Jump to content

Maryam Hiyana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maryam Hiyana
Rayuwa
Ƙabila Hausawa
Sana'a
Sana'a jarumi

Maryam Hiyana ta kasance tsohuwar jaruma ce a masana'antar fim ta hausa wato bama Kannywood ,Maryam Hiyana jaruma ce da ta yi tashe a shekarun baya, ta dade tana fim daga baya tai aure. Tayi tashe a lokacin ta, kyakkyawar doguwar mace a zamanin ta tana ɗaya daga cikin kyawawan mata a masana'antar, tayi zamani dasu Fati Muhammad, Kubra Dako, Jamila Nagudu.[1].

Maryam Hiyana ta fito a Fina-finai da dama irin su Hiyana, Tutar So, Na Goma da sauran su.

Takaitaccen Tarihinta

[gyara sashe | gyara masomin]

Maryam usman Hiyana (maryam olomi ko Kuma maryam Hiyana) ta samo sunan Hiyana ne a sanadiyyar fim ɗin da tayi Mai suna Hiyana. shine fim ɗin ta na farko a masana'antar fim ta Hausa wato kannywood. Tayi fim din tare da manyan jarumai irin su Sarki Ali Nuhu da Kuma Adam A Zango, Ahmad S. Nuhu, Jamila Umar Nagudu , Ahmad. Sadiq, Wanda babban Mai bada umarni a masana'antar fitaccen a fannin Ashiru Nagoma ya shirya. Daga wannan fim ɗin ake Kiran ta da Maryam Hiyana.[2].

= Aure da Iyali =

[gyara sashe | gyara masomin]

Maryam Hiyana tayi aure bayan Wani iftila'i ya fada mata a harkan fim inda tai aure Kuma tana zaune lafiya a gidan mijin ta. Ta auri Ado Ahmad dangulla. Shine masoyin daya aure ta bayan wannan iftila'i ya sameta a rayuwar ta. Ya aure ta kuma ya riketa da Amana. A yanzun haka jarumar tana da Yara guda biyar (5) tare da maigidanta Ado Ahmad dangulla cikin inuwar aure.

Fina finan ta

[gyara sashe | gyara masomin]

Bata dade

  • Hiyana
  • Tutar so
  • Babban gari
  • Ahali
  • Da sauran su
  1. https://hausa.legit.ng/1104610-dandalin-kannywood-maryam-hiyana-ta-ba-marada-kunya.html
  2. https://hausatutoblog.blogspot.com/2018/01/kannywood-jaruma-maryam-hiyana-taba.html?m=1