Jump to content

Malik Asselah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Malik Asselah
Rayuwa
Haihuwa Aljir, 8 ga Yuli, 1986 (38 shekaru)
ƙasa Aljeriya
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  NA Hussein Dey (en) Fassara-
  NA Hussein Dey (en) Fassara2006-2010
  Algeria national under-23 football team (en) Fassara2007-200710
  Kungiyar Kwallon Kafa ta Aljeriya2008-
  JS Kabylie (en) Fassara2010-2014660
CR Belouizdad (en) Fassara2014-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai tsaran raga
Lamban wasa 30
Tsayi 190 cm

Malik Asselah (an haife shi a ranar 8 ga watan Yulin shekarar 1986) dan kwallon Algeria ne wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron raga na ƙungiyar Al-Hazem da Ƙungiyar kwallon kafa ta Algeria .

An haife shi a Algiers, Asselah asalin ta ƙauyen Ighil Imoula ne na Lardin Tizi Ouzou .

Samfurin NA Hussein Dey ƙarami ne, Asselah ya fara zama ɗan wasa na farko a ƙungiyar a shekarar 2006.

A ƙarshen kakar shekarar2009-2010, ya bar NA Hussein Dey bayan da suka sauka. Daga baya kuma ya sanya hannu kan kwantiragin shekara ɗaya tare da JS Kabylie .

Ayyukan duniya

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 31 ga Disamban shekarar, 2007, Asselah ya fara buga wa ƙungiyar kwallon kafa ta ' yan ƙasa da shekaru 23 ta Algeria wasa a wasan sada zumunci da suka doke Saudi Arabia a Riyadh .

A ranar 17 ga Afrilun shekarar, 2008, an gayyace shi zuwa kungiyar A 'National Algerian don wasan neman cancantar buga gasar cin kofin Afirka da Morocco amma ya fice daga kungiyar da rauni.

An gayyaci Asselah cikin manyan ‘yan wasan Algeria don wasan neman tikitin shiga gasar cin Kofin Afirka na 2017 da Seychelles a ranar 2 ga Yulin shekarar 2016.

  • Sunyi Kofin Algeriya sau ɗaya tare da JS Kabylie a 2010–11