Rijiyar Zamzam
Rijiyar Zamzam | |
---|---|
General information | |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 21°25′21″N 39°49′35″E / 21.422568°N 39.826524°E |
Kasa | Saudi Arebiya |
Territory | Makkah |
Rijiyar Zamzam (larabci زَمْزَم) wata rijiya ne dake a cikin Babban masallacin Makkah a birnin Mecca, ƙasar Saudiya, 20 m (66 ft) a bangaren gabashin Kabah, mafi tsarkakan wuri na musulunci. Kamar yadda Addinin Musulunci ya bayyana, rijiyar wani aya ne na ubangiji dake bayar da ruwa, wanda ya kwashe shekaru dubbai da suka shude, Ɗan annabi Ibrahim ʾIsmaʿil an barsa da mahaifiyarsa Hajara acikin kurmun sahara, inda ya rika jin ƙishirwa yayi ta kuka yanata murmuzar da kafafunsa har Mala'ika Jibrilu (A.S) ya zo ya gina rijiyar zamzam a nan inda Isma'il ya ta murmuza kafafafunsa, sanadiyar samuwar rijiyar kenan a wannan wuri tun daga waccan lokaci. Miliyoyin mahajjata ne ke ziyartar rijiyar a duk shekara lokacin aikin Hajji ko ta Umrah saboda su samu su sha daga ruwan rijiyar ta zamzam.