Jump to content

Suleiman Hussein Adamu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Suleiman Hussein Adamu
Minister of Water Resources (en) Fassara

21 ga Augusta, 2019 - 2023
Minister of Water Resources (en) Fassara

Nuwamba, 2015 - 2019
Muktar Shagari
Rayuwa
Haihuwa 19 ga Afirilu, 1963 (61 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da civil servant (en) Fassara

Suleiman Adamu Injiniya ne na Najeriya kuma Ministan Ma'aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayyar Najeriya.[1] Ya ƙaddamar da aikin samar da ruwan sha na yankin Ogbia a Otuoke na jihar Bayelsa.[2] Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi Ministan Albarkatun Ruwa.[3][4][5]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Suleiman a garin Kaduna a shekarar 1963 kuma ya kammala karatunsa a jami'ar Ahmadu Bello Zariya, Kaduna kafin ya wuce jami'ar karatu ta ƙasar Ingila.[6]

Kyauta da karramawa

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2020, Suleiman Hussein Adamu ya sami lambar yabo ta duniya ta shekarar 2020 don ƙwaƙƙwaran gudummawa ga WaterAid daga Mai martaba, Yarima Charles, Yariman Wales.[7]