Jump to content

Maganar hannu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maganar hannu
sign language (en) Fassara da modern language (en) Fassara
Bayanai
Suna a harshen gida Maganar hannu
Gajeren suna HSL
Ƙasa Najeriya
Indigenous to (en) Fassara Babban Birnin Tarayya, Najeriya, Jihar Neja da Hausawa
Ethnologue language status (en) Fassara 6a Vigorous (en) Fassara
Shafin yanar gizo hausa-sign-language.com

Maganar hannu ko harshen bebaye na ƙasar Hausa (ko Hausa Sign Language a Turance) yare ne na bebayen ƙasar Hausa.

Maganar hannu ta Hausawa

Gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ba a san yawan bebayen da suke arewacin Nijeriya ko yawan mutanen da suke amfani da harshen bebaye na ƙasar Hausa ba. Kiyasi ya bambanta sosai dangane da yawan masu amfani da wannan harshen, tsakanin mutane dubu 70 da miliyan 5.[1]

Ba a san asalin harshen bebaye na ƙasar Hausa ba, amma ana kyautata zaton cewa tun lokacin da bebaye suka fara hulɗa da juna suke amfani da harshensu na bebaye. Ba a koyar da harshen bebaye na ƙasar Hausa a makarantu, amma bebaye tsoffi sukan koya wa yara, su kuma sai su koya wa nasu yaran. Yara sukan koyi wannan yare a wurin iyayensu, ko abokansu, ko ’yan ƙungiyar bebaye. Harshen bebaye na ƙasar Hausa yana daɗa bunƙasa duk lokacin da bebaye sukan haɗu, ko a waje, ko a makaranta, ko ma a ƙungiyance.

Tsarin harshe[gyara sashe | gyara masomin]

Harshen bebaye na ƙasar Hausa yare ne cikakke mai zaman kansa. Harshen bebaye ya bambanta da na Hausar baka ta yadda ake ƙirar kalma da kuma ta yadda ake ginin jimla, ma’ana tsarin sauti da nahawun harshen bebaye na ƙasar Hausa sun bambanta da na Hausar baka. Amma harshen Hausar baka yana da tasiri kan harshen bebaye.

Ana amfani da hannaye domin nuna alamomin (wato kalmomin) harshen bebaye. Cikin harshen bebaye ana harhaɗa siffofin hannu, da wurin da aka sa hannu, da motsin da hannu ke yi, ya samar da ma’ana. Yana kuma da muhimmanci inda tafin hannu ke kallo. Wato in an harhaɗa waɗannan ma’aunai akan ƙera wata alama, wato wata kalmar harshen bebaye. Ana iya yin alama da hannu ɗaya ko biyu.

Sigar jiki, da motsin jiki, da kuma alamun fuska, da sauran sigogi su ma suna yin tasiri. Suna iya zama wani ma’auni na alamomi, amma kuma za su ma iya ɗaukar wata ishara ta nahawu, kamar tambaya ko jaddada magana.

Littattafai kan harshen bebaye na ƙasar Hausa[gyara sashe | gyara masomin]

 • Schmaling, Halima C. 2020. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na farko: Iyali. Hamburg: Buske. [Hausa Sign Language, Book 1: Family.] (2nd rev. and ext. ed.)
 • Schmaling, Halima C. 2019. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na takwas: Kayan gida. Hamburg: Buske. [Hausa Sign Language. Book 8: Things in the house.]
 • Schmaling, Halima C. 2018. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na bakwai: Ilmi. Hamburg: Buske. [Hausa Sign Language. Book 7: Education.]
 • Schmaling, Halima C. 2018. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na shida: Lokaci da yanayi. Hamburg: Buske. [Hausa Sign Language. Book 6: Time and weather.]
 • Schmaling, Halima C. 2017. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na biyar: Ayyukan yau da kullum. Hamburg: Buske. [Hausa Sign Language. Book 5: Everyday activities.]
 • Schmaling, Halima C. 2016. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na hudu: Kasuwanci da kidaya. Hamburg: Buske.[Hausa Sign Language. Book 4: Commerce and counting.]
 • Schmaling, Halima C. 2016. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na uku: Kwatancin mutane da abubuwa. Hamburg: Buske. [Hausa SignLanguage, Book 3: Describing people and things.]
 • Schmaling, Halima C. 2014. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na biyu: Haduwa da sadarwa. Hamburg: Buske. [Hausa Sign Language, Book 2: Meeting and communicating.]
 • Schmaling, Halima C. and Bala Hausawa, Lawan. 2011. Maganar hannu: Harshen bebaye na kasar Hausa. Littafi na farko: Iyali. Kano: Government Printers. [Hausa Sign Language, Book 1: Family.]
 • Kamei, Nobutaka (2004). "The Sign Languages of Africa". Journal of African Studies. 2004 (64): 43–64. doi:10.11619/africa1964.2004.43.
 • Schmaling, Constanze. 2003. A for Apple: The impact of Western education and ASL on the deaf community in Kano State, northern Nigeria. In Many ways to be deaf: nternational variation in Deaf communities, ed. L. Monaghan, C. Schmaling, K. Nakamura, G. Turner. Washington, DC: Gallaudet University Press, 302-310.
 • Schmaling, Constanze. 2001. ASL in Northern Nigeria: Will Hausa sign language survive. Signed languages: Discoveries from international research, ed. by Valerie Dively, 2001, 180–93. Gallaudet University Press.
 • Schmaling, Constanze. 2000. Maganar Hannu: Language of the hands. A descriptive analysis of Hausa Sign Language. Hamburg: Signum.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. Schmaling, Constanze. 2015. Sign Languages of the World: A Comparative Handbook, Julie Bakken Jepsen, Goedele De Clerck, Sam Lutalo-Kiingi, William B. McGregor, (eds.), 362-390. Berlin: Walter de Gruyter. DOI: https://doi.org/10.1515/9781614518174