Mao, Chadi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mao, Chadi

Wuri
Map
 14°07′10″N 15°18′48″E / 14.1194°N 15.3133°E / 14.1194; 15.3133
Ƴantacciyar ƙasaCadi
Region of Chad (en) FassaraKanem
Department of Chad (en) FassaraKanem Department (en) Fassara
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 19,004 (2008)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 339 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Mao ( Larabci: مؤ‎ ) Birni ne da ke ƙasar Chadi, babban birnin yankin Kanem kuma na sashen da ake kira Kanem. Shi ne birni na 16 mafi yawan jama'a a Chadi, kuma yana da nisan kilomita 226 (mil 140) a arewa maso gabas da N'Djamena.

A kan iyakar Sahara, yanayin Mao akwai alamar yashi da ciyayi marasa kyau. Yawancin mazauna Mao Musulmai ne. Akwai majami'u na Kirista guda biyu ( Katolika ɗaya da Furotesta ɗaya) a birnin na Mao.

Kamar yadda yake a sauran yankunan Chadi, Sarkin Mao na gargajiya ne[1] da kuma jami'an gwamnati. Sarkin Kanem, wanda ke zaune a Mao, shi ne sarkin gargajiya na Kanembou.[1] Yunƙurin da ake na samun riƙon sakainar kashi ya samu cikas sakamakon sarkakiyar alakar da ke tsakanin sarakunan gargajiya a Chadi da hukumomin ƙasa.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An ƙirƙiro Mao a cikin shekara ta 1898, wanda ya ƙirƙiro shi ne, Sultan Ali, ɗan'uwan Sultan Djourab wanda Fezzans da sauran abokansa suka kashe shi. Tun daga 1900, Mao ta kasance cibiyar gudanarwa mai inganci a arewa.

A ranar 18 ga watan Yuli, 2010, Sultan na Kanem, Alifa Ali Zezerti, ya mutu a asibiti a N'Djamena yana da shekaru 83, sakamakon kamuwa da ciwon zuciya. Shi ne mai mulki na 39 a daular Kanem,[2] kuma ya yi sarauta tun 1947.[3] An binne shi a Mao. Magabacinsa, Sultan Zezerti, ya rasu a ranar 26 ga Satumban 1947,[4] ya fara mulki tun 1925.[5] An zaɓi ɗansa a matsayin Sultan a zaben fidda gwani ba tare da gasa ba.

A watan Oktoban 2013, tarzoma ta ɓarke a babbar kasuwar Mao da aka yi ta nuna adawa da gwamnatin Idriss Deby bayan harbin wani farar hula da wani jami'in na kusa da Deby ya yi.[6][7]

A ranar 30 ga watan Satumba, 2015, da misalin karfe 8 na dare, wata babbar gobara ta ƙone babbar kasuwar Mao.[8] Ba'a iya tantance asalin nisan abin tashin wutar ba. Ba a bayar da rahoton mutuwar mutane ba.

A ranar 12 ga watan Mayu, 2016, da ƙarfe 5 na safe, wata babbar gobara ta bazu ko'ina da ina a babbar kasuwar Mao, gobarar a karo na biyu cikin ƙasa da shekaru biyu.[9] Gobarar ta tashi ne a wani ma'ajiyar man da ke kusa. Ba a samu asarar rai ba.

Sufuri[gyara sashe | gyara masomin]

Yankin ya keɓe sosai kuma tafiye-tafiyen ƙasa yana da wahala.[1] Garin yana da ƙaramin filin jirgin sama, Mao Airport.

Tattalin Arziki[gyara sashe | gyara masomin]

A ranakun Laraba, wato “Ranar Kasuwa”, ana sayar da sabbin kayan amfanin gona irin su albasa, tafarnuwa, dabino, karas, tumatur, cucumbers da wani lokacin aubergines, wadanda Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar a shekarar 2009. Ana kuma sayar da 'ya'yan itace, musamman ayaba da mangwaro, gwanda da gwaba. Gero kuma yana samuwa a launin Fari da Ja.[10]

Alkaluma[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara Yawan jama'a
1993 13,277
2009 35,468
2019 50,000

Adadin yawan jama'a na Shekara ta 1993 da 2009 ya yi daidai da ƙidayar jama'a a hukumance, na shekarar 2019 an ƙiyasta ta bisa karuwar yawan jama'a a yankin Kanem.[11]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

Bayanan kula[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 "République du Tchad - Projet de développement agricole des ouadis du Kanem - (PDAOK) - Rapport d'évaluation intermédiaire". April 2003. pp. A. Area and Context of the Intervention, Target Group. Retrieved 12 March 2017.
  2. "Tchad : Le Sultan du Kanem s'en est allé". www.africa-info.org (in Faransanci). Retrieved 2017-03-12.
  3. Waldar. "NECROLOGIE :Le sultan du Kanem ALIFA MAO S'EST ETEINT - WALDARI WA AKHBAARA". WALDARI WA AKHBAARA (in Faransanci). Retrieved 2017-03-12.
  4. Lanne, Bernard (1998-01-01). Histoire politique du Tchad de 1945 à 1958: administration, partis, élections (in Faransanci). KARTHALA Editions. p. 119. ISBN 9782865378838.
  5. Lanne, Bernard (1998-01-01). Histoire politique du Tchad de 1945 à 1958: administration, partis, élections (in Faransanci). KARTHALA Editions. p. 103. ISBN 9782865378838.
  6. "JournalDuTchad.com: Mao: des jeunes tchadiens incendient la gendarmerie". Archived from the original on 2017-09-09. Retrieved 2017-03-12.
  7. Administrateur. "Tchad/Émeutes à Mao: les secours accourent vers Mao". letchadien.com (in Faransanci). Archived from the original on 2017-03-13. Retrieved 2017-03-12.
  8. "Tchad : incendie au marché central de Mao". Tchadinfos.com (in Faransanci). 2015-10-01. Retrieved 2017-03-12.
  9. "Un incendie d'origine inconnu ravage le marché de Mao". Tchadinfos.com (in Faransanci). 2016-05-12. Retrieved 2017-03-12.
  10. "Tchad Profond...Mao, la ville sablonneuse". Regard'ailleurs. Retrieved 2017-03-12.
  11. "Tschad: Regionen, Städte & urbane Orte - Einwohnerzahlen, Karten, Grafiken, Wetter und Web-Informationen".

Sources[gyara sashe | gyara masomin]