Rikicin Jos, 2001
Iri | riot (en) |
---|---|
Kwanan watan | Satumba 2001 |
Wuri | Jos |
Ƙasa | Najeriya |
Participant (en) | |
Adadin waɗanda suka rasu | 1,000 |
Rikicin Jos a shekara ta 2001 ya kasance tarzoma da ya shafi kiristoci da musulmi a birnin Jos na Najeriya, kan nadin wani dan siyasa musulmi, Alhaji Muktar Mohammed, a matsayin babban kodinetan shirin kawar da fatara na gwamnatin tarayya.[1] Rikicin dai ya fara ne a ranar 7 ga watan Satumba kuma ya shafe kusan makonni biyu ana gwabzawa, a ranar 17 ga watan Satumba. An kashe mutane kusan 1,000 a lokacin tarzomar.[2][3]
Dalilai
[gyara sashe | gyara masomin]Rigingimun addini da na kabilanci sun sha faruwa a garin Jos saboda yadda garin ya kasance a Najeriya. Jos, babban birnin jihar Filato, yana tsakiyar kasar ne, wanda ke tsakanin arewacin kasar da galibin Musulmi ne da kuma kudancin kasar Kiristanci. Haka kuma Jos ta shahara wajen samar da guraben ayyukan yi da ta sa mutane daga sassa daban-daban na Najeriya suka koma can domin samun aikin yi. Yawan jama'a ya haifar da tashe-tashen hankula tsakanin 'yan ƙabilar "'yan asali" (yan asali, jihar) da kuma kabilun da ba na asali ba (wanda ba yan asalin jihar ba).[4][5] A watan Yunin shekara ta 2001, gwamnatin tarayya ta naɗa wani dan siyasar kasar, bahaushe kuma Musulmi, Alhaji Muktar Mohammed, a matsayin babban kodinetan shirin kawar da fatara na gwamnatin tarayya, wanda hakan ya sa mabiya addinin Kirista suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da naɗin nasa.[ana buƙatar hujja] Kuma tashin hankali na ranar 7 ga Satumba 2001, lokacin da wata mata Kirista ta yi yunkurin tsallaka wani shingen a wajen wani masallaci a lokacin sallar Juma'a. Hakan ya haifar da rikici tsakaninta da gungun musulmi. Daga karshe fadan ya yaɗu zuwa wasu sassan birnin.[1][6]
Tarzoma
[gyara sashe | gyara masomin]Faɗan dai ya bazu a unguwannin Jos daban-daban da kuma kewaye.[6] An cinnawa dukiyoyi da ma mutane wuta. An ƙona gidaje da shaguna da masallatai da coci-coci da dama. An bar motoci da aka kona kan tituna birjik, bayan arangamar. Shugabannin Kiristocin sun ruwaito cewa, Musulmi sun kai farmaki kan Kiristoci ba zato ba tsammani tare da ƙona majami’u, ciki har da coci-coci uku na Cocin Kristi a Najeriya (wanda a yanzu ake kira, ‘Church of Christ in Nations’ COCIN), da babbar cocin Assemblies of God, da Cocin Apostolic na Jos.[1] Daga karshe dai an tura sojoji tare da dakatar da tashin hankalin.[6] Majiyoyin gida sun ce shiga tsakani da sojoji suka yi da kuma tsaurara dokar hana fita ya taimaka wajen kawo karshen faɗan.[ana buƙatar hujja]
Bayan haka
[gyara sashe | gyara masomin]Kwanaki 10 na tashin hankalin ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 1,000.[7] Saboda yawan mutanen da aka kashe a rikicin, dole ne a shirya jana’izar jama’a.[1] Rikicin ya yi sanadiyar raba fararen hula akalla dubu 50,000 daga muhallansu.[6] Hukumomin kasar sun kama mutane dari da dama tare da kafa kwamitin bincike, wanda ya gano mutanen da ake zargi da hannu a rikicin, amma babu wanda ya samu nasarar gurfanar da su, a gaban kuliya.[3]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 Obed Minchakpu (1 October 2001). "Religious Riots in Nigeria Leave Hundreds Dead". Christianity Today. Retrieved 30 November 2008.
- ↑ "300 bodies taken to mosque on 2nd day of Nigeria riots". CNN. 29 August 2008. Archived from the original on 3 February 2023. Retrieved 30 November 2008.
- ↑ 3.0 3.1 Human Rights Watch (December 12, 2013). "Leave Everything to God": Accountability for Inter-Communal Violence in Plateau and Kaduna States, Nigeria. pp. 42–43. Archived from the original on 21 April 2015. Retrieved May 5, 2015.
- ↑ Krause, Jana (2011). A Deadly Cycle: Ethno-Religious Conflict in Jos, Plateau State, Nigeria (PDF). Geneva Declaration. Archived from the original (PDF) on 7 July 2021. Retrieved 5 May 2015.
- ↑ Human Rights Watch (April 2006). “They Do Not Own This Place”: Government Discrimination Against “Non-Indigenes” in Nigeria (PDF). Retrieved 5 May 2015.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 6.3 Human Rights Watch (December 2001). Jos: A City Torn Apart (PDF). Retrieved 5 May 2015.
- ↑ Nigeria Christian and Muslim conflict timeline | Timetoast timelines. Timetoast.com.