Jump to content

Rufus Ada George

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rufus Ada George
gwamnan jihar Rivers

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Godwin Abbe - Dauda Musa Komo
Rayuwa
Haihuwa Okrika, 11 ga Yuli, 1940 (84 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Rose A. George (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rufus Ada George (An haife shi a ranar 11 ga Yulin shekarar 1940) shi ne gwamnan jihar Ribas ta Najeriya na biyu, wanda ya riƙe muƙamin daga watan Janairun shekarar 1992 har zuwa Nuwamban shekarata 1993 a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya . [1]

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ada George a ranar 11 ga Yulin shekarar 1940 a George-Ama, Okrika, Jihar Rivers. An nadashii a matsayin akawu, kuma ya zama abokin Cibiyar Akantoci na Najeriya. Ya kasance akawu a Kamfanin Raya Man Fetur na Shell na Najeriya daga Afrilu 1972 zuwa Disamban shekarata 1979, inda ya bar Mataimakin Babban Akanta zuwa Gwamnatin Jihar Ribas. A karkashin gwamnatin Cif Melford Okilo, ya kasance sakataren gwamnatin jihar kuma ya riƙe wasu mukamai da suka hada da Darakta-Janar, Daraktan Ayyuka da Darakta na Kotu. Daga baya ya zama mataimakin manajan darakta na kamfanin zuba jari na Dangil Holdings Limited (1984-1991), kafin a zabe shi gwamnan jihar Ribas. Cite error: Invalid <ref> tag; refs with no name must have content

Gwamnan Jihar Ribas

[gyara sashe | gyara masomin]

An zabi Ada George ne a Jam'iyyar National Republican Convention (NRC) a matsayin gwamnan jihar Ribas a zaɓen share fage da Janar Ibrahim Babangida ya dauki nauyi a matsayin wani mataki na tabbatar da dimokuradiyya da jamhuriya ta uku. Ya hau mulki a watan Janairun shekarar 1992. Mataimakin gwamnan shi ne Peter Odili, wanda shi kansa ya zama gwamna a shekarar 1999. A shekarar 1993 al’ummar Ogoni a jihar Ribas karkashin jagorancin kungiyar kare hakkin al’ummar Ogoni, sun nuna rashin amincewarsu da cin zarafin da Shell, tsohon ma’aikacin Ada George ke yi. An samu tashin hankali. ‘Yan Ogoni sun yi la’akari da cewa gwamnan yana karfafa rikicin. An samu tsaikon watanni biyu kafin a tura dakarun gwamnatin tarayya domin dawo da zaman lafiya.

Zaman Ada George ya kare ne lokacin da Janar Sani Abacha ya karbi mulki a juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Nuwamban shekarata 1993. Ada George ya yi ritaya a rayuwarsa har zuwa lokacin da magajin Abacha Abdulsalami Abubakar ya janye dokar hana siyasa a shekarar 1998.

Bayan ya kammala aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan komawar dimokradiyya a shekarar 1999, Ada-George ya zama shugaban jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) a jihar Ribas. An sami tashin hankali a Okrika, Jihar Ribas tsakanin 22 zuwa 24 ga Satumba 2001. A yayin wani tashin hankalin da ya barke a Okrika a shekarar 2002, wanda aka ce jam'iyyar PDP mai mulki ce ta kaddamar da shi, an kona masa gidaje guda biyu. A watan Yunin shekarar 2008 Hukumar Gaskiya da sasantawa ta jihar ta ji zargin cewa Ada George ya dauki nauyin yan iskan gari a watan Satumban 2001 da ya barke a yunkurin kafa jam’iyyar All People’s Party (APP) a yankin. [2]

Karin bayani

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Jerin Gwamnonin Jihar Ribas

Samfuri:RiversStateGovernorsSamfuri:State governors in the Nigerian Third Republic

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-09-07. Retrieved 2022-09-07.
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named onah