Jump to content

Masarautar Nembe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Nembe
masarautar gargajiya a Najeriya
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 4°32′N 6°25′E / 4.53°N 6.42°E / 4.53; 6.42
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Bayelsa

Masarautar Nembe jiha ce ta gargajiya a yankin Neja Delta.Ta haɗa da ƙananan hukumomin Nembe da Brass[1] na jihar Bayelsa,[2] Najeriya. Sarakunan gargajiya suna daukar taken “Amanyanabo”.[ana buƙatar hujja] A yau[3] ta rabu tsakanin Amanyanabos na Ogbolomabiri, Bassambiri, Okpoama, Odioama da Twon Brass.[4]

Nembes ’ ƴan ƙabilar Izon ne na yankin Neja-Delta, sun zauna a yankin da ya haɗa da dajin Edumanom.[5] Ba a san ranar kafuwar tsohuwar masarautar Nembe ba. Al'ada ta ita ce ana kiran sarki na goma Ogio, yana mulki a kusan shekarar 1639, kakan duk sarakunan da suka biyo baya. Daga baya yaƙin basasa ya raba garin gida biyu. A farkon ƙarni na 19, sarki Ogbodo da mabiyansa suka koma wani sabon mazauni a Bassimibiri, yayin da sarki Mingi ya zauna a birnin Nembe.[6]

Da zuwan Turawa a bakin teku, masarautar Nembe ta zama ƙasa ta kasuwanci, amma ta kasance matalauta idan aka kwatanta da Bonny da kuma Calabar.[7] [8]

Kasuwancin bayi na Nembe ya samo asali ne a cikin kwata na biyu na ƙarni na 19 lokacin da Burtaniya ta yi yunƙurin daƙile cinikin bayi a Afirka ta hanyar toshe tashar jiragen ruwa na Bonny da Calabar. Matsayin garin Nembe mai nisan mil 30 da Kogin Brass ya zama mai fa'ida a cikin waɗannan yanayi.[9] Duk da haka, tare da raguwar buƙatar bayi, a shekara ta 1856 cinikin dabino ya zama mafi mahimmanci kuma ciniki ya koma garin [Twon-Brass]] a bakin teku.[8] A cikin ƙarni na 19 na ƙarshe, mishan na Kirista[10] sun ba da gudummawa ga tashe-tashen hankula tsakanin Nembe. Ogbolomabiri ya sami aikin Kirista a 1867, yayin da Bassambiri ya kasance "heathen".[7]

Bayan shekara ta 1884, an haɗa masarautar Nembe a cikin yankin da Birtaniyya ta yi iƙirarin ikon mallaka a matsayin wani ɓangare na Kare Kogin Mai. Nembe, wanda a yanzu ke sarrafa cinikin dabino, da farko ta ƙi sanya hannu kan wata yarjejeniya, kuma ta nemi hana Kamfanin Royal Niger samun ikon mallakar kasuwanci.[6] A cikin Janairu 1895 Sarkin Nembe William Koko ya jagoranci harin wayewar kai na mayaka fiye da dubu a hedkwatar kamfanin a Akassa. Wannan ya haifar da wani hari na ramuwar gayya wanda wani rundunar[11] da Sir Frederick Bedford ke jagoranta suka kama Nembe gami da korarsa, wanda ya faru a lokaci guda[12] na ɓarkewar cutar sankarau a cikin Masarautar. [6] Daga baya turawan ingila sun kafa ƙaramin ofishin jakadanci a Twon-Brass, daga nan ne suke gudanar da yankin. An sake shigar da sarakunan gargajiya a cikin 1920s, amma tare da ainihin wani alama na nuna matsayi, wanda suke riƙe da shi a yau.[13]

Ogbolomabiri

[gyara sashe | gyara masomin]

Sarakunan Ogbolomabiri:[14]

Fara mulki Gama mulki Mai mulki
1745 1766 Mingi I
1766 1788 Ikata Mingi II
1788 1800 Gboro Mingi III
1800 1832 Kuko Mingi IV "King Forday"
1832 1846 Amain Mingi V "King Boy"
1846 1846 Kuki
1846 1863 Kien Mingi VI
1863 1879 Joshua Constantine Ockiya Mingi VII
1879 1889 (babu)
1889 1896 Frederick William Koko Mingi VIII (d. 1898)
1896 1926 (babu)
1926 1939 Joshua Anthony O. Ockiya Mingi IX (BC1873 - d. 1939
1939 1954 (babu)
1954 1979 Francis O. Joseph Allagoa Mingi X (d. 1979)
1979 2007 Ambrose Ezeolisa Allagoa Mingi XI (b. 1914 – d.
Fabrairu 23, 2008 Edmund Maduabebe Daukoru, Mingi XII (b. 1943)

Daga baya sarakunan Bassambiri:[14]

Fara mulki Gama mulki Mai mulki
1870 Arisimo "King Peter"
1870 1894 Ebifa
1894 1924 (babu)
1924 1927 Albert Oguara
1928 Ben I. Warri
1978 1993 King Collins Festus Amaegbe-Eremienyo Ogbodo VII An haife shi a ranar 29 ga Nuwamba 1930 ya rasu Yuli 1993 kuma an binne shi a 1994.
1996 2013 Ralph Michael Iwowari, Mein VII B1930, an binne shi a watan Nuwamba 2014

Biyu / Brass

[gyara sashe | gyara masomin]
Fara Ƙarshe Mai mulki
  1. "Nigeria: Administrative Division (States and Local Government Areas) - Population Statistics, Charts and Map". www.citypopulation.de. Retrieved 2022-03-09.
  2. "Bayelsa State Government – The Glory of all Lands" (in Turanci). Archived from the original on 2022-03-07. Retrieved 2022-03-10.
  3. "leadership - Google Search". www.google.com. Retrieved 2022-03-10.
  4. "Nembe Bassambiri". Nembe Ibe USA. Archived from the original on 14 July 2011. Retrieved 17 September 2010.
  5. "The Niger Delta – Niger Delta Budget Monitoring Group" (in Turanci). Retrieved 2021-09-17.
  6. 6.0 6.1 6.2 Mogens Herman Hansen (2000). A comparative study of thirty city-state cultures: an investigation. Kgl. Danske Videnskabernes Selskab. p. 534. ISBN 87-7876-177-8.
  7. 7.0 7.1 G. I. Jones (2001). The trading states of the oil rivers: a study of political development in Eastern Nigeria. James Currey Publishers. p. 85ff. ISBN 0-85255-918-6.
  8. 8.0 8.1 Joanne Bubolz Eicher (1995). Dress and ethnicity: change across space and time. Berg Publishers. pp. 168–169. ISBN 1-85973-003-5.
  9. "Circumstances - Definition, Meaning & Synonyms". Vocabulary.com (in Turanci). Retrieved 2022-03-11.
  10. "Missionary - Definition, Meaning & Synonyms". Vocabulary.com (in Turanci). Retrieved 2022-03-11.
  11. "Expeditionary - Definition, Meaning & Synonyms". Vocabulary.com (in Turanci). Retrieved 2022-03-10.
  12. "Devastating - Definition, Meaning & Synonyms". Vocabulary.com (in Turanci). Retrieved 2022-03-10.
  13. "Tourism in Bayelsa State". Bayelsa State Union of Great Britain and Ireland. Archived from the original on 1 March 2010. Retrieved 5 March 2010.
  14. 14.0 14.1 "Traditional States of Nigeria". WorldStatesmen.org. Retrieved 14 September 2010.