Jump to content

Nasiru Kabara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Nasuru Kabara)
Nasiru Kabara
Rayuwa
Haihuwa 1912
Mutuwa 1996
Sana'a

Nasiru Muhammad Al -Muktar Kabara wanda aka fi sani da Nasuru Kabara (An haife shi a ranar 18 ga watan Afrilu, a shekara ta alif 1924 zuwa shekarar 1996),

An haife shi a shekara ta alif 1924, kuma ya rasu a shekara ta alif 1996. Babban fitaccen malamin Addinin Musulunci na Ɗariƙar Qadiriyya ne a jihar Kano, wanda ya kafa Darul Qadiriyya, kuma Jagoran Qadiriyya na Ƙasashen Afirka ta yamma[1] a hukumance, Ɗansa Qaribullah Nasiru Kabara ne ya gaje shi bayan rasuwar sa. Kuma mahaifin wanda ake zargi da yin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta Manzon Rahama (S A W), Abduljabbar Nasiru Kabara. Abduljabbar Nasiru Kabara wanda a yanzu haka gwamnatin jihar Kano a ƙarƙashin Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam ta turashi zuwa gidan gyara hali a jihar Kano. Mal Nasiru Kabara yana ɗaya daga cikin fitattun Malaman addinin Musulunci a Najeriya da Africa a bangaren Ɗariƙar Qadiriyya.[1][2]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Kuringawa a jihar Kano. Asali an ce kakansa ya fito daga tashar jiragen ruwa ta Kabara kusa da kogin Nijar, bayan Jihadin Usman dan Fodio a (1804-8). Daga nan ne ya yi hijira zuwa kasar Hausa, zuwa masarautar Kano a bayan ƙarni na goma sha takwas (18), inda ya zauna a gaban fadar masarautar Kano, inda aka ba shi fili don ya zauna, wanda yau an wayi gari ana kiran wajen da matsayin Kabara Ward "Unguwar Kabara".[3]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Nasiru Kabara ya sami mafi yawan iliminsa daga kawunsa kuma sanannen malamin Qadiriyya a wancan lokacin, wanda aka fi sani da Ibrahım Ahmad Al-kanawı Natsughünne, wanda yana ɗaya daga cikin fitattun malamai a Kano. Kawunsa da malaminsa sun yi hidimar sarki hudu daban -daban a matsayin mai ba da shawara kan Harker kin addini, daga cikinsu akwai Aliyu Babba, Abbas, Usman da Abdullahi Bayero, a lokacin kawun nasa yana daya daga cikin manyan membobin 'yan uwan Qadiriyya a garinsa.

Ya sanya ‘ya'yan Kabara zuwa rassa biyu na darika, wato Kuntiyya da Ahlulbaiti, wanda Shehu Usman Dan Fodio ya kafa.

Darika[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kammala karatunsa a karshen karni na 1940s, Nasiru Kabara ya mai da hankali kan haɗa kan kungiyar Qadiriyya a Kano a karkashin jagorancinsa, daga nan ya cigaba da buɗe masallatai da dama a duk faɗin ƙasar Hausa a matsayin ɓangaren ƙadiriyya, wanda hakan ya sa kuma ya zama jagoran Qadiriyya a Afirka.

Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]

Shine wanda ya assasa Darul Qadiriyya (gidan Qadiriyya) a jihar Kano, inda dukkan mabiya Qadiriyya a duk fadin Afirka ta Yamma suka dauke ta a matsayin cibiyar Qadiriyya ta Yammacin Afirka, an ba shi taken Nasuru Kabara, Al-Sinhaji, Al-ibiadiri, Al-Maliki, Al-Ash'ari, Sarkin yakin Shehu Usmanu Bin Fodiyo.[4]

Harkar Qadiriyya[gyara sashe | gyara masomin]

Rubutu[gyara sashe | gyara masomin]

Ya rubuta litattafan musulunci da dama akan Tafseer da Hadisi, wanda aka ce sun kai littattafai sama da 300.

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Nasuru Kabara yana da 'ya'ya da yawa amma fitattu sune Qaribullah Nasiru Kabara babban ɗansa kuma magajinsa, ɗayan kuma Abduljabbar Nasuru Kabara.[5] sauran sun haɗa da

 • Sheikh Ibrahim Mu'azzam Nasir Kabara
 • Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Nasir Kabara.
 • Malam Askiya Nasir Kabara
 • Malam Yahya Nasir Kabara
 • Malam Aburumana Nasir Kabara
 • Sayyidah Saratu Nasir Kabara
 • Sayyidah Nafisatu Nasir Kabara
 • Sayyidah Khudriyyah Nasir Kabara
 • Sayyidah Zam'atu Nasir Kabara 1
 • Sayyidah Saffanatu Nasir Kabara 1
 • Sayyidah Aishatu Mannubiyyah Nasir Kabara
 • Sayyidah Ummu Aimanal Habashiyyah Nasir Kabara (I)
 • Sayyidah Khadijatul Habashiyyah Nasir Kabara (II)
 • Sayyidah Huza'iyyah Nasir Kabara
 • Sayyidah Jamila Nasir Kabara
 • Sayyidah Bulkisu Nasir Kabara
 • Sayyidah Rukayya Nasuru Kabara
 • Sayyidah Hansa'u Nasir Kabara.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

 • Qaribullahi Nasiru Kabara

Haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 "Sheikh Nasir Muhammad Kabara". www.rumbunilimi.com.ng. Retrieved 2021-08-03. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
 2. "Ku San Malamanku tare da Abduljabbar Kabara". BBC News Hausa. 2020-11-06. Retrieved 24 December 2021.
 3. "Teachings and writings of Nasuru Kabara" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2021-08-06. Retrieved 2021-08-08.
 4. Tudun Nufawa, Abdulk̳adir Sammani; Sheshe, Aminu Ahmad (1997). Hasken Allah ba ya Gushewa: tarihin Sheikh Muhammad Nasuru Kabara, Al-Sinhaji, Al-K̳adiri, Al-Maliki, Al-Ash'ari, Sarkin Yak̳in Shehu Usmanu Bin Fodiyo (RA). Kano: The authors. OCLC 173037236.
 5. Malumfashi, Muhammad (2021-08-02). "An jirkita kalaman Abduljabbar – 'Yan Gidan Kabara sun zargi Malamai da sharri". Legit.ng - Nigeria news. Retrieved 24 December 2021.