Surame
Surame | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Kebbi | |||
Labarin ƙasa | ||||
Bangare na | Jahar Nasarawa Sokoto |
Tsohon birnin Surame wani abin tarihi ne na al'ummar Najeriya dake cikin jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya. Muhammadu Kanta Sarkin Kebbi ne ya ƙirƙiro tsohon birnin a ƙarni na 16, wanda ya mallaki daula a yankin. An bar garin a kusan a shekarar 1700 lokacin da babban birnin, birnin garin ya koma Birnin Kebbi.[1]
Bayani
[gyara sashe | gyara masomin]Birnin na ya mamaye yanki kimanin kilomita 9 km, wurin ya ƙunshi harsashin ginin matsugunan mutane, ganuwa, rijiyoyi da tukwane.[2] Akwai katangar tsaro da aka gina daga dutse a kusa da ƙauyuka, da kuma ramuka da aka haƙa a kusa da babban yanki kuma an cika su da ciyayi masu ƙaya a matsayin wata hanyar kariya ko tsaro.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Tsohuwar Masarautar Suram tana da iko daga ƙarni na 15 zuwa na 16.[2]
Kayan tarihi na Nijeriya
[gyara sashe | gyara masomin]An ayyana Surame a matsayin daɗaɗen abin tarihi na ƙasa a ranar 15 ga watan Agustan shekarar 1964.[1]
Matsayin Al'adun Duniya
[gyara sashe | gyara masomin]Birnin an saka sunansa cikin jerin abubuwan tarihi na UNESCO a ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2007 a ɓangaren rukunin kayan tarihi na (Mixed Cultural + Natural)--->( Al'adun da aka cakuɗe wuri ɗaya da na asali).[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "NATIONAL COMMISSION FOR MUSEUMS AND MONUMENTS". NATIONAL COMMISSION FOR MUSEUMS AND MONUMENTS. Archived from the original on 25 February 2012. Retrieved 29 April 2012.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Surame Cultural Landscape - UNESCO World Heritage Centre