Sonni Gwanle Tyoden
Sonni Gwanle Tyoden | |||||
---|---|---|---|---|---|
2015 - 29 Mayu 2023 ← Ignatius Datong Longjan (en) - Josephine Piyo →
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Jahar pilato, 22 Satumba 1950 (74 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
University of Lancaster (en) Jami'ar Ibadan | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Sonni Gwanle Tyoden (an haifeshi a ranar ashirin da biyu 22 ga watan Satumba, shekara ta 1950). Farfesa ne a Najeriya, Sonni Farfesa ne a fannin Kimiyyar Siyasa, Mai Gudanar da Ilimi, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Jos (University of Jos).[1][2]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Tyoden a ranar 22 ga Satumba, 1950. Ya halarci makarantar Sakandire ta Boys a jihar Filato, Arewacin Najeriya, inda ya sami takardar shaidar makarantar sakandaren Afirka ta Yamma. Daga baya ya wuce zuwa Jami'ar Ibadan inda ya sami Digiri na farko na Kimiyya (B.Sc) a Kimiyyar Siyasa.[3] Ya sami digiri na biyu a fannin kimiya (M.Sc) da kuma digirin digirgir (Ph.D) a kan alakar kasa da kasa da tattalin arzikin siyasa daga jami'ar Lancaster da ke kasar Ingila.[4][5][6]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Tyoden ya fara aikinsa a shekarar 1978, a matsayin Mataimakin Sakatare a Ma’aikatar Kafa Gwamnatin Filato. Daga baya ya zama memba na ma’aikatan ilimi a Jami'ar Jos, inda ya zama cikakken Farfesa a 1990.[7] Bayan Tyoden ya zama Farfesa a 1990, sai aka nada shi, Shugaban Sashen Kimiyyar Siyasa, Jami’ar Abuja[8] Ya koma wurin nasa alma mater, Jami'ar Jos a 2000, kuma ya zama Dean na Faculty of Social Sciences a 2001, mukamin da ya rike har zuwa 2005.[9] An nada shi Mataimakin Shugaban Jami'ar Jos a ranar 12 ga Yulin 2006, matsayin da ya rike har zuwa Yuni 11, 2011. Ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban Jami'ar.[10][11] An zabe shi a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Filato a 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.[12][13][14]
Kyaututtuka
[gyara sashe | gyara masomin]- Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), reshen jami’ar Jos ta bayar da takardar shaidar karramawa.
- Kyautar Distinguished Academic Leadership award da Rotary Club Naraguta, Jos, Plateau state.
- Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa ta Najeriya a 2013
- Cibiyar Ilimin zamantakewa ta Najeriya a watan Disamba 2014.[15]
Wallafe-Wallafe
[gyara sashe | gyara masomin]- Inter and intra-party relations: towards a more stable party system in Nigeria.[16]
- The Kaduna Mafia. Jos: Jos University Press. TakuyaThe Kaduna Mafia1987.
- The middle belt in Nigerian politics. AHA.
- Of Citizens and Citizens: The Dilemma of Citizenship in Nigeria.[17]
- Tyoden, S. G. (1994). The Place of the Middle Belt in Nigeria's Power Equation. In Commission paper for the National Conference on" The Equity Question in Nigeria", Centre for Development Studies, University of Jos, 6–7 May.
- The Kaduna Mafia. Jos University Press.
- Nigeria: Youth agenda for the 21st century. Sibon Books.
- The Domestic Socio-Political Situation This includes, the nature of the political system, and the nature and conduct of the politics and government In other words, in a political system where the political. Towards the Survival of the Third Republic, 203.
- Vice Chancellor's Speech: Presented at the 24th Convocation Ceremony of the University of Jos.
- Towards a Progressive Nigeria. Triumph Publishing Company.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Mohan, Giles; Zack-Williams, Tunde (2004). The Politics of Transition in Africa. James Currey. ISBN 9780852558225.
- ↑ "Jang Wants Teachers to Call off Strike, Articles - THISDAY LIVE". Archived from the original on 25 October 2014.
- ↑ Dokubo, Charles Quarker; Bassey, Celestine Oyom (20 January 2011). Defence Policy of Nigeria. AuthorHouse. ISBN 9781456731557.
- ↑ "Sonni Gwanle Tyoden". Nnu.ng - Nigeria News Update. (in Turanci). Retrieved 24 May 2020.[permanent dead link]
- ↑ "NIPSS :: Political Parties Leadership and Policy Development Centre (PPLPDC)". pplpdc.nipsskuru.gov.ng. Archived from the original on 15 February 2020. Retrieved 2 May 2020.
- ↑ "Sonni Gwanle Tyoden".[permanent dead link]
- ↑ Our Correspondent. "New Telegraph – Don seeks blueprint on govt policies". Archived from the original on 25 October 2014.
- ↑ Lagos, Ikenna Emewu in (3 October 2001). "Nigeria: Oputa Rules On Appearance, Group Demands Apology Over June 12". This Day (Lagos). Retrieved 22 December 2017.
- ↑ "National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru, Nigeria".
- ↑ "UNIJOS VC, others hail Tyoden on varsity ranking as 2nd best". Vanguard News. 27 June 2011.
- ↑ "The Battle For UNIJOS Vice Chancellorship".
- ↑ Bako, Friday (12 March 2020). "Plateau Deputy Governor, Prof. Sonni Tyoden Lauds Berom's Educational Agenda, Says it is result-oriented". View Point Nigeria (in Turanci). Retrieved 29 April 2020.
- ↑ Adama, Dickson S.; Jos (12 December 2019). "Plateau deputy gov advises Nigerians on democracy". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 29 April 2020.
- ↑ Agencies (27 September 2019). "Plateau not ripe for state police – deputy governor". TODAY (in Turanci). Retrieved 29 April 2020.
- ↑ Plateau State Government Website. "Professor Sonni Gwanle Tyoden". Laravel (in Turanci). Retrieved 30 May 2020.
- ↑ Tyoden, S. G. (2002). "Inter and intra-party relations: towards a more stable party system in Nigeria" (PDF). The Constitution. 3 (1): 1–23.
- ↑ Tyoden, S.G. (2006). "Of Citizens and Citizens: The Dilemma of Citizenship in Nigeria" (PDF). Inaugural Lecture, Delivered at the University of Jos.