Jump to content

MaameYaa Boafo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
MaameYaa Boafo
Rayuwa
Haihuwa Pakistan, 20 century
Karatu
Makaranta Rutgers University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a jarumi
IMDb nm5545649

MaameYaa Boafo Abiah (an haife ta a shekarar 1980). Ƴar wasan Pakistan da Ghana ce kuma yar wasan ban dariya, barkwanci.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Boafo haifaffiyar Pakistan ce. Mahaifinta ya yi aiki da Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.[1] Tana daga cikin yan ƙabilar Ashanti (Ghanian).[2] Ta girma a Sudan, Habasha, Geneva da kuma Kenya, amma 'yar asalin Ghana ce..[3] A shekara ta 2001, bayan kammala karatun sakandare, Boafo ta tafi Amurka don koyon Faransanci da sadarwa. Bayan ta kammala karatu a kwalejin Hood a 2005, ta samu gurbin karatu a jami’ar Rutgers kuma ta samu digiri na biyu a shekarar 2019.[4] Boafo tayi karatun sa a kasashen waje a Jami'ar Marc Bloch da ke Strasbourg, Faransa.

Boafo ta fara wasan kwaikwayo ne a matsayin Asa a cikin gajeren fim ɗin shekarar 2012 mai suna Asa, A Beautiful Girl.[5] A cikin 2014, Boafo ta fara fitowa a matsayin Nana Yaa a cikin jerin shirye-shiryen gidan talabijin na Nicole Amarteifio An African City. Halinta a cikin shirin a matsayin ɗan jarida ce wadda ke ƙoƙarin samun kuɗin haya a Accra, shirin da yayi kama da na Carrie Bradshaw a Sex and the City. Boafo ta ɗauki wasan kwaikwayon ya fi siyasa fiye da sex and the CityJima'i . Har ila yau, a cikin 2014, Boafo ta yi rawar gani a cikin shirin Bus Nut, wani gajeren fim na gwaji wanda a ciki ta karanta kalmomin daga gwajin Rosa Parks. Ya fara ne a San Francisco Film Festival.

A cikin 2015, Boafo tana da ƙaramin matsayi a The Family Fang. Ta fito a cikin gajerun fina-finan New York, I love You da Olive a shekara ta 2016.[6] Daga 2017 zuwa 2018, ta zama kamar Paulina a cikin wasan kwaikwayon School Girls, wanda Mean Girls suka samar.[7]

Lambar yabo

[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓi Boafo domin bata lambar yabo ta (Lucille Lortell) da kuma (Los Angeles Drama Circle Award) a matsayin Gwarzuwar jaruma, kuma ta karɓi lambar yabo ta (Drama Desk) saboda rawar da ta taka. Ta taka rawar (Abena Kwemo) mai cutar kanjamau a cikin shirin 2018 na Chicago Med.[8] A cikin 2019, ta yi wasa mai binciken sirri Briana Logan a cikin jerin shirye-shiryen Telebijin na Bluff City Law.[9] Boafo ta fito a matsayin (Zainab) a cikin jerin shirye shiryen telebijin din Ramy a shekarar 2020.[10]

Rayuwar Iyali

[gyara sashe | gyara masomin]

Boafo ta auri Irmiya Abiah kuma tana zaune a birnin New York City.[11] Ta kasance mai son ƙwallon ƙafa. Boafo ta yi bidiyo don nuna alhinin mutuwar Freddie Gray a Baltimore mai taken "As Nina", tunda tana kama da Nina Simone. Baya ga Ingilishi, tana magana da Twi.

Haɗin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. Meyerfeld, Bruno (15 May 2015). "MaameYaa Boafo, la diva de la websérie " An African City "". Le Monde (in Faransanci). Archived from the original on 21 September 2018. Retrieved 2 November 2020.
  2. Kodjo, Cyprien (13 October 2014). "An African "Sex and the City"". New York Amsterdam News. Retrieved 2 November 2020.
  3. "MaameYaa Boafo Bio". Broadway World. Retrieved 2 November 2020.
  4. "Briana Johnson". NBC. Retrieved 2 November 2020.
  5. Forson, Viviane (7 March 2016). "Diaspora - Télévision - MaameYaa Boafo : il faut s'affirmer tel que l'on est". Le Point (in French). Retrieved 2 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  6. Green, Jesse (16 November 2017). "Review: 'School Girls' Is a Gleeful African Makeover of an American Genre". The New York Times. Retrieved 2 November 2020.
  7. Coulston, John Connor (3 January 2018). "'Chicago Med' Takes on HIV in Latest Episode". Popculture.com. Retrieved 2 November 2020.
  8. Isama, Antoinette (19 May 2019). "'An African City' and 'School Girls' Star MaameYaa Boafo Lands Role in New NBC Legal Drama". OkayAfrica. Retrieved 2 November 2020.
  9. Ali, Lorraine (17 June 2020). "Struggling Ramy character makes for smart humor amid questions of faith, commitment". Los Angeles Times. Retrieved 2 November 2020.
  10. "2005: Summer Update 2014". Hood College. Retrieved 2 November 2020.[permanent dead link]