Jump to content

Masarautar Gusau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Garin Gusau gari ne da aka kafa shi tun a shekara ta alif Dari takwas da goma shadaya 1811 kimanin shekarar Dari biyu da bakwai (207) da suka gabata bayan tasowar garin daga ‘Yandoto a shekarar alif dari takwas da shida (1806). Garin Gusau yana daya daga cikin manyan garuruwan tsohuwar Jihar Sakkwato kafin daga bisani ya zama babban birnin Jihar Zamfara a shekarar alif dara da cassa,in da shida 1996. Kamar yadda kundin tarihin kasa na alif Dari Tara da ashirin 1920 ya nuna, garin yana kan titin Sakkwato zuwa Zariya ne kimanin kilomita 179, kilomita 210 tsakaninsa da Sakkwato. Daga Gabas garin Gusau ya yi iyaka da Jihar Katsina da ta Kwatarkwashi daga Arewa kuma ya yi iyaka da garin kaura a yayin da ya yi wata iyakar da garin Bunguɗu daga Yamma a bangaren Kudu kuma ya yi iyaka da dansadau da kuma Tsafe.

Wanda ya kafa garin Gusau[gyara sashe | gyara masomin]

Almajirin Shehu Usmanu dan Fodiyo da sheikh abdulsalami ne wato Malam Sambo dan Ashafa Kuma bahaushene ya kafa garin Gusau wanda yake shi da Jama’arsa ba ruwansu da duk harkokin da suka shafi bautar iskokai ko tsafi irin wanda Hausawa ke yi kafin zuwan addinin Musulunci, garin Gusau ba shi da tarihin jahiliya hakan,ne ya sa duk al’adun Gusawa al’adu ne irin na musulunci kuma shigowar wasu mutane wato baki a Gusau bai gurbata kyawawan al’adunsu ba don kuwa mafi yawan bakin da ke tahowa malamai ne na Musulunci da almajirai Hausawa da wasunsu da kan taho garin don tsira da Addininsu da mutuncinsu da kuma dukiyarsu saboda gudun ta addancin Dan fodio dayafara bayan yafara kwadayin samun iko na mulki.A bangaren fada kuma duk umurnin da zai fito daga can zai kasance na dabara da abin da musulunci ya yarda da shi ne na kyawawan dabi’u da al’adu saboda duk kusan sarakunan da aka yi a garin Gusau Hausawane malamai ne na addinin musulunci.

Masarautar Gusau[gyara sashe | gyara masomin]

Masarautar Gusau, kamar yadda tarihi ya nuna ta kafu ne a shekara ta alif dari takwas da shida (1806) a hannun Malam Muhammadu dan Ashafa, a wannan shekarar ne a birnin Gada Malam Muhammadu Bello dan Shehu Usmanu, ya tsaga kasar Katsina biyu Gabas da Yamma gari saba’in saba’in tsakanin shi Malam Sambo din da kuma Malam Umarun Dallaje, tun daga wannan lokaci ne kuma garin Gusau da masarautarsa suke ci gaba da bunkasa ta hanyoyi daban-daban.

Kafin rasuwar Malam Sambo an yi wani lokaci da hedkwatar wannan masarauta ta koma garin Wonaka sakamakon rashin cikakken tsaro kuma a dalilin namun daji masu hadari, Sai bayan rasuwar Malam Sambo dansa Sarkin Katsina Malam Abdulkadir ya dawo da wannan hedkwatar a mazauninta na farko wato Gusau, a dai dai wannan lokaci ne kuma aka nada Sarkin Musulmi Atiku dan Shehu a lokacin da Malam Abdulkadir ya tafi mubaya’a sai ya labarta wa Amirul muminina wannan ci gaba da aka samu, shi kuma Sarkin Musulmi a nasa bangaren bai yi wata wata ba sai ya umurci Sarkin Zamfara Jibrin da Sarkin kaura Namoda da cewa su sa hannu a kewaye garin Gusau da ganuwa wanda a sakamakon wannan aiki ne garin a matsayinsa na hedkwatar masarautar ta sami kokofi guda tara (9) da suka hada da: kofar Kwatarkwashi, da kofar Katsaura da kofar Rawayya da kofar Jange da kofar Dogo da kofar Mani da kofar Tubani da kofar Koje da kuma kofar matsattsa.

Tsarin Mulkin masarautar Gusau[gyara sashe | gyara masomin]

A takaice dai garin Gusau yana da masarauta daya mai babban sarki, akwai kuma iyayen kasa goma sha hudu, ‘yan majalisar sarki goma sha takwas, sarautun fada kuma akwai kimanin dari da hudu, Garin yana da masallatan juma’a ashirin da uku yana da kananan makarantun boko guda sittin da hudu matsakaita guda arba’in da uku sannan akwai manyan makarantu guda hudu.

Garin Gusau gari ne da yake da manyan kasuwanni guda uku yana kuma da kamfanoni na ‘yan kasuwa guda ashirin da bakwai akwai manyan malaman addinin Musulunci tsakanin rayayyu da wadanda suka rasu kimanin sittin da biyar.

Daga lokacin da aka kafa garin Gusau bayan malam Sambo dan Ashafa a 1806- zuwa 1827 an yi sarakuna daga cikin zuri’arsa irin su.

Masarautar Gusau a alif Dari takwas da ashirin da bakwai (1827-1917)[gyara sashe | gyara masomin]

Daga wannan shekarar anyi wasu Sarakuna da ba a fadi sunayensu ba daga 1917-1984 sannan sai *Alhaji Muhammadu Kabir danbaba (1984 -2015)

Yiwa masarautar gyaran fuska=[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta dubu biyu da uku 2003 da aka zabi Alhaji Ahmad Sani Yeriman Bakura gwamnan Jihar Zamfara shi ma ya kara sake fasalin majalisar, masarautar ta Gusau inda ta koma kamar haka.

Daga karshe iyayen kasa kuma da suke karkashin wannan masarauta ta Gusau da ake kira Katsinan Gusau, sun hada da Galadima da Mayana da Madawaki da Magajin Sabon Gari da Baraden Tudun Wada da Sarkin Kudun Damba da Ubandoman wanke da Farimanan Magani da Sarkin Yakin Rijiya da Magajin Mada da Kogon Wonaka ta Yamma da Magajin Ruwan Baure.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

[1] [2]

  1. https://punchng.com/banditry-months-after-no-fly-order-fg-shuts-down-telecom-sites-in-zamfara/
  2. Nwannah, Ifeanyi (2022-08-06). "Zamfara govt commends House of Assembly for passing Social Protection Bill into law". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-08-08.