Tamina
Tamina | |
---|---|
dessert (en) | |
Kayan haɗi | semolina (en) , man shanu da zuma |
Tarihi | |
Asali | Aljeriya |
Tamina (Arabic) ko "semolina cake," tsohuwar zuma ce ta Aljeriya wacce ta kunshi semolina mai laushi, mai launin zinariya amma ba launin ruwan ƙasa ba, haɗe da man shanu, da zuma mai narkewa. Yawanci ana yi mata ado da cinnamon, Pistachio ko almonds mai sukari.[1]
Ana kuma kiransa Tamena, Taqnata ko Takneta wani irin kek ne mai daɗi, wanda aka saba yi a Aljeriya da Maroko a lokacin haihuwa ko kuma Maulidi Ennabawi echarif (biki na addini na tunawa da maulidin Annabin Musulunci Muhammad (A)) ko kuma ana yin sa a lokacin bukukuwa haihuwar yaro amma ana iya shirya shi kowace rana na shekara. [2]
Akwai wani irin kek na Aljeriya mai suna tamina (Rfiss Tousni), amma ana yin wannan da gasasshen semolina, da man shanu da man dabino (garss). [2] Yana da zaƙi mai daɗi don raka tare da kyakkyawan shayi na Mint na Aljeriya ko latte a lokacin ciye-ciye. Ana yi wa Tamina ado da ƙwayayen Pine don ƙarin daɗi. [3]
Yawanci ana raba Tamina tsakanin wasu ’yan tsiraru, kamar yadda ake haɗawa a ƙananan faranti ana sha da ƙananan cokali.
Sinadaran
[gyara sashe | gyara masomin]- 500 grams na semolina (matsakaici-niƙa)
- 250 g man shanu mai narkewa
- 250 g zuma
- 1 tsp ruwan furanni lemo (mazhar)
- Cinnamon na ƙasa (don ado)
- Dragées, Pistachio ko almonds (don ado na ƙarshe)
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.tasteatlas.com/tamina
- ↑ 2.0 2.1 "Tamina: Algerian Semolina Honey Dessert - African Food Network". African Food Network (in Turanci). 2022-06-16. Retrieved 2024-09-07. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ Safia, Um. "Tamina - Algerian Toasted Semolina & Honey Sweet Recipe - Dessert.Food.com". www.food.com (in Turanci). Retrieved 2024-09-07.