Jump to content

Fati Muhammad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fati Muhammad
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 15 ga Yuni, 1982 (42 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo da jarumi

Fati MuhammadTsohuwar shahararriyar jarumar finafinai ce a masana'antar finafinai ta kannywood wacce ke da mazauni a Arewacin Najeriya.

(An haife ta ranar 15 ga watan Yuni, shekara ta 1982)T[1]. [2].

Farkon Rayuwa da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Asalin mahaifan Fati Fulani ne daga jihar Adamawa. An haife ta a ranar 15 ga Yuni, na shekara ta 1982 a unguwar Tukuntawa dake cikin Birnin Kano. Tayi firamare da sakandare a Tukuntawa.

Fati ta fara harkar fim ne tun daga lokacin da ta gabatar da sha'awar ta ta shiga harkar finafinai a lokacin tana da karancin shekaru. Ta fara da nuna ma Tahir Muhammad Fagge wani fitaccen mai shirya finafinai a masana'antar Kannywood sha'awar ta ta shiga harkar finafinai. Shi kuma Tahir ya haɗa ta da Ishaq Sidi Ishaq, shararren mai hada hoto a masana'artan Kannywood. Daga nan ne Ishaq Sidi Ishaq ya fara saka Fati a fim dinsa mai suna "Da Babu", irin rawar da ta taka da kyawu da salon ta sune suka kara fito da ita a fim din inda nan take daga fitar fim din aka san ta. Wannan ya kara jan hankalin sauran producers na masana'antar inda suka yita saka Fati a finafinan su.

Fati ta yi finafinai da dama. Daga cikin su akwai;

  • Sangaya
  • Nagoma
  • Babban Gari
  • Zarge
  • Da babu
  • Marainiya
  • Mujadala
  • Kudiri
  • Tutar So
  • Garwashi
  • Tawakkali
  • Gasa
  • Abadan Da'iman
  • Zo mu Zauna
  • Tangarda
  • Hujja
  • Al'ajabi
  • Halacci
  • Samodara
  • Zumunci
  • Murmushin
  • Alkawari
  • Gimbiya
  • Bakandamiya
  • Taskan Rayuwa dss.

Fati tace a yanzu ta daina fitowa a finafinai amma kuma tana cigaba da shirya finafinai.[3]

Rayuwar Kashin kai

[gyara sashe | gyara masomin]

Fati ta yi aure inda ta auri jarumi a masana'antar Kannywood mai suna Sani Mai Iska. Inda ta bar masana'antar tabi mijin ta suka koma London. Bayan wasu shekaru da aurensu, sai auren ya rabu, daga nan Fati ta dawo gida Najeriya. Bayan dawowar ta nan ma ta tsunduma cikin harkokin fina-finai, saidai bata dade ba ta dakatar bisa ganin wasu sauye sauye da tace ta gani a masana'antar.

Fati ta sake aure kuma inda ta auri Umaru Kanu wani mai shirya finafinai a masana'antar Kannywood kuma yaya ga mawaki Ali Jita. Bayan wani lokaci kuma auren su yazo karshe. Fati bata haihu ba a iya rayuwar ta ta aure.

A shekara ta 2019 anga fati a tarukan siyasa. Kuma Fati ta tabbatar da cewa ta shiga harkokin siyasa.[4].

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-11-23. Retrieved 2021-02-16.
  2. http://hausafilms.tv/actress/fati_muhammad
  3. https://www.blueprint.ng/ive-retired-from-acting-fati-mohammed-2/
  4. https://www.pulse.ng/hausa/fati-muhammed-jaruma-ta-samu-karin-matsayi-a-gidauniyar-atiku-abubakar/nzzt96x[permanent dead link]