Mallam Dendo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mallam Dendo
Rayuwa
Haihuwa Kebbi, 1760
Ƙabila Mutanen Fulani
Mutuwa 1833
Sana'a
Sana'a warlord (en) Fassara da Malami

Mallam Muhammadu Bangana wanda aka fi sani da Mallam Dendo ko Manko, ya kasance fitaccen mutumen tarihi a karni na 19 a kasar Najeriya a yau. Ya fito ne daga al’ummar Fulani mazauna Kebbi, dake Arewacin Najeriya.[1]

A cikin ƙarni na 19, lokacin da yankin Sudan ta tsakiya ke samun gagarumin sauyi sakamakon mamayar da Uthman dan Fodio ya jagoranta, Mallam Dendo ya yi hijira zuwa kasar Nupe. Wannan lokaci ne Sarkin Gwandu ya yi wa mutanen Nupe sarauta .

Mallam Dendo ya kware a siyasa da tsare-tsare. Yunkurinsa na wayo ya taimaka sosai wajen canza al'ummar Nupe sosai. An san shi da yin sabuwar hanyar yin abubuwa a Nupe da aka yi kusan shekaru 200, wanda kuma ya mayar da Nupe na zamani.

Ana kuma tunawa da Mallam Dendo da son karatun addinin musulunci da kuma kasancewarsa babban shugaba. Labarin rayuwarsa, tun daga koyon addinin Musulunci har ya zama babban malami kuma jagora na Musulunci, ya nuna irin tasirin da ya yi a tarihin Nupe.

Har yau, mutane suna tunanin abin da Mallam Dendo ya yi. Yana da muhimmin ɓangare na tarihin Nupe kuma yana ƙarfafa wasu suyi tunani da koyo.[2][3][4][5][6][7]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. salau, mohammed bashir salaumohammed bashir (2011-01-01), "Mallam Dendo", Dictionary of African Biography (in Turanci), Oxford University Press, doi:10.1093/acref/9780195382075.001.0001/acref-9780195382075-e-1248, ISBN 978-0-19-538207-5, retrieved 2023-10-04
  2. Olubiyo, Kolade (2003-01-01). "The Nupe People of Nigeria". Cite journal requires |journal= (help)
  3. Editor (2022-03-30). "Al'ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nufe a Nijeriya (II)". Manhaja - Blueprint Hausa version. Retrieved 2023-10-04.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  4. "Dangantakar Harshen Hausa Da Nufanci: Nazarin Tasirin Hausa A Kan Harshen Nufanci (4)". Retrieved 2023-10-04.
  5. Reporter, Our (2021-11-10). "Cultural heritage: What you need to know about the Etsu Nupe's palace". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-10-04.
  6. "AFRICA | 101 Last Tribes - Nupe people". www.101lasttribes.com. Retrieved 2023-10-04.
  7. "NYSC Bida>>History of Nupe tribe". web.archive.org. 2011-02-11. Archived from the original on 2011-02-11. Retrieved 2023-10-04.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)