Son Ali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Son Ali
sarki

Rayuwa
Haihuwa 1464 (Gregorian)
ƙasa Dipper (en) Fassara
Mutuwa 1492 (Gregorian)
Yanayin mutuwa accidental death (en) Fassara (Nutsewa)
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a sarki

Sunni Ali, wanda kuma aka sani da Si Ali, Sunni Ali Ber (Ber ma'anar "Ma Girma"),[1] an haife shi ne garin a Ali Kolon.[2][3] Ya yi mulki daga tsakanin shekara ta alif 1464 zuwa 1492. Sunni Ali shi ne sarki na farko na daular Songhai, dake nahiyar Afrika kuma shine sarki na 15 na daular sunni. A karkashin umarnin Sunni Ali, an mamaye garuruwa da yawa sannan kuma aka yi musu katamga, irin su Timbuktu (wanda aka kama a shekarar 1468) da Djenné (wanda aka kama a shekarar 1475). Sunni ya gabatar da wata manufa ta danniya ga malaman Timbuktu, musamman na yankin Sankore da ke da alaka da Abzinawa wadanda Ali ya kora yayin da ya mallaki garin.

Sunni Ali ya shirya wani jirgin ruwa zuwa kogin Niger. A lokacin mulkinsa, Songhai ta zarce har zuwa daular Mali, inda ya mamaye yankunan daular Mali (da kuma daular Ghana kafin ta). Babu cikakken bayani akan mutuwarsa, a ranar 6 ga watan Nuwamba, shekara ta alif 1492. A cewar Tarikh al-Sudan, Ali ya nutse ne a ruwa a yayin da yake ketara kogin Neja.[4] Al’adar baka sun nuna cewa dan ‘yar uwarsa, Askia Muhammad Ture ne ya kashe shi.[4][5] Sai dansa Sunni Baru ya gaje shi, wanda Askia ta kalubalancei shi saboda ba a ganin Baru a matsayin cikakken musulmi ba. Askiya ta ci sarautar. A cewar Tarikh al-Sudan an yi imanin cewa wannan al'amari ya sa 'ya'yan Sonni Ali mata suka yi ihu "A si kiya!" Karin magana na zamani zai kasance "A si tiya" ko (ba zai yiwu ba), a yayin da aka kawo musu labarin juyin mulkin.[6]

Sunni Ali ya yi mulke musulmai na birni da kuma wadanda ba musulmi na kauya a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen zamantakewar tsakanin addinai daban-daban. Riko da yayi ga tsubun mutanen Afirka yayin da kuma yake ikirarin Musulunci ya sa wasu marubuta su siffanta shi a matsayin musulmi a zahiri ko kuma a fake.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Walker, Robin (1999). The West African empire of Songhai in 10 easy lessons : introduction to black history. Siaf Millar. Birmingham: Concept Learning Ltd. ISBN 1-903181-00-3. OCLC 47678165.
  2. Adeleke, Tunde (1996). Songhay (1st ed.). New York: Rosen Pub. Group. ISBN 0-8239-1986-2. OCLC 31936544.
  3. "Chapter 2: The Origin of the Sonni" (PDF). siiasi.org. Sankore Institute of Islamic African Studies International. Retrieved 14 October 2015.
  4. 4.0 4.1 4.2 Saʻdī, ʻAbd al-Raḥmān ibn ʻAbd Allāh,? (1999). Timbuktu and the Songhay Empire : Al-Saʻdi's Taʼrīkh al-Sūdān down to 1613, and other contemporary documents. John O. Hunwick. Leiden: Brill. ISBN 90-04-11207-3. OCLC 40602667.
  5. Lipschutz, Mark R. (1986). Dictionary of African historical biography. R. Kent Rasmussen (2nd ed., expanded and updated ed.). Berkeley: University of California Press. ISBN 0-520-05179-3. OCLC 14069361.
  6. "African Legends". Africanlegends.info. Retrieved 2015-10-14.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}