Phillip Asiodu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Phillip Asiodu
Rayuwa
Haihuwa Delta, ga Faburairu, 1934 (90 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta The Queen's College (en) Fassara
King's College, Lagos (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Phillip Asiodu, (CON) (an haife shi ranar 19 ga watan Fabrairun 1934) ɗan Diflomasiyar Najeriya ne, Ofishin Jakadanci kuma tsohon Ministan Man Fetur, Najeriya.[1][2]

Rayuwa da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Phillip a ranar 26 ga watan Fabrairun 1934, a jihar Legas, kudu maso yammacin Najeriya. Ya halarci Kwalejin King da ke Legas kafin ya wuce Queen's College, Oxford inda ya yi digiri na biyu a fannin Falsafa.[3][4] Ya shiga aikin farar hula na Najeriya a cikin shekarar 1964 ya kuma zama babban sakataren gwamnatin tarayya, kuma ya fara aiki a ƙarƙashin Janar Gowon kafin yaƙin Najeriya da Biyafara. Ya taka rawar gani wajen karkata yarjejeniyar Aburi da Gowon ya yi.[5] Daga nan ya zama mai ba shugaban tarayyar Najeriya shawara na musamman Alhaji Shehu Shagari kan harkokin tattalin arziƙi.[6][7][8] A cikin shekarar 1999, an naɗa shi babban mai baiwa tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo shawara kan tattalin arziƙi.[9][10][11] Daga cikin sauran ayyukan jagoranci sun haɗa da tsarawa da aiwatar da manufofin man fetur da iskar gas na Najeriya. Ya kuma halarci shawarwarin shigar Najeriya OPEC, 1971.[12]

Ƙanensa, dan wasa Sidney Asiodu ya mutu a kisan gillar da aka yi a Asaba.

Rayuwar Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A 1998, ya zama memba na jam'iyyar People's Democratic Party, kuma Amintaccen jam'iyyar.[13] A cikin shekarar 1999, ya tsaya takara a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar amma bai yi nasara ba.[14]

Kyauta[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://web.archive.org/web/20141204200751/http://www.thisdaylive.com/articles/asiodu-how-murtala-obasanjo-foisted-economic-stagnation-on-nigeria/131031/
  2. https://www.thenationonlineng.net/archive2/tblnews_Detail.php?id=49587
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2017-10-03. Retrieved 2023-03-28.
  4. https://www.vanguardngr.com/2013/04/philip-asiodu-speaks-at-oxford-cambridge-alumni-luncheon/
  5. https://books.google.com.ng/books?id=fvIxpy7ZESsC&dq=Philip+Asiodu+served+as+federal+minister+of+petroleum&pg=PA60&redir_esc=y#v=onepage&q=Philip%20Asiodu%20served%20as%20federal%20minister%20of%20petroleum&f=false
  6. https://books.google.com.ng/books?id=YxiTAgAAQBAJ&dq=Nigerian+Diplomat-+Philip+Asiodu&pg=PA78&redir_esc=y#v=onepage&q=Nigerian%20Diplomat-%20Philip%20Asiodu&f=false
  7. https://www.vanguardngr.com/2011/12/main-reason-gowon-was-toppled-by-philip-asiodu/
  8. https://web.archive.org/web/20141204112331/http://news.biafranigeriaworld.com/archive/2004/feb/26/0048.html
  9. https://web.archive.org/web/20150329055444/http://www.highbeam.com/doc/1G1-73739037.html
  10. https://web.archive.org/web/20141219123243/http://businessdayonline.com/2013/11/of-nigerias-refineries-proposed-sale-and-failed-attempts/
  11. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-08-07. Retrieved 2023-03-28.
  12. https://books.google.com.ng/books?id=1KBP7QbalX0C&dq=Phillip+Asiodu+Join+PDP&pg=PA781&redir_esc=y#v=onepage&q&f=false
  13. https://www.vanguardngr.com/2014/10/delta-2015-intrigues-anioma-battle-pdp-ticket/
  14. https://www.nae.ng/fellows_profiles.asp?id=24[permanent dead link]
  15. https://web.archive.org/web/20141006072847/http://newtelegraphonline.com/service-chiefs-eight-governors-others-make-national-honours-list/

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]