Jump to content

Remi Sonaiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Remi Sonaiya
Rayuwa
Haihuwa Jahar Ibadan, 2 ga Maris, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Cornell
Jami'ar Obafemi Awolowo
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, marubuci da educational theorist (en) Fassara

Oluremi Comfort Sonaiya (an haife shi a 2 ga Maris din shekarar 1955), yar siyasan Nijeriya ce, masaniyar ilmi kuma marubuciya.[1] Ta kasance mace ta farko da ta fara tsaya wa takarar kujerar shugaban kasa a Najeriya a zaben shekara ta 2015 a karkashin jam'iyyar KOWA.[2][3] Amma kwanan nan ta rasa takarar ta a hannun Dr. Adesina Fagbenro Byron don sake wakiltar jam’iyyar a zaben shekara ta 2019.[4][5]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sonaiya a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda ta kammala karatun ta na firamare da sakandire a makarantar St. Luke's Demonstration School, Ibadan da kuma St. A shekarar 1977, ta kammala karatun ta a Jami’ar Ife ( wacce a yanzu ake kira Jami’ar Obafemi Awolowo), inda ta karanci Faransanci.[6]

Daga baya ta samu digiri na biyu a fannin adabin Faransanci a jami’ar Cornell da ke Amurka, sannan ta sake samun digiri na biyu a fannin ilimin harsuna daga wata jami’a a Najeriya a shekarar 1984. Ta koma jami'ar Cornell ne a shekara ta 1988 don karatun PhD a fannin ilimin harshe.[7]

A shekarar 1982, an dauke ta aiki matsayin mataimakiyar malami a Sashen Harsunan kasashen Waje, a Jami’ar Obafemi Awolowo kafin ta kai matsayin Farfesa a Fannin Harshen Faransanci da Kimiyyar Harshe a shekara ta 2004.[8] Ita mabiyar aikin Gidauniyar Alexander von Humboldt ce inda aka nada ta matsayin wakiliyar kimiya na gidauniyar na kimiyya daga shekara ta 2008 zuwa 2014.[7]

A shekara ta 2010 ne, ta yi ritaya daga matsayinta a Jami’ar Obafemi Awolowo kuma ta zama 'yar siyasa, a Jam’iyyar KOWA inda aka zabe ta a matsayin Jami’ar Hulda da Jama’a ta Kasa, sannan ta ci gaba da zama 'yar takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar a zaben shekara ta 2015.[9][10][11] A zaben, Sonaiya ta samu kuri'u 13,076 kuma ta kare a matsayi na 12.[12]

Littattafai

[gyara sashe | gyara masomin]

Sonaiya marubuciya ce ga jaridar The Niche,[13][14] jaridar gidan yanar gizo ta Najeriya, Sonaiya ta buga littattafai da dama da suka hada da:

  • Culture and Identity on Stage: Social-political Concerns and Enactments in Contemporary African Performing Arts (2001) ISBN 9789782015785
  • Language Matters: Exploring the Dimensions of Multilingualism (2007)[15]
  • A Trust to Earn – Reflections on Life and Leadership in Nigeria (2010)[16] ISBN 9789789115983  
  • Igniting Consciousness – Nigeria and Other Riddles (2013) ISBN 9785108473
  • Daybreak Nigeria – This Nation Must Rise! (2014) ISBN 9789785205732

Ta auri Babafunso Sonaiya, farfesa a fannin kimiyyar dabbobi, kuma suna da ɗa daya, da mace ɗaya da jikoki.[6]

  1. "Nigeria's first female presidential candidate done with 'cheerleading'". Vanguard News. March 18, 2015. Retrieved July 17, 2016.
  2. "McBain, Will (March 26, 2015). "Nigeria election: The country's first-ever female presidential candidate hoping to inspire other women to become politically active". The Independent. Retrieved July 17,2016.
  3. "Exclusive Interview With Professor Remi Sonaiya, KOWA Candidate For President of Nigeria". Sahara Reporters. February 7, 2015. Retrieved July 17,2016.
  4. "Fagbenro Byron Emerges as (KOWA) partys President candidate". Pulse.ng. Retrieved February 11, 2020.
  5. "Sanni, Kunle (September 30, 2018). "2019: KOWA Party announces presidential candidate". The Premium Times, Nigeria. Retrieved March 11, 2019.
  6. 6.0 6.1 "Biography". Retrieved July 17, 2016
  7. 7.0 7.1 "Varghese, Johnlee (March 12, 2015). "Nigeria Elections 2015: Who is Comfort Remi Sonaiya, the Only Female Presidential Candidate?". International Business Times. Retrieved July 17, 2016.
  8. "Agbonkhese, Josephine (February 8, 2015). "I'm rebuilding Nigeria into a nation that works— Remi Sonaiya, presidential candidate". Vanguard News. Retrieved July 17, 2016.
  9. "Ordinary Citiziens [sic] Like Me Can Be President Too – Sonaiya". Channels TV. January 7, 2015. Retrieved July 17, 2016.
  10. "Soyinka receives Presidential Candidate, Remi Sonaiya, in Lagos". Premium Times. March 26, 2015. Retrieved July 17, 2016.
  11. "Odunsi, Wale (May 25, 2016). "2019: Ignore APC, PDP, explore other options – Ex-presidential candidate, Remi Sonaiya urges Nigerians". Daily Post. Retrieved July 17, 2016.
  12. "Summary of Results" (PDF). Independent National Electoral Commission. p. 1. Retrieved July 18,2016.
  13. "Johnson-Salami, Laila. "Professor Remi Sonaiya, breaking down barriers for Nigerian women". rizing.org. Retrieved July 19, 2016.
  14. "There was no way I could have worked with Jonathan – KOWA Party's Remi Sonaiya – Olisa.tv". olisa.tv. Retrieved July 19, 2016.
  15. Remi Sonaiya (2007). Language Matters: Exploring the Dimensions of Multilingualism. Obafemi Awolowo University Press.
  16. "There was no way I could have worked with Jonathan – KOWA Party's Remi Sonaiya – Olisa.tv". olisa.tv. Retrieved July 19, 2016.