Niyyah
|
Islamic term (en) | |
|
| |
| Bayanai | |
| Ƙaramin ɓangare na | niyya |
| Addini | Musulunci da Sufiyya |
| Muhimmin darasi |
Mubah (en) |
| Mabiyi |
Taklif (en) |
| Ta biyo baya | bauta a musulunci, aiki a musulunci, kyawawan aiki a musulunci, aiki da aiki |
| Commemorates (en) |
Volition of God in Islam (en) |
| Depicts (en) |
sincerity in Islam (en) |
| Ta jiki ma'amala da |
Noor (en) |
| Work available at URL (en) | corpus.quran.com… da qurananalysis.com… |
| Abu mai amfani |
'Aql (en) |

Niyyah (Larabci: نِيَّةٌ, fassarar daban-daban niyyah, niyya ar, "Niyya") Musulunci ne ya tsara haka: yin niyya a cikin zuciyar mutum don yin wani aiki na Ibadah don Allah ( Allah ).
Shar'anta/wajabcin niyyah a Musulunci ya tabbata ne a cikin Alqur'ani mai girma cikin Surah ta 33 (Suratu Al-Ahzab) Aya ta 5:
Babu laifi a cikin abinda kuka aikata a bisa kuskure, face abinda kuka aikata da niyyah. Kuma Allah shine mai gafara mafi jinƙai.
Kamar yadda Ibn Rajab ya rawaito hadisi a cikin Arba’una Hadis na Imamu Nawawi: Hadisi na 1, ana hukuncin ayyuka ne da niyya: “ Umar b. al-Khattab ya ruwaito cewa, Annabi ya ce: Lallai tabbas dukkan Ayyuka sai da niyya, kuma mutum yana samun lada ne kawai bisa ga abin da ya yi niyya." [1]
Hakazalika, niyyar mutum na da matuqar muhimmanci a cikin sharuɗɗan layya. Akwai muhawara dangane da wajabcin yin lafazin yayin Niyyah. Mafi yawan malamai sun yarda cewa, duk niyyah ana qudurta ta a zuciya ne, ba sai an furta ta ba a baki. Bugu da ƙari, babu wata shaida da ke nuna cewa Annabin Musulunci Muhammad (S A W) ko wani daga cikin sahabbansa sun taɓa yin niyya da a bayyane kafin salla.
Dole ne musulmi ya kasance ya ƙulla niyya kafin ya fara sallah, da kuma fara aikin Hajji a ( Makka ).
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Commentary: Hadith "Deeds are by Intentions"". sunnah.org. Archived from the original on February 23, 2020. Retrieved 2021-06-11.