Wole Soyinka
Akinwande Oluwole Babatunde Soyinka (Yarbanci: Akínwándé Olúwo̩lé Babátúndé S̩óyíinká; an haife shi ne a 13 ga watan Yulin shekara ta 1934), wanda aka sani da Wole Soyinka (lafazin [wɔlé ʃójĩnká]), ɗan wasan kwaikwayo ne na Nijeriya, mawaƙi kuma marubuci. An ba shi lambar yabo ta Nobel ta adabi a shekara ta 1986, mutum na farko a sub-saharan Africa da aka girmama a wannan rukunin. An haifi Soyinka a cikin dangin Yarbawa a Abeokuta. A 1954, ya halarci Kwalejin Gwamnati a Ibadan, sannan ya halarci Kwalejin Jami'ar Ibadan da Jami'ar Leeds a Ingila. Bayan ya yi karatu a Najeriya da Ingila, ya yi aiki tare da gidan wasan kwaikwayo na Royal Court da ke Landan. Ya ci gaba da rubuta wasannin kwaikwayo waɗanda aka samar a ƙasashen biyu, a gidajen kallo da rediyo. Ya taka rawar gani a tarihin siyasar Najeriya da gwagwarmayar neman 'yanci daga Burtaniya. A shekarar 1965, ya kwace gidan watsa labarai na Yammacin Najeriya ya watsa shirye-shiryen neman a soke zaben yankin Yammacin Najeriya. A shekara ta 1967, a lokacin yaƙin basasar Najeriya, gwamnatin tarayya ta Janar Yakubu Gowon ta tsare shi tare da sanya shi a kurkuku na tsawon shekaru biyu.