Rijiyar Zamzam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rijiyar Zamzam
Zamzamwill.JPG
General information
Labarin ƙasa
Geographic coordinate system (en) Fassara 21°25′21″N 39°49′35″E / 21.422568°N 39.826524°E / 21.422568; 39.826524
Kasa Saudi Arebiya
Territory Makkah
rijiyar Zamzam a makka

Rijiyar Zamzam (larabci زَمْزَم) wani rijiya ne dake a cikin Babban masallacin Makkah a birnin Mecca, ƙasar Saudiya, 20 m (66 ft) a bangaren gabashin Kabah, mafi tsarkakan wuri a musulunci. Kamar yadda Addinin Musulunci ya bayyana, rijiyar wani aya ne na ubangiji dake bayar da ruwa, wanda ya kwashe shekaru dubbai da suka shude, Ɗan annabi Ibrahim ʾIsmaʿil an barsa da mahaifiyarsa Hajara acikin kurmun sahara, inda ya rika jin ƙishirwa yayi ta kuka yanata murmuzar da kafafunsa har Mala'ika jibril (A.s) ya zo ya gina rijiyar zamzam a nan inda Isma'il ya ta murmuza kafafafunsa, sanadiyar samuwar rijiyar kenan a wannan wuri tun daga waccan lokaci. Miliyoyin mahajjata ne ke ziyartar rijiyar a duk shekara lokacin aikin Hajji ko ta Umrah saboda su samu su sha daga ruwan rijiyar na zamzam.

Anazarci[gyara sashe | gyara masomin]