Mirella Ricciardi
Mirella Ricciardi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kenya, 14 ga Yuli, 1931 (93 shekaru) |
ƙasa | Kenya |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mai daukar hoto |
Mirella Ricciardi (an haife ta a ranar 14 ga watan Yulin shekara ta 1931) 'yar kasar Kenya ce Kuma ta kasance mai daukar hoto kuma babbar marubuciya.[1][2] Ta kuma fito a fim din Michelangelo Antonioni na 1962 L'Eclisse, tana taka rawar gani sosai .
Rayuwa ta farko
[gyara sashe | gyara masomin]Mirella Rocco ita ce 'yar Mario Rocco (shekara 1893 zuwa shekara ta 1975) da Giselle Bunau-Varilla (shekara ta 1892 zuwa shekara 1978). Mahaifinta, wanda ya fito ne daga Naples, jami'in sojan doki ne na kasar Italiya wanda ya shiga Yaƙin Duniya na farko . Mahaifiyarta 'yar asalin kasar Faransa ce wacce ta kasance ɗalibar Rodin.[3] Iyayenta biyu sun yi aure (amma ba tare da juna ba) lokacin da suka tashi zuwa Afirka a ƙarshen shekara ta 1928. [4] Da farko sun shirya su tsere a Belgian Congo kuma su yi arziki ta hanyar kashe giwaye da sayar da hauren giwa. Kuma bayan safari na shekara guda Giselle ta yi juna biyu kuma ma'auratan sun tafi kasar Kenya don zuwa asibiti.[3] Daga karshe sun zauna a kasar Kenya lokacin da aka haifi babban ɗan'uwan Mirella, Dorian Rocco (shekara ta 1930 zuwa shekara ta 2013). An haifi ƙarami daga cikin yara uku, Orla, a shekara ta 1933.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Vanishing Africa: The poignant tale and images of Mirella Ricciardi". Afritorial. 1 October 2012. Archived from the original on 16 October 2017. Retrieved 19 July 2017.
- ↑ Ciugu Mwagiru (22 August 2015). "They put Kenya on world map, so why the hatred?". Daily Nation (online), Nairobi. Retrieved 19 July 2017.
- ↑ 3.0 3.1 Nicki Grihault (17 September 2003). "Hunter's daughter who saved the elephants". This source is more directly concerned with Mirella Ricciardi's younger sister who married a young Scottish zoologist and became Oria Douglas-Hamilton. Daily Telegraph, London. Retrieved 19 July 2017.
- ↑ Fiametta Rocco (21 September 2003). "The Miraculous Fever-Tree (First chapter extract placed online)". New York Times. Retrieved 19 July 2017.