Stephen Akiga
Stephen Akiga | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
Mayu 2002 - Mayu 2003 ← Ishaya Mark Aku - Musa Mohammed (Dan Siyasa) →
9 ga Faburairu, 2001 - Mayu 2003 ← David Jemibewon (en) - Broderick Bozimo →
2000 - 30 ga Janairu, 2001 ← Iyorchia Ayu - Magaji Muhammed → | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 1942 | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Mutuwa | 6 Satumba 2004 | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Stephen Akiga | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Suna | Stephen (mul) |
Shekarun haihuwa | 1942 |
Lokacin mutuwa | 6 Satumba 2004 |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | Minister of Industry, Trade and Investment (en) , Minister of Police Affairs (en) da Minister of Sports (en) |
Ɗan bangaren siyasa | Peoples Democratic Party |
Stephen Ibn Akiga (ko Steve Akiga ) (ya rasu a ranar 6 ga watan Satumban 2004) ya kasance ministan masana'antu na Najeriya, sannan ministan harkokin ƴan sanda sannan kuma a ƙarshe ministan wasanni a majalisar ministoci ta farko ta shugaba Olusegun Obasanjo.
Obasanjo ya kori majalisar ministocinsa a ranar 30 ga watan Janairun 2001. A ranar 9 ga watan Fabrairu Stephen Akiga ya koma Ma'aikatar Masana'antu zuwa Harkokin ƴan sanda.[1] A cikin watan Mayun 2001 Akiga ya ce nan ba da daɗewa ba ƴan sanda za su iya kawar da amfani da ƙananan bindigogi a ƙoƙarin da suke na dakatar da harsasai na bazata.[2]
A cikin watan Mayun 2002 aka naɗa Akiga Ministan Wasanni don maye gurbin Ishaya Mark Aku, wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama.[3] A cikin watan Agustan 2002 Akiga ya yarda cewa Najeriya na da matsala wajen shirya gasar wasannin Afirka na shekarar 2003, amma ya ce an shirya yunƙurin karɓar baƙuncin gasar Olympics ta shekarar 2012.[4] A cikin watan Janairun 2003 Akiga ya sanar da cewa Najeriya ta kafa kwamitin da zai shirya fafutukar neman shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010.[5] A cikin watan Mayun 2003, lokacin da aka samu jinkiri kafin Obasanjo ya naɗa sabuwar majalisarsa bayan zaɓen, an samu rahotannin cewa ma’aikatan ma’aikatar wasanni sun fara azumi da addu’a don ganin Allah bai mayar musu da Akiga ba.[6]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Akiga ya mutu a ranar 6 ga watan Satumban 2004.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://allafrica.com/stories/200102090284.html
- ↑ http://news.bbc.co.uk/2/hi/africa/1322017.stm
- ↑ http://www.accessmylibrary.com/coms2/summary_0286-25589135_ITM
- ↑ http://news.bbc.co.uk/sport2/hi/other_sports/2205083.stm
- ↑ http://news.bbc.co.uk/sport2/hi/football/africa/2649003.stm
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2017-12-05. Retrieved 2023-04-06.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-01-05. Retrieved 2023-04-06.