Jump to content

Tattaunawar user:Hauwau sulaiman

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Barka da zuwa![gyara masomin]

Ni Robot ne ba mutum ba.

Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, Hauwau sulaiman! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma muna fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial. Na gode. AmmarBot (talk) 21:29, 27 Mayu 2023 (UTC)[Mai da]

Yawwa sannu Hauwau sulaiman (talk) 19:39, 12 ga Yuli, 2023 (UTC)[Mai da]

Hauwau sulaiman (talk) 21:26, 14 ga Yuli, 2023 (UTC) nagode me robot[Mai da]

Barka da aiki @Hauwau sulaiman, naga kokarin ki wajen kirkiran maƙaloli da yadda kike samar da references a dukkanin makalar da kika kirkira. Akwai wasu abubuwa da ya kamata ki yi la'akari da su a nan gaba.

  • Kafin ƙirƙirar makala ki shiga akwatin bincike (searching) domin ki tabbata babu irin makalar domin kaucewa maimaita makalar da aka riga aka yi ta.
  • Sannan ki rinka bawa makala suna mafi inganci, misali a makalar da kika kirkira ta Alhaji musa dan kwairo kamala yayi ta zama kar haka Alhaji Musa Dankwairo', kuskure na biyu kuma shine akwai ta a Hausa Wikipedia Musa Dankwairo, a nan dole sai an goge wadda kika yi. Sannan makalar da kika yi ta Hadiza kabara kamata yayi ta zama kamar haka Hadiza Kabara. Wata farkon ko wanne suna ya fara da babban baki tunda dai sunan makalar ne.

Da Wannan nake so na sanar dake cewa a matsayi na na Admin a Hausa Wikipedia na yaba da kokarin ki kuma kina kirkirar maƙaloli masu Inganci. Allah ya bada Sa'a. Gwanki(Yi Min Magana) 17:10, 18 ga Yuli, 2023 (UTC)[Mai da]

Hauwau sulaiman (talk) 21:02, 18 ga Yuli, 2023 (UTC) na fahimci kukurena yallabai nagode inshallah zan gyara , inda nai kukure a cigaba da tunatar dani[Mai da]

Cancanta[gyara masomin]

Barka @Hauwau sulaiman. Na ga kina yawan ƙirƙirar makaloli game da yan masana'antar fim ta Hausa, hakan ya na da kyau. Sai dai kallon fuskokinsu a fina-finai barkatai ba zai taɓa zame mana hujjar cewa dukkan su sun cancanci a rubuta makala game da su ba. Akwai ka'idoji da sharuddai da ke zama ginshikin na assasa dukkan wata makala a wanna wuri. Don haka dukkan wata makala da ki ke fatan ƙirƙira anan ya zamana ta Cancanta!.

Domin karin bayani ki duba sakon Barka da Zuwa akwai bayani dalla-dalla game da yanda ake ke ƙirƙiro makala mai inganci ko wadda ta Cancanta. Idan kina buƙatar tambaya kina iya tambaya ta, ta nan ko wani editan ko a Group da aka buɗe a dandalin WhatsApp. Nagode. BnHamid (talk) 14:58, 31 ga Maris, 2024 (UTC)[Mai da]

Nagode kwarai da gaske insha Allah zan gyara . Kafin nayi wata mukala sena duba komai bayani gameda cancantar mukalar kafin na rubuta. Nagode insha Allah zan ƙara neman sani agurin yan uwa dangane da mukalar. Hauwau sulaiman (talk) 18:44, 15 ga Afirilu, 2024 (UTC)[Mai da]

Tunatarwa don jefa kuri'a yanzu don zaɓar membobin U4C na farko[gyara masomin]

Kuna iya samun wannan sakon da aka fassara zuwa ƙarin harsuna akan Meta-wiki. Kuyi ƙoƙarin fassara wannan saƙo zuwa Hausa

Ya ku 'yan Wikimedia,

Kuna karɓar wannan saƙo saboda a baya kun shiga cikin tsarin UCoC.

Wannan tunatarwa ce cewa lokacin jefa ƙuri'a na Kwamitin Daidaitawa da Gamayyar Tsarin Gudanarwa (U4C) yana ƙare ranar 9 ga Mayu, 2024. Karanta bayanin akan Shafin jefa ƙuri'a akan Meta-wiki don ƙarin koyo game da zaɓe da cancantar masu jefa ƙuri'a.

Kwamitin Daidaitawa da Gamayyar Tsarin Gudanarwa (U4C) ƙungiya ce ta duniya da aka keɓe don samar da daidaito da daidaiton aiwatar da UCoC. An gayyaci membobin al'umma don gabatar da aikace-aikacen su na U4C. Don ƙarin bayani da alhakin U4C, da fatan sake duba Tsarin Dokan ta U4C.

Da fatan za a raba wannan sakon tare da membobin al'ummar ku don su ma su shiga ciki.

A madadin Kungiyar Ayyukan UCoC,

RamzyM (WMF) 23:11, 2 Mayu 2024 (UTC)[Mai da]