Talo-talo
Talo-talo | |
---|---|
Scientific classification | |
Class | Aves |
Order | Galliformes (en) |
Dangi | Phasianidae (en) |
Subfamily | Meleagridinae (en) |
genus (en) | Meleagris Linnaeus, 1758
|
General information | |
Tsatso | turkey meat (en) |
Talo-talo | |
---|---|
Scientific classification | |
Class | Aves |
Order | Galliformes (en) |
Dangi | Phasianidae (en) |
Subfamily | Meleagridinae (en) |
genus (en) | Meleagris Linnaeus, 1758
|
General information | |
Tsatso | turkey meat (en) |
Talo-talo tsuntsu ne daga cikin nau'in tsuntsayen gida haka za'a iya cewa talotalo dabba ne daga dabbobin gida. Sai dai shi talo-talo yana da dan girma sosai sama da sauran wasu tsuntsayen girma. [1][2][3][4][5]. Masana sunyi bayani akan akwai nau'in talo-talo biyu da na gida da na daji, sai dai an bayyana cewa na gida yafi na daji girma. A turance ana kiran talo-talon gida da (Ocellated turkey) sai na daji kuma ana kiransa da (Wild turkey).
Sifan Talotalo
[gyara sashe | gyara masomin]Talotalo tsuntsu ne mai girma da kuma yana baza gashin shi tunba maza ba haka mazan talotalo sunfi matan girma. Anan ake banbance tsakanin maza da kuma matan talotalo, sai kuma maza suna fitar da wani abu da ake kira kora duk da mata ma suna fitar wa amma ta mazan tafi don ta mazan kusan tana lulluɓe kan namijin talotalo da kuma ƙasan wuyanshi wani fata-fata yana fitowa kamar dai ace gemu ne irin na mazan talotalo. Haka kuma gashin talotalo namiji yafi tsawo don wani lokaci yakan bazashi a yayin faɗa ko yin adon kalan nasu, na dabbobi. Matan talotalo basuda kalolin gashi daban-daban saɓanin mazan. Mazan talotalo suna faɗa da junansu musamman idan akwai mata a tare dasu har yakai ga wani ya kashe wani. Ana kiran talotalo da turanci da (turkey). Wasu daga cikin Hausawa musamman matasa basu ainahin sunan namijin talotalo ba, to sunan namijin talotalo shine, (Toron Talotalo).
Asalin yadda aka sama Talotalo suna da turanci
[gyara sashe | gyara masomin]Wani manazarci mai suna Mario pei, Yana ganin talotalo ya sami sunan shi da turanci ne tun farkon da aka fara shiga da talotalo cikin ƙasashen Turai ana kasuwancin sa daga ƙasar Turkiyya zuwa ƙasashen Turai ɗin to kuma ita ƙasar sunanta da turanci shine (Turkey), daga Haka kawai sai suka cigaba da kiransa da turkey shikenan har zuwa yanzu.
Alfanu da fa'idar kiwon talotalo
[gyara sashe | gyara masomin]Kiwon talotalo yanada sauƙin gaske don kusan komai ci yake, haka idan ya girma musamman mazan talotalo yana gadin gida, don har cizo (sara) yakeyi. Haka wani bincike ya nuna cewa cin naman talotalo yana sanya isasshen bacci.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ko kun san cin naman talo-talo na sa isasshen bacci?". BBC Hausa. 14 May 2017. Retrieved 1 August 2021.
- ↑ Musa, Aisha (30 October 2019). "Tirkashi: An tsare wani Fasto kan satar talotalo da akuya". legit hausa. Retrieved 1 August 2021.
- ↑ Olusegun, Mustapha (22 November 2013). "Kwastam Sun Kama Shinkafa Da Daskararrun Naman Kaji Da Talo-Talo A Legas". Aminiya.dailytrust. Retrieved 1 August 2021.
- ↑ "Menene Sunan Macen Talo Talo Da Hausa..? Gamu A Titi Episode 1 AMDT TV HAUSA". AMB TV. 30 August 2019. Retrieved 1 August 2021.
- ↑ Garba, Isyaku (7 February 2018). "Fassara wasu sunayen tsuntsaye da dabbobi daga turanci zuwa Hausa". isyaku.com. Archived from the original on 1 August 2021. Retrieved 1 August 2021.