Muhammad Ali
Muhammad Ali (sunan yanka Cassius Marcellus Clay Jr.; an haife shi a ranar 17 ga Watan Janairu, shekarar 1942 ya rasu; a ranar 3 ga Watan yuni ,shekarar 2016) dan wasan dambe ne dan kasar Amurika. Yana daga cikin manyan yan damben duniya. a shekarar 1999, muhimmiyar mujallar wasanni ta bawa Muhammad Ali matsayin babban dan wasa na karni. yadau gasar damben masu nauyi matakin karshe a duniya har sau uku. Hakanam ma Ali ya yacinye gwal a gasar wasanni ta Olympics a shekara ta 1960 a birnin Roma. Ana ganin Ali da muhimmancin gaske.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a Louisville, inda aka rada masa sunan banan shi Cassius Marcellus Clay Sr. Ali ya sake suna bayan ya musulinta a shekara ta 1965. Saboda addinin sa Ali baiyi wasaba a lokacin yakin Vietnam. Wannan lamarin ya kara fito da Ali fili. Ali yabar wasanni a shekarar 1981. A farkon shekarun 1980 aka gano Ali yana dauke da cuta.[1][2] Ali yayi suna sosai bisa ga aiyukansa na taimako, sadaka da jinkan al'uma.
Muhammad Ali ya shiga Musulunci a shekarar 1960.
Muhammad Ali yayi aure sau hudu ne a rayuwar sa. Kuma yana da yaya mata bakwai da maza biyu.
A ranar 20 ga watan Disamba ,shekarar 2014, Aka kai Ali asibiti.[3] A Janairu 15, 2015 aka sake maisasshe shi.[4][5] Kashe gari aka sallame shi.[6]
Lafiya da rasuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An samu Ali yana dauke da cutar ':Parkinson's disease.[7] Ali ya rasu Yunk 3, 2016, yana da shekaru 74.[8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Thomas Jr., Robert McG. (September 20, 1984). "Change In Drug Helps Ali Improve". The New York Times. pp. D–29. Retrieved March 19, 2009.
- ↑ "Ali Leaves Hospital Vowing to take better care of himself and get more sleep". The New York Times. September 22, 1984. Retrieved March 9, 2009.
- ↑ "Muhammad Ali hospitalized with pneumonia". The Journal.com. Retrieved December 21, 2014.
- ↑ "Boxing legend Muhammad Ali in hospital after being found 'unresponsive' at his home". Mirror.com. January 15, 2015. Retrieved January 16, 2015.
- ↑ "Muhammad Ali back in hospital after he was found 'unresponsive in his bed' - just days after the boxing great's 73rd birthday". Daily Mail. January 15, 2015. Retrieved January 16, 2015.
- ↑ "Ali out of hospital in time for 73rd birthday". MSN.com. Retrieved January 17, 2015.
- ↑ https://www.bbc.co.uk/news/health-36455016
- ↑ "Muhammad Ali dies". The Sydney Morning Herald. 4 June 2016. Retrieved 4 June 2016.
__LEAD_SECTION__
[gyara sashe | gyara masomin]Muhammad Ali /ɑːˈliː/ ; an haife shi Cassius Marcellus Clay Jr .; a ranar 17 ga watan Janairu,shekarata alif 1942 zuwa ranar 3 ga watan Yuni shekarata alif 2016),ƙwararren ɗan dambe ne kuma ɗan gwagwarmaya. A shekarar 1999, ana kirashi daSportsman of the Century daga Sports Illustrated da kuma Sports Personality of the Century daga BBC.
An haifeshi Kuma ya girma a Louisville, Kentucky, ya fara horarwa a matsayin maison dambe a shekara 12. Ya musulunta bayan shekarar 1961. Ya lashe gasar zakarun ajin masu nauyi na duniya, inda ya doke Sonny Liston a wani babban bacin rai a ranar 25 ga watan Fabrairu, shekarata alif 1964, yana da shekaru 22. A lokacin wannan shekarun, ya soki/la'anta sunansa na haihuwa a matsayin"slave name" dakuma bisa ka'ida na canza sunanshi zuwa Muhammad Ali.