Mata a cikin fasahar Afirka
Women in Tech Africa (WiTA)' ƙungiya ce da ke mai da hankali akan faɗaɗɗen 'yan kasuwa da haɓakan adadin mata a fasaha, musamman matan Afirka wanda Ethel D Cofie ne ya kafa ta.[1] A cikin shekarun da suka gabata, WiTA ta mai da hankali akan dabarun baiwa mata damar fitar da labarin ci gaban Afirka wanda ya haifar da tasiri kan rayuwar mutum ta hanyar fasaha zamani. A halin yanzu, masu sauraron sa sun ƙunshi ƴan kasuwa mata masu shekaru 18 zuwa 40. Mata a fasaha a Africa ita ce rukuni mafi girma a nahiyar da ke da mambobi a cikin ƙasashe 30 a duniya tare da rassan a ƙasashe kamar Ghana, Malawi, Zimbabwe, Somaliya, Jamus, Ayilan, Kenya, Tanzaniya da Mauritius[2]
Makasudai ƙungiyan WiTA
[gyara sashe | gyara masomin]- Ƙarfafa ƙwarin gwiwar mata don fasaha da ɗaukar matsayi na jagoranci a fannonin fasaha.
- Ƙirƙirar hanyoyi na mata don zaɓar sana'o'in fasahan zamani.
- Ƙarfafa mata shiga cikin fasaha na kasuwanci.
Manyan Aiyukan WiTA
[gyara sashe | gyara masomin]- Mata a Makon Fasaha (WiTW)
Wannan bikin na dijital yana kawo mata masu fasaha a duniya su zama a tare don murnar nasara da tasiri ta hanyar horar da jagoranci, koyan takwarorinsu, da kuma tarurrukan bita.[3] Batutuwan da aka fi maida hankali akai sun shafi fasaha, kasuwanci, ma'aunin aiki-rayuwa, da jagoranci. Masu sauraro na waɗannan abubuwan gaba ɗaya sun ƙunshi mata 'yan kasuwa na fannin fasaha, 'yan mata masu neman sana'o'in Fasaha da matakan zartarwa na zamani. Wadannan abubuwan sun fi mayar da hankali ba kawai ga mata a Afirka ba amma matan Afirka a duk faɗin duniya. A halin yanzu, WiTW ta sami amincewa daga Gidauniyar Graca Machel Trust.