Makarantar kwalejin Ilimi ta Tarayya Kontagora

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Makarantar kwalejin Ilimi ta Tarayya Kontagora
Bayanai
Iri jami'a
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 1978
fcekg.edu.ng

Makarantar Kwalejin Ilimi ta Tarayya Kontagora (FCE Kontagora) tana a jihar Neja , jahar dake arewa ta tsakiya Najeriya. An ƙirƙira/kafa makarantar a watan Satumba shekara ta 1978 a matsayin kwalejin malamai (Federal Advanced Teachers College, FATC) a lokacin Mulkin Olusegun Obasanjo (GCFR) mulkin soja kenan. Wannan ya faru ne bayan da Sir. Eric Ashby ya bada umurnin a ƙarƙashin dokar Najeriya mai no. 4 na shekara ta 1986, sai kuma aka dawo aka gyara shi a lamba no. 6 a shekarar 1993 An ɗaukaka matsayin kwalejin a ƙarƙashin Jami'ar Ilorin da kuma Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.[1][2]

Tarihin shugabancin kwalejin[gyara sashe | gyara masomin]

Mr. O. O. Ogun shine shugaban makarantar na farko a wani wajen da aka kafa makarantar a matsayin wucin gadi bana din-din-din ba a shekara ta 1978 a wannan lokacin duk wasu aikace-aikacen da koyarwa anayinsu ne a wajajen da hukumar makarantar ta kama haya ko kuma tayi aro a cikin garin Kontagora har yau-wajiya Malamai da Ɗaliban makarantar suna zama ne kodai haya ko kuma wani gurin da ba cikin makarantar ba a cikin gari. A shekara ta 1981 Dr. S K Afolabi an naɗa shi a matsayin muƙaddashin shugaban makarantar ya zauna a wannan matsayin har watan Disamba shekara ta 1982. Sai kuma a watan Janairu shekara ta 1983. Dr. M A Uppal an tsammani ya zama shugaban makarantar bayan ya ɗau lokaci yana shugabantar makarantar na wuccin gadi, daga baya kuma sai aka maye gurbin shi da Dr. S A Abdurrahman a shekarar 1985 zuwa shekarar 1987. Bayan nan Alhaji Shehu Ɗalhatu ya zamo shugaban makarantar wanda yake da cikakken iko na shugabancin kwaleji har tsawon shekaru 6, wato tunda ya fara a shekarar 1987-1993 ya sauka. A ranar 8 ga watan Maris shekarar 1993 Dr. Elisha G Kutara ya maye gurbin Alhaji Shehu Ɗalhatu a matsayin shugaban kwalejin, wanda ya rasa aikin shi daga Kwalejin Ilimi ta Zariya. Bayan nan an naɗa Dr. A. M Tura a matsayin shugaban kwalejin a shekarar 1996 a dalilin wani rikicin da ya dabaibaye makarantar wanda yayi dalilin har sai shugabannin Ilimi na ƙasa suka baki a rikicin kuma suka sake daidaita tsarin shugabancin kwalejin. A ranar 1 ga watan Disamba 1998 Dr. Emmanuel I. Makoju ya karɓe shugabancin kwalejin wanda ya shugabanci kwalejin har sau biyu shekara 8 kenan bayan saukar shi a (2006). A watan Oktoba shekarar 2006 an naɗa Alhaji Shehi T Sidi a matsayin shugaban kwalejin na wucin gadi har tsawon shekaru 3. Shugaban ƙasa Dr. An sake Dr. Nathaniel O. Odediran a matsayin shugaban kwalejin bayan ya gama zagaye na farko na shugabantar kwalejin, shugaban ƙasa Dr Goodluck Ebele Jonathan ya sake naɗa shi a matsayin shugaban kwalejin har shekara ta 2018. An naɗa Alhaji Jibril Garba a matsayin shugaban kwalejin na riƙon ƙwarya tsawon watanni 3. Ranar 10 ga watan Afrilu shekara ta ta 2018 Gwamnatin tarayya ta naɗa Farfesa Faruk Rasheed Haruna a matsayin shugaban kwalejin, wanda har zuwa yanzu magana da ake shine shugaban makarantar.

Kwasa-kwasai da ake koyarwa a kwalejin[gyara sashe | gyara masomin]

Waɗannan sune jerin darussan da ake koyarwa a kwalejin Kontagora

  • Adult and Non-Formal Education

Agricultural Science

  • Agricultural Science and Education
  • Arabic / Christian Religious Studies
  • Arabic / English
  • Arabic / French
  • Arabic / Hausa
  • Arabic / Igbo
  • Arabic / Islamic Studies
  • Arabic / Social Studies
  • Arabic / Yoruba
  • Biology / Chemistry
  • Biology / Integrated Science
  • Biology / Mathematics
  • Biology / Physics
  • Business Education
  • Christian Religious Studies / Economics
  • Christian Religious Studies / English
  • Christian Religious Studies / French
  • Christian Religious Studies / Geography
  • Christian Religious Studies / History
  • Christian Religious Studies / Hausa
  • Christians Religion Studies / Social Studies
  • Christians Religion Studies / Yoruba
  • Computer Science Education / Mathematics
  • Early Childhood Care Education
  • Economics / English
  • Economics / Mathematics
  • Economics / Social Studies
  • Education and Arabic
  • Education and Biology
  • Education and Christian Religious Studies
  • Education and English Language
  • Education and Hausa
  • Education and Integrated Science
  • Education and Islamic Studies
  • Education and Mathematics
  • Education and Physics
  • Education and Social Studies
  • English / French
  • English / Hausa
  • English / History
  • English / Igbo
  • English / Integrated Science
  • English / Islamic Studies
  • English / Political Science
  • French / Social Studies
  • French / Hausa
  • French / History
  • French / Igbo
  • French / Yoruba
  • Geography / Mathematics
  • Geography / Social Studies
  • Hausa / Igbo
  • Hausa / Islamic Studies
  • Hausa / Political Science
  • History / Islamic Studies
  • Igbo / Social Studies
  • Igbo / Yoruba
  • Integrated Science / Mathematics Education
  • Integrated Science / Yoruba
  • Islamic Studies / Economics
  • Islamic Studies / Geography
  • Islamic Studies / Social Studies
  • Islamic Studies / Yoruba
  • Mathematics / Physics
  • Mathematics / Social Studies
  • Physical and Health Education
  • Political Science / Social Studies
  • Primary Education Studies
  • Social Studies / Yoruba
  • Teacher Education Science
  • Physical And Health Education (Double Major)
  • Computer Science / Biology
  • Computer Science / Chemistry
  • Computer Science / Physics
  • Fine And Applied Arts (Double Major)
  • Special Education (Double Major)
  • Social Studies (Double Major)
  • Primary Education ( Double Major)
  • Home Economics (Double Major)

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Plans underway to upgrade FCE Kontagora to University of Education — Provost". Daily Nigerian (in Turanci). 4 October 2020. Archived from the original on 6 January 2022. Retrieved 6 January 2022.
  2. Dickson (29 October 2020). "Need For More TETfund Interventions At FCE, Kontagora". Leadership News - Nigeria News, Breaking News, Politics and more (in Turanci). Archived from the original on 6 January 2022. Retrieved 6 January 2022.