Jump to content

Muhammad Siddiq Al-Minshawi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muhammad Siddiq Al-Minshawi
Rayuwa
Haihuwa Al-Munsha'āh (en) Fassara, 20 ga Janairu, 1920
ƙasa United Arab Republic (en) Fassara
Kingdom of Egypt (en) Fassara
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Mutuwa Al-Munsha'āh (en) Fassara, 20 ga Yuni, 1969
Ƴan uwa
Mahaifi Siddiq El-Minshawi
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a qāriʾ (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Al-Minshawi yana karanta Suratul An'am 6:95 zuwa 6:98

Muhammad Siddiq Al-Minshawi ( Larabci: محمد صديق المنشاوي‎ ‎ 20 Janairu 1920 - 20 Yuni 1969), wanda aka fi sani da Al-Minshawi, malamin Al-qur'ani ne na Masar kuma Hafizi ne. Al-Minshawi ya fito daga cikin wani shahararren ahalin musulmi na Masar. Kakansa, mahaifinsa, da ɗan'uwansa su ma shahararrun Mahaddata ne. Al-Saut Al-Baki ( Larabci: الصوت الباكي‎), yana daga cikin ƴan huɗu, tare da Abdul Basit, Mustafa Ismail, da Al-Hussary, waɗanda ake ganin su ne mafi muhimmanci kuma shahararrun Mahaddata Al-Qur'ani a wannan zamani da suka yi tasiri a duniyar Musulunci.

Taƙaitaccen Tarihin sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan da mahaifinsa ya yi tasiri sosai, Al-Minshawi kuma ya kasance ƙwararren Muhammad Rifat,[1] Muhammad Salamah,[2] mashahuran mawallafa na ƙarni arni na 20. Ya karanci ƙa'idojin karatu a wajen Ibrahim As-Su'oodi tun yana karami. Ya ya haddace Al-Qur'ani mai girma yana da shekaru 8 a duniya.[3] Ya yi balaguro zuwa ƙasashe da dama a wajen ƙasarsa, da suka haɗa da Indonesia, Jordan, Kuwait, Libya, Falasdinu ( Al-Aqsa ), Saudi Arabia, da Syria .

Al-Minshawi kuma ya halarci karatun da akayi rekodin tare da sauran masu karatu guda biyu: Kamel al-Bahtimi da Fouad al-Aroussi.[3] Ya taimaka wa yara da karatun Alqur'ani.

Al-Minshawi ya yi aure sau biyu, ya haifi ƴa-ƴa maza uku da mace ɗaya da matar farko, maza biyar da mata huɗu tare da mata ta biyu, amma a shekarar 1968, matarsa ta biyu ta rasu a lokacin da take aikin hajji.[3]

Teburin yadda alhalin sa suke

Al-Minshawi na cikin alhalin Huffaz na gargajiya, masu sana'ar zane na rubutun larabci, da Qaris ; kuma kamar shi, mahaifinsa, Seddik Al Minshawy, da ɗan'uwansa, Mahmoud Al Minshawy, sun kasance ƙwararrun Mahaddata (Gwanaye), suma. Ɗan shi Musaf Mulaim shi ma ya zama kwararren mai mahaddaci da koyar da yara kamar yadda mahaifinsa yake yi.[1][3][4] Ya rasu a ranar 20 ga watan Yunin shekarar 1969, saboda wani ciwo da ya yi tsawon lokaci a rayuwarsa.

Abin tunawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Karatun Al Minshawi ya ci gaba da kasancewa a matsayin sananne saboda tajwidinsa da salonsa qira'ar sa.[5] Shi ne marubucin littafai da dama da suka shafi ɓangarori daban-daban na Alqur'ani. kuma yana da hannu wajen buga rubutun Alqur'ani da "World of Islam festival ".Matsayinsa na Qari yana da daukaka: Yana riƙe da laƙabin Shaykh al-Maqâri,[4] kuma kafafen yada labarai na yawan neman ra'ayinsa kuma su][ Mutum Zai iya ƙirga matasa masu ɗinbin yawa waɗanda suke kwaikwayon salon karatun sa (kamar ace matasan ƙarni ɗaya).[6] Al Minshawi ya yi karatu a gaban manya manyan mutane irin su shugaban ƙasar Masar Gamal Abdel Nasser a masallacin Umayyawa na ƙasar Siriya a shekara ta 1959. Abdel Nasser ya kuma gayyaci Sheikh al Minshawi don yin karatu a wurin jana'izar rasuwar mahaifinsa a Alexandria, 1968.[7]

  1. 1.0 1.1 "About the life of Sheikh Mohammed Siddiq Minshawi". Islamweb. Archived from the original on 18 May 2020. Retrieved 2019-08-06.
  2. الاتحاد, صحيفة (2016-11-24). "الشيخ محمد سلامة.. رفض التلاوة في الإذاعة". صحيفة الاتحاد (in Larabci). Retrieved 2022-08-03.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 "Muhammad Al-Minshawi". islamhouse.com. 14 Apr 2008. Archived from the original on 18 May 2020. Retrieved 18 May 2020.
  4. 4.0 4.1 "Reports on Death of Egyptian Quran Master Denied". iqna.ir. 25 May 2016. Archived from the original on 18 May 2020. Retrieved 18 May 2020.
  5. "Ulama on the wonder that is Muhammad Siddiq al-Minshawi". contemplatequran.wordpress.com. 25 Feb 2015. Archived from the original on 18 May 2020. Retrieved 18 May 2020.
  6. "Egyptian Qari Says Mostly Inspired by Minshawi". iqna.ir. 18 July 2017. Archived from the original on 18 May 2020. Retrieved 18 May 2020.
  7. "شائعة تاريخية .. هل رفض الشيخ محمد صديق المنشاوي تلاوة القرآن أمام الرئيس جمال عبدالناصر ؟". النصر 24. Archived from the original on 2021-12-07. Retrieved 2021-09-05.