Jump to content

Ali Nuhu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ali Nuhu
Lua error a mw.lua, layi na 656: invalid value (nil) at index 1 in table for 'concat'.
Rayuwa
Cikakken sunaAli Nuhu Mohammed
HaihuwaMaiduguri, 15 ga Maris, 1974 (52 shekaru)
ƙasaNajeriya
MazauniKano
Harshen uwaHausa
Harshen Waja
Ƴan uwa
MahaifiNuhu
Karatu
MakarantaJami'ar, Jos
Matakin karatuDigiri
Bachelor of Arts (mul) Fassara
HarsunaTuranci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'ajarumi, darakta, mai tsara fim da marubin wasannin kwaykwayo
Kyaututtuka
Imani
AddiniMusulunci
IMDbnm2683171
alinuhu.net

Ali Nuhu Mohammed An haifi shi a ranar 15 ga watan Maris na shekarar (1974) a garin Maiduguri dake Jihar Borno a nan Nijeria. Ya girma a jihar Kano, mahaifinsa kuma dan Balanga ne a jihar Gombe dake Arewacin Najeriya.

Ali Nuhu ya fito daga kabilar Tangale Waja, cikakken sunan mahaifinsa shi ne Nuhu Poloma wanda dan asalin jihar Gombe ne.

Ali Nuhu ya girma ne a hannun mahaifiyar sa a jahar Kano, mahaifiyar sa ta rasu a shekarar alif da dari tara da casa'in da tara (1999) miladiyya . Shi kuma mahaifinsa ya rasu a shekara ta dubu biyu da ashirin (2020). Ali Nuhu jarumine a harkar fina-finai, sannan marubucine, mai bada umarni kuma furodusa ne a masana,antar shirya fina-finai ta kannywood da Nollywood. Sannan kuma wasu lokutan ya kan yi rawa a wasu fina-finai.

Ali Nuhu yana fina-finan sa cikin harshen Hausa da turanci, sannan kuma yana cikin manyan jaruman da suka kafa masana'antar shirya finafinai ta kannywood.


Shekarun sa 52 a shekarar 2026, ya kuma karanci geography a jami'ar Jos wato University of Jos a turance.

Mutane suna masa inkiya da "sarki Ali Nuhu" (King of kannywood), wanda aƙalla zuwa yanzu ya fito a fina-finai sama da dari bakwai(500) wanda ya samu lambobin yabo da dama. Ko a shekara ta 2023 sai da ya samu lambar yabo ta "Best actor award in the Nollywood Europe Golden Award (NEGA a shekarar 2023)".

Ali Nuhu ya fara harkar fim tun a shekarar alif da dari tara da casa'in da tara (1999) miladiyya wato shekarar da mahaifiyar sa ta rasu da wani fim mai taken "ABIN SIRRI NE" ya kuma fito a finafinan masana'antar shirya finafinai ta kudanci najeriya NOLLYWOOD irin su Tout too, The Ghost, The Millions and Diamonds in the Sky, da dai sauransu.

A shekarar 2024 shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi a matsayin shugaban masana'antar fina-finai ta Najeriya gaba daya.

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ali Nuhu Muhammad a birnin Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe dake a Arewacin Najeriya da mahaifiyarsa mai suna Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.[1]

Ali Nuhu yana da mata daya da Yara guda biyu, Ahmad Ali nuhu da Fatima Ali nuhu.

Ali ya yi karatu a Jami'ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin na fasaha daga Jami'ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami'ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.[2]

Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a "Sangaya" wanda ya zama ɗayan Fina-finan Hausa da suka fi samun kudi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka haɗa da Azal, Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummuwa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (shekara ta 2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana'antar nishaɗantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).[3]

Shugaban Hukumar Fina-finai ta Najeriya

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2024 shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban hukumar kula da fina-finai ta Najeriya.[4]

inda akayi ittifaki akan yana da mabiya a Twitter sama da mutane dubu dari da arba'in 140,000 da kuma mabiya a Facebook sama da mutane dubu uku 3,000,000 da kuma wasu a shafin Instagram sama da milyan mutane dubu dari 1,000,000.[5][6]

Shekara Suna Matsayi Salo Kamfanin daya shirya
2007 Sitanda Jarumi Wasa
2011 Carbin Kwai Jarumi Wasa
2012 Madubin Dubawa Jarumi Wasa
2012 Last Flight to Abuja Jarumi Wasa Nollywood Film Factory
2013 Blood and Henna Jarumi Wasa Newage Networks
2013 Confusion Na Wa Jarumi Was Cinema KpataKpata
2013 Wani Hanin Jarumi Wasa
2014 Matan Gida Jarumi Wasa
2015 Jinin Jikina Jarumi Wasa
2016 Nasibi Jarumi Wasa
2016 Ojukokoro Jarumi Wasa Singularity Media
2017 Banana Island Ghost Jarumi Wasa Allura cikin ruwa

Shekara ta 2024

Lamban girma

[gyara sashe | gyara masomin]

Ali Nuhu yana daga cikin jaruman fina-finan Hausa wadanda ke gaba-gaba wajen samun gagarumar nasarori a masana'antar ta Kannywood dama ta mutanen kudancin Najeriya wato Nollywood. Anan zamu kawo maku wasu daga cikin kyaututtukan da Ali Nuhu ya samu a harkar sa ta shirya fina-finai.[7][8]

Shekara Kyauta Rukuni Sakamako
2005 Arewa Films Award Best Actor
2007 3rd Africa Movie Academy Awards Best Upcoming Actor award Nasara
2008 The Future Award Best Actor Nasara
2011 Zulu African Film Academy Awards Best Actor (Indigenous)
2012 2012 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
2013 9th Africa Movie Academy Awards Best Supporting Actor Nasara
2013 2013 Nigeria Entertainment Awards Best Actor Nasara
2013 2013 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
2013 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2014 Kannywood Awards Best Actor Nasara
2014 Leadership Awards Best Artiste Nasara
2014 City People Entertainment Awards Best Actor Nasara
2014 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2014 Arewa Music and Movie Awards Pride of Kannywood Nasara
2014 Arewa Music and Movie Awards Best Actor (Popular) Nasara
2015 19th African Film Awards Most Outstanding Actor Nasara
2015 2015 Best of Nollywood Award Best Actor (Hausa) Nasara
2015 2015 Kannywood Awards Best Actor (Popular) Nasara
2015 City People Entertainment Awards Kannywood Personality Nasara
2016 2016 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
2016 Arewa Music and Movie Awards Best Actor Nasara
2016 Kannywood Awards Best Actor Nasara
2016 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2016 Arewa Creative Industry Awards Entertainment Award Nasara
2016 Wazobia FM’s COWA Awards Excellent Entertainer Nasara
2017 Northern Nigeria Peace Awards Best Actor Nasara
2017 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2017 City People Entertainment Awards Best Actor Nasara
2017 2017 Best of Nollywood Awards Special Recognition Award An dakatar

Ali Nuhu

  1. ↑ "Yanzu Jama'a Sun Fara Fahimta Da Rungumar Ayyukanmu-In Ji Jarumi Ali Nuhu". voahausa.com. Voice of America. Retrieved 13 October 2017.
  2. ↑ https://www.voahausa.com/a/a-39-2005-08-06-voa1-91733284/1370189.html
  3. ↑ Lere, Mohammed (15 January 2019). "Ali Nuhu celebrates 20 years in Kannywood". Premium Times. Retrieved 25 November 2019.
  4. ↑ Tinubu appoints Kannywood actor Ali Nuhu MD of Film Corporation
  5. ↑ https://www.premiumtimesng.com/entertainment/kannywood/305949-ali-nuhu-celebrates-20-years-in-kannywood.html
  6. ↑ https://www.legit.ng/1216404-ali-nuhus-biography-family-career.html
  7. ↑ "Sharia Affected Cinema Culture In Northern Nigeria – Nuhu". leadership.ng. Leadership Newspaper. Archived from the original on 13 October 2017. Retrieved 13 October 2017.
  8. ↑ "Ali Nuhu honoured with Doctorate by Cotonou University – Daily Trust". Daily Trust (in Turanci). 2018-10-10. Archived from the original on 2018-10-10. Retrieved 2018-10-11.