Richard Howitt (dan siyasa)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Richard Howitt (dan siyasa)
member of the European Parliament (en) Fassara

1 ga Yuli, 2014 - 1 Nuwamba, 2016 - Alex Mayer
District: East of England (en) Fassara
Election: 2014 European Parliament election (en) Fassara
member of the European Parliament (en) Fassara

14 ga Yuli, 2009 - 30 ga Yuni, 2014
District: East of England (en) Fassara
Election: 2009 European Parliament election (en) Fassara
member of the European Parliament (en) Fassara

20 ga Yuli, 2004 - 13 ga Yuli, 2009
District: East of England (en) Fassara
Election: 2004 European Parliament election (en) Fassara
member of the European Parliament (en) Fassara

20 ga Yuli, 1999 - 19 ga Yuli, 2004
District: East of England (en) Fassara
Election: 1999 European Parliament election (en) Fassara
member of the European Parliament (en) Fassara

19 ga Yuli, 1994 - 19 ga Yuli, 1999
District: Essex South (en) Fassara
Election: 1994 European Parliament election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Reading (en) Fassara, 5 ga Afirilu, 1961 (62 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Makaranta Lady Margaret Hall (en) Fassara
University of Hertfordshire (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Wurin aiki Strasbourg da City of Brussels (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Labour Party (en) Fassara
richardhowittmep.com

Richard Stuart Howitt (an haife shi a ranar 5 ga watan Afrilun 1961) ɗan siyasa ne na Jam'iyyar Labour da ke Biritaniya, kuma tsohon[1] Babban Jami'in Gudanarwa na International Integrated Reporting Council. Shekaru biyar kafin ya zama Shugaban IIRC, ya yi aiki a matsayin jakadan IIRC na sa kai, ya kasance mai assasa Haɗin kai a cikin manufofin da al'ummomin kasuwanci. Ya karɓi ragamar mulki daga hannun shugaban kamfanin da ya gabata wato Paul Druckman.[2] Ya kasance memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) tsawon shekaru 22 tun daga shekara ta 1994 zuwa 2016.

Fage[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Howitt a birnin Reading, Berkshire. Ya taso daga iyali na mai kula daya, a gidan kansila, sannan ya tafi makarantar firamare.[3] Ya kammala karatunsa na digiri na BA a fannin Siyasa, Falsafa da Tattalin Arziki daga Lady Margaret Hall, Oxford a shekarar 1982 kuma ya sama Diploma na Digiri a fannin Gudanarwa daga Jami'ar Hertfordshire.[4]

Bayan ya bar jami'a, ya yi aiki na tsawon shekaru huɗu a fannin ayyukan sa kai sannan kuma shekara takwas a kungiyar nakasassu.

Ayyukan siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Howitt ya rike matsayin kansila a Majalisar gundumar Harlow daga shekarun 1983 zuwa 1995, gami da shekaru uku a matsayin Shugaban majalisa. A wannan matasayi, ya jagoranci wasu gagaruman ayyuka na tantance tasirin muhallin kananan hukumomi.[5] Ya kasance dan takarar jam'iyyar Labour a Billericay a babban zaben 1987.[4]

An zabi Howitt a matsayin MEP na Majalisar Turai, mai wakiltar mazabar Essex ta Kudu, kuma ya yi aiki a mazabar Gabashin Ingila a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2016.

Howitt shine mabuɗin ginshiƙai na umarnin EU ba na kuɗi ba, ɗayan manyan sauye-sauye a cikin bayyana kamfanoni a ko'ina cikin duniya. Ya kasance mai ba da rahoto kan batutuwan da suka shafi rahoton kamfanoni, gami da alhakin zamantakewa, tsawon shekaru masu yawa. A kan wannan batu an kwatanta shi a matsayin "trailblazer".[5]

A matsayinsa na jagoran MEP kan ayykan hadin kai, Mista Howitt ya wakilci EU a kan ayyuka da yawa a duniya, yana balaguro a Asiya, Afirka da Amurka. Ya wakilci muradun Turai a cikin shirye-shiryen kasa da kasa da dama, ciki har da taron Majalisar Dinkin Duniya na Kasuwanci da Kare Hakkokin Dan Adam da Dandalin OECD kan Halayyar Kasuwanci.[6]

Howitt ya taimaka wajen bada shawarwari kan asusun Tarayyar Turai na fam miliyan 22 don taimakawa bankunan abinci na Birtaniya, amma a shekara ta 2013 gwamnatin Birtaniya ta ki karbar kudaden. Howitt ya ce:

It is very sad that our government is opposing this much-needed help for foodbanks on the basis that it is a national responsibility, when in reality it has no intention of providing the help itself. The only conclusion is that Conservative anti-European ideology is being put before the needs of the most destitute and deprived in our society.[7]

Howitt ya kasance memba na kungiyar Labour Party's National Policy Forum tsakanin 1994 da 2016.[4] Ya kuma goyi bayan Owen Smith a zaben jagoran jam'iyyar Labour na 2016.[8]

A watan Satumban 2016 ne, Howitt ya sanar da ajiye mukaminsa na Majalisar Tarayyar Turai don zama babban jami'in zartarwa na Majalisar Hadaddiyar Rahoto ta Duniya. Dan takarar jam'iyyar Labour na gaba a cikin jerin jam'iyyar daga Zaben Turai na 2014, Alex Mayer, ya maye gurbinsa a matsayin MEP.[9][10]

A watan Mayun 2021, an sake zaben shi matsayin memba na Majalisar Karamar Hukumar Cambridgeshire.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "International Integrated Reporting Council CEO Richard Howitt steps down". Accounting Today. Retrieved 22 June 2019.
  2. "IIRC appoints Richard Howitt as new chief executive - Public Finance". www.publicfinanceinternational.org.
  3. "biography". Richard Howitt. Retrieved 18 April2012.
  4. 4.0 4.1 4.2 "Richard Howitt". European Parliament. Retrieved 18 April 2012.
  5. 5.0 5.1 "Reporting lines: interview with International Integrated Reporting Council chief Richard Howitt | Public Finance". www.publicfinance.co.uk. Retrieved 16 February 2017.
  6. "Richard Howitt | Integrated Reporting". integratedreporting.org. Retrieved 16 February 2017.
  7. Watt, Nicholas (17 December 2013). "Government under fire for rejecting European Union food bank funding". The Guardian. Retrieved 22 May 2016.
  8. Smith, Mikey; Bloom, Dan (20 July 2016). "Which MPs are nominating Owen Smith in the Labour leadership contest?". Mirror. Retrieved 10 November 2018.
  9. Conor Pope (5 September 2016). "Senior MEP Richard Howitt to quit Brussels for financial services job". LabourList. Retrieved 8 November 2016.
  10. Sophie Day (27 October 2016). "East of England MEP bids farewall to European Parliament role". The Hunts Post. Retrieved 8 November 2016.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]