Okwesilieze Nwodo
Okwesilieze Nwodo | |||||
---|---|---|---|---|---|
1999 -
ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993 ← Herbert Eze - Temi Ejoor → | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Okwesilieze Emmanuel Nwodo | ||||
Haihuwa | Nsukka, 28 ga Yuli, 1950 (74 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Harshen, Ibo | ||||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Najeriya, Nsukka Kwalejin Gwamnati Umuahia University of Belgrade School of Medicine (en) University of Belgrade (en) | ||||
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Dr. Okwesilieze Nwodo (An haife shi ranar 28 ga watan Yuli 1950) a Nsukka, ɗan siyasan Najeriya ne wanda aka zaɓe shi gwamnan jahar Enugu a watan Janairu 1992 a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya. Daga baya ya zama sakataren kasa, shugaban kasa, kuma babban dan siyasane a jam'iyyar People's Democratic Party (PDP).
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Dr. Okwesilieze mamba ne a daular siyasar Nwodo. Shi ne dana ga Igwe J.U na biyu. Nwodo, wani basaraken gargajiya wanda ya fito daga Ukehe, a jihar Enugu. J.U. an nada shi Ministan Kasuwanci a tsohon yankin Gabas karkashin Firimiya Michael Okpara, sannan ya zama Ministan kananan hukumomi.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Nwodo ya yi karatun likitanci a Jami'ar Najeriya, Nsukka (1971-77). A tsakanin shekarar 1977 zuwa 1980, ya kuma kasance jami’in gida a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya da ke Enugu da kuma Asibitin Soja da ke Jos. Ya ci gaba da karatu a Royal College of Surgeons, Landan (1980) da Makarantar Kiwon Lafiya ta Belgrade, Yugoslavia ( 1980–84), yayi MB.BS a fannin Magani da Tiyata. Ya yi aiki a matsayin likitan tiyatar yara a kasar Yugoslavia da kuma birnin Birmingham na kasar Ingila, kafin ya dawo Najeriya ya dauki Aikin Likitanci a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Ukehe da Maternity (1984-1991).
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An zabi Nwodo a matsayin gwamnan jihar Enugu a watan Janairun shekarar 1992 akan tsarin NRC a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya. Ya rike mukamin har zuwa watan Nuwamba 1993, lokacin da Janar Sani Abacha ya hau mulki a juyin mulkin soja.
Sau biyu aka zabe shi babban sakataren jam’iyyar PDP a shekarar 1999-2001. A watan Oktobar shekarar 2001, Vincent Ogbulafor ya maye gurbinsa a matsayin sakataren jam’iyyar PDP. Ya yi karo da gwamnan jihar Enugu Chimaroke Nnamani a shekarar 2002. A cikin watan Disambar shekarar 2003, hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta sanar da cewa tana binciken Nwodo da sauran su kan badakalar cin hanci na biliyoyin naira da ke da alaka da shirin katin shaidar dan kasa. A shekara ta 2010, an wanke shi daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa na badakalar katin shaidar dan kasa.[1]
A shekarar 2007, ya samu lambar yabo ta kasa, Kwamandan Niger (CON), wanda shugaba Shehu 'Yar'aduwa ya ba shi. A cikin 2010, an zabe shi shugaban jam'iyyar People's Democratic Party na kasa. A shekarar 2014, kungiyar Beta Sigma Fraternity International ta zabi Dr Okwesilieze Nwodo, tsohon gwamnan jihar Enugu, a matsayin shugabanta na tsawon shekaru biyu.[2]
A jawabinsa na karramawa, Nwodo, ya hori dukkan mambobin kungiyar da su yi aiki da kyawawan manufofin da aka kafa Beta Sigma a Najeriya. Ya ci gaba da cewa, “a daidai lokacin da al’ummarmu ke fama da matsalolin zamantakewar al’umma da kuma kalubalen tsaro, ya kamata ‘yan uwa su mika hannun zumunci ga marasa galihu dake a cikin al’ummarmu. [3] Dan uwa ne ga Cif John Nnia Nwodo, wanda ya kasance ministan sufurin jiragen sama a lokacin shugaban kasa Shehu Shagari, sannan kuma ya sake zama ministan yada labarai a karkashin shugaba Abdusalami Abubakar. A halin yanzu Cif John Nwodo shine shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo na 9. Dr. Okwesilieze kuma dan uwa ne ga Dokta Joseph Nwodo, dan takarar shugaban kasa a zaben shugaban kasar Najeriya a 1993.