Jump to content

Makaman nukiliya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Makaman nukiliya
explosive device (en) Fassara, nuclear technology (en) Fassara da weapon functional class (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na weapon of mass destruction (en) Fassara da nuclear explosive (en) Fassara
Yana haddasa nuclear explosion (en) Fassara
Tarihin maudu'i history of nuclear weapons (en) Fassara
Uses (en) Fassara nuclear reaction (en) Fassara

Yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya, Yarjejeniya ce, da aka ƙirƙirota domin iyakance yaɗuwar makaman nukiliya a duniya. kuma ta samo asali ne shekara guda bayan da Amirka ta ƙaddamar da harin makaman nukiliya a Hiroshima da Nagasaki a shekarar 1945. Tun daga wannan lokaci ne Amirkan ta ƙuduri aniyar hana sayarwa ko kuma bayar da makaman nukiliya ga wata ƙasa.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Tashar nukiliya ta ƙasar Faransa Shekaru 23 da yin haka sai ƙasashen duniya suka shiga yin yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa akan hana cinikin makaman nukiliya tsakanin ƙasashen duniya. Wannan ne ya sa a ranar 1 ga wata Yulin shekara ta 1968, aka kuma ƙaddamar da yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya, domin ƙasashen duniya su ci gaba da rattaba hannu a kowanne lokaci. Kuma yanzu haka akwai kasashe 189 da tuni suka rattaba hannun akan amincewa da wannan yarjejeniya. Kodadai biyar daga cikin su sun mallaki makaman nukiliya ɗin.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Tashar nukiliya ta ƙasar Birtaniya Ƙasashen da suka rigaya suka ratabba hannun amincewa da wannan yar jejeniya amma kuma sun mallaki makaman nikiliya sun haɗa da ƙasar Amirka da Birtaniya da Faransa da Rasha da kuma Chana, wanda kuma sune ƙasashen da ke da wakilcin dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Tukwanen sanyaya nukiliya na ruwa a ƙasar Amirka Daga cikin ƙasashe masu cikakken 'yanci a duniya, ƙasashe huɗu ne kaɗai ba su sanya hannu akan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliyar ba, kuma sun haɗa da ƙasar Indiya da Isra'ila da Pakistan da kuma Koriya ta Arewa. Inda ƙasar Indiya da Pakistan da Koriya ta Arewa duk sun fito fili sun yi gwajin makaman nukiliyar na su a sarari. Kuma sun bayyana ƙarara cewa, sun mallaki makaman nukiliya. Ita kuwa Isra'ila wani salo ta ɗauka na jirwaye da kamar wanka, ba ta dai fito ƙarara ta nuna nufinta a game da shirinta na makaman nukiliya ba.

Ƙasashen Ireland da Finland dai, su ne suka baiwa duniya shawarar kafa wannan yarjejeniya, su ne kuma ƙasashe na farko da suka fara rattaba hannun amincewa da ita. Yarjejeniyar dai ta ƙunshi gabatarwa da kuma sassa guda tara.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Ofishin harkokin nukiliya na ƙasar Chaina Ana dai sabunta yarjejeniyar duk bayan shekaru biyar. Kuma duk da cewa, da farko an tsara yarjejeniyar za ta kasance ne tsawon shekaru 25, to amma ƙasashen da suka sanya hannun gabakiɗayansu sun amince da a bar ƙofa buɗe ba tare da iyakancewa ba, ga duk ƙasar da take buƙatar sanya hannu a yarjejeniyar nan gaba.