Patricia Etteh
Patricia Etteh | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
ga Yuni, 2011 - District: Ayedaade/Irewole/Isokan
6 ga Yuni, 2007 - 30 Oktoba 2007 ← Aminu Bello Masari - Dimeji Bankole →
1999 - | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 17 ga Augusta, 1953 (71 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Jami'ar Abuja | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa |
Alliance for Democracy (en) Peoples Democratic Party |
Patricia Olubunmi Foluke Etteh (an haife ta ranar 17 ga watan Agusta, 1953)[1] ita ce Shugabar Majalisar Wakilan Nijeriya daga watan Yuni zuwa watan Oktoban shekara ta 2007.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Etteh, Bayarabiya ce[2] an haife ta kuma a ranar 17 ga watan Agusta shekarar 1953.[1][3] Ta yi karatu akan gyaran gashi da kuma mai ilmin gyaran jiki, amma kuma ta samu digirin lauya daga Jami’ar Bukingham da ke Ingila kuma ta zama Lauyan Najeriya[4] a shekarar 2016.
Harkar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Etteh na wakiltar mazaɓar Ayedaade / Isokan / Irewole a jihar Osun Da farko an zaɓe ta a shekarar 1999 a matsayin mamba ta Alliance for Democracy (AD), amma ta sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) lokacin da ta sake tsayawa takara a 2003. An zaɓe ta a matsayin kakakin majalisa gaba ɗaya ga watan Yunin 2007,[5] kuma ita ce mace tilo da ta taba rike wannan mukamin a cikin gwamnatin Najeriya.[6]
Badaƙalar cin hanci da rashawa
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Satumbar 2007, ta fuskanci wani kwamiti na 'ƴan majalisar kan zarge-zargen cewa ta ba da izinin kashe Naira miliyan 628 (kwatankwacin dalar Amurka miliyan 5) a kan gyaran gidanta da na mataimakinta, da kuma sayen motocin hukuma guda 12 da aka tanada don Majalisar Wakilai. An zarge ta da satar yayinda take ƙoƙarin yin magana a cikin majalisar, kuma an fitar da ita ta hanyar tsaro yayinda lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali,[7] duk da cewa ba a gurfanar da ita a hukumance ba.
A hukumance PDP ta cigaba da mara wa Etteh baya, kodayake wasu mambobin, kamar Isyaku Ibrahim, sun soki wannan matsaya.[8] Marubuci kuma malami Wole Soyinka na daga cikin waɗanda suka yi kira da ta yi murabus,[9] yayinda tsohon Shugaban kasa kuma dan jam’iyyar PDP Olusegun Obasanjo ya cigaba da mara mata baya.[10] A ranar 30 ga Oktoba, bayan matsin lamba na makonni, Etteh ta yi murabus daga matsayinta na kakakin majalisa. [11] Mataimakin ta, Babangida Nguroje shi ma ya yi murabus. Koyaya a wurin zama na karshe na zaman majalisar wakilai karo na 6, an amince cewa "Babu wani rikodi ko cigaban majalisar inda aka taba gurfanar da Patricia Olubunmi Etteh,"[12]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Etteh moves birthday party to US". Nigerian Tribune online. African Newspapers of Nigeria. 15 August 2007. Archived from the original on 26 September 2007. Retrieved 15 August 2007.
- ↑ Bamidele, Yemi (19 September 2007). "Adedibu – 'Etteh is Yorubas' Only Hope'". Daily Trust. Media Trust Limited, via allAfrica.com. Retrieved 20 October2007.
- ↑ "Honourable Patricia Etteh". NassNig.org. National Assembly of Nigeria. Archived from the original on 12 October 2007. Retrieved 7 October2007.
- ↑ "Former House of Reps Speaker, Patricia Etteh, among 4,225 new lawyers". Vanguard Online. Vanguard.
- ↑ "Homepage". The Nation Newspaper. Retrieved 8 March 2022.
- ↑ "Mark, Etteh, emerge Senate President, Speaker". IndependentNGonline.com. Daily Independent. 6 June 2007. Archived from the originalon 25 October 2007. Retrieved 15 August 2007.
- ↑ "Nigerian MPs brawl over speaker". BBC News. BBC. 20 September 2007. Retrieved 14 October2007.
- ↑ Izang, Atang (7 October 2007). "Etteh – PDP Endorsed Corruption – Isyaku Ibrahim". Leadership. Leadership Newspapers Group, via allAfrica.com. Retrieved 14 October 2007.
- ↑ Ekenna, Geoffrey (5 October 2007). "Resign, Soyinka tells Etteh". The Punch. Archived from the original on 15 July 2011. Retrieved 7 October2007.
- ↑ Nyam, Philip. "Etteh: Countdown To 16 October". Leadership. Leadership Newspapers Group. Archived from the original on 13 July 2011. Retrieved 14 October 2007.
- ↑ "Nigeria's parliamentary speaker quits over corruption scandal", Associated Press (International Herald Tribune), 30 October 2007.
- ↑ "Nigeria speaker goes in graft row" Archived 20 January 2016 at the Wayback Machine, BBC News, 30 October 2007.