Tarayya a watan Yunin 2011. Audu Innocent Ogbeh ne ya gaje shi wanda shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa a shekarar 2015.[7] Shugaba Buhari bai rike Audu a wa’adi na biyu ba sai Sabo Nanono ya maye gurbinsa a 2019.[8] Mustapha Baba Shehuri shi ne karamin minista a yanzu yayinda Dr. Ernest Afolabi Umakhihe ya kasance sakataren dindindin na ma'aikatar noma da raya karkara ta tarayya.[9]
Hakki.
[gyara sashe | gyara masomin]Ma'aikatar tana da alhakin ayyuka daban-daban da suka shafi manufofin kasa na cigaban karkara da samar da abinci da karuwar kudaden shiga na karkara da samar da ayyukan yi.[10] Ma'aikatar tana cika nauyin da ke kanta ta hanyar sassanta da ma'aikatunta. Haka kuma, tana kulawa da bayar da kudade ga cibiyoyin bincike kamar Cibiyar Binciken Tushen amfanin gona ta ƙasa da Cibiyar Binciken Samar da Dabbobi ta ƙasa (NAPRI), da Cibiyar Binciken Dabbobi ta Ƙasa (NVRI), da Cibiyar Binciken Roba ta Najeriya (RRIN) da Kwalejojin Noma da Gandun daji tsakanin wasu. Cibiyar Binciken Roba ta Najeriya (RRIN) tana cikin ƙauyen IYANOMO, kusa da babbar hanyar Benin/Sapele, cikin birnin Benin, Jihar Edo.
Duba kuma.
[gyara sashe | gyara masomin]- Ci gaban karkara a Najeriya.
- Noma a Najeriya.
Manazarta.
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ (https://fmard.gov.ng/2022). [https://www.premiumtimesng.com/news/484290-livestock-transformation-plan-priority-new-agric-minister-says.html
- ↑ "Buhari Sacks Ministers Of Agriculture And Power | Channels Television". www.channelstv.com. Retrieved 2021-09-23..
- ↑ Blueprint (2021-09-15). "On the appointment of agric minister". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2022-06-01.
- ↑ "Ministry of Agriculture And Natural Resources, Ebonyi State Government". www.ebonyistate.gov.ng. Archived from the original on 2022-10-31. Retrieved 2022-06-01. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ George Oji (7 April 2010). "Jonathan Takes Over Ministry of Power". ThisDay. Retrieved 2011-02-27.
- ↑ "Welcome". Abba Sayyadi Ruma. Archived from the original on 2010-03-26. Retrieved 2009-12-15. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "Buhari finally names a new Nigerian government cabinet—but it's not that new". QuartzAfrica. Retrieved 2019-08-26.
- ↑ "Ex-Ministers Dropped By Buhari". Sahara Reporters. Retrieved 2019-08-26.
- ↑ Ibukun Odusote Archived 2 ga Faburairu, 2016 at the Wayback Machine, Federal Ministry of Agriculture and Rural Development, Retrieved 23 January 2016
- ↑ "Welcome". Federal Ministry of Agriculture and Rural Development. Retrieved 2019-08-26.