Jump to content

Thomas Sankara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Thomas Sankara
Murya
5. Shugaban ƙasar Burkina Faso

4 ga Augusta, 1983 - 15 Oktoba 1987
Saye Zerbo (mul) Fassara - Blaise Compaoré
5. Prime Minister of Burkina Faso (en) Fassara

10 ga Janairu, 1983 - 17 Mayu 1983
Saye Zerbo (mul) Fassara - Youssouf Ouédraogo (mul) Fassara
Rayuwa
Cikakken suna Thomas Isidore Noël Sankara
Haihuwa Yako (en) Fassara, 21 Disamba 1949
ƙasa Republic of Upper Volta (en) Fassara
Burkina Faso
Mutuwa Ouagadougou, 15 Oktoba 1987
Makwanci Ouagadougou
Yanayin mutuwa  (gunshot wound (en) Fassara)
Ƴan uwa
Mahaifi Mutanen Fulani
Mahaifiya Mossi
Abokiyar zama Mariam Sankara (en) Fassara  1987)
Ahali Odile Sankara
Karatu
Makaranta Prytanée militaire de Kadiogo (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, hafsa, statesperson (en) Fassara, Soja da minista
Muhimman ayyuka Une Seule Nuit (en) Fassara
Kyaututtuka
Kayan kida Jita
Aikin soja
Fannin soja Army of Burkina Faso (en) Fassara
Digiri captain (en) Fassara
Ya faɗaci Agacher Strip War (en) Fassara
Imani
Addini Katolika
IMDb nm5174887
thomassankara.net
Shugaban juyin mulki ƙasar Burkina faso thomas sankara

Thomas Isidore Noël Sankara An haifi Thomas Isidore Noel Sankara a ranar (22 )ga watan Disamban shekarar (1949) zuwa (15 ) ga watan Oktoba, (1987). Shine shugaban juyin-juya hali na ƙasar Burkina Faso, daga shekarar (1983) zuwa (1987). Babban ɗan kishin Afrika ne, sannan kuma masoyansa na kallon sa a matsayin wata alama ta juyin-juya-hali.

A lokacin da yake da shekaru 33, Sankara ya zama Shugaban Jamhuriyar Upper Volta kuma ya kaddamar da jerin gyare-gyare na zamantakewa,muhalli, da tattalin arziki da ba a taba ganin irinsu ba wanda ya kasance wani bangare na abin da ya kira juyin juya halin dimokuradiyyar jama'a. A shekarar 1984, Sankara ya jagoranci sauya sunan ƙasar zuwa Burkina Faso ('ƙasar mutanen kirki'),kuma ya rubuta taken ƙasa da kansa [1] [2] Manufofinsa na waje sun ta'allaka ne akan adawa da mulkin mallaka kuma ya ƙi karɓar rance da jari daga ƙungiyoyi irin su Asusun Ba da Lamuni na Duniya.Duk da haka, ya karɓi wasu tallafin ƙasashen waje a ƙoƙarin sa inganta tattalin arzikin cikin gida, bambanta hanyoyin taimako da kuma sanya Burkina Faso ta dogara da kanta.[3] Manufar cikin gida ta haɗa da hana yunwa, faɗaɗa aikin gona,gyaran ƙasa, da dakatar da harajin zaɓen karkara, Shirye-shiryen kiwon lafiya na Sankara sun rarraba miliyoyin allurai na rigakafi ga yara a fadin Burkina Faso.[4] Gwamnatinsa kuma ta mai da hankali kan gina makarantu,cibiyoyin kiwon lafiya,wuraren ajiye ruwa, da ayyukan gina ababen more rayuwa.[5] [6] Ya yi yaƙi da hamadar Sahel ta hanyar dasa fiye da miliyan 10 na bishiyoyi. A zamantakewa, gwamnatinsa ta tilasta haramta kaciya ga mata,auren dole da kuma auren mata fiye da daya.[7]

Sankara ya karfafa hoton sa na jama'a inda ya bayar da umarnin sayar da manyan motoci da kadarori na gwamnati domin rage tsadar kayayyaki.Bugu da kari, ya haramta abin da ya yi la'akari da kayan alatu na kwandishan a ofisoshin gwamnati.da gidajen ƴan siyasa[8] Ya kafa kwamitoci masu kwazo don Kare juyin juya hali don yin aiki a matsayin sabon tushe na al'umma. Sakon gwamnati An nada Sankara ministan yada labarai a gwamnatin soja ta Saye Zerbo a watan Satumbar 1981. Sankara ya banbanta kansa da sauran jami’an gwamnati ta hanyoyi da dama kamar hawan keke zuwa aiki yau da kullum,maimakon tukin mota. Yayin da magabatansa za su yi ta cece-kuce ga 'yan jarida da jaridu.

Sankara ya karfafa aikin jarida na bincike kuma ya ba wa kafafen yada labarai damar buga duk abin da suka samu Wannan ya sa jaridu na masu zaman kansu da na gwamnati suka buga badakalar gwamnati[ Ya yi murabus a ranar 12 ga Afrilu 1982 don adawa da abin da yake gani a matsayin gwamnati na yaki da ƙwadago, yana mai shelanta 'Bala'i ga waɗanda ke damfarar jama'a!' (Malheur à ceux qui bâillonnent le peuple!)

A ranar 15 ga Oktoba 1987, an kashe Sankara ta hanyar sojoji da Blaise Compaoré ya jagoranta, wanda ya karɓi jagorancin kasar ba da daɗewa ba. Compaoré ya riƙe mulki har zuwa tashin hankali na Burkina Faso a shekarar 2014. A shekarar 2021, an tuhume shi a gaban kotun soja da laifin kisan Sankara kuma an same shi da laifi.[9]

da kuma yaƙin neman zaɓe na ƙasa da ƙasa da shirin rigakafin cututtuka don rage meningitis, zazzabin cizon sauro da sankarau Bayan horon aikin soji a makarantar Sakandire a shekarar (1966), Sankara ya fara aikin soja yana ɗan shekara 19. Bayan shekara ɗaya an tura shi zuwa Madagascar don horon hafsin soja Antsirabe. Sankara ya karfafa hoton sa na jama'a inda ya bayar da umarnin sayar da manyan motoci da kadarori na gwamnati domin rage tsadar kayayyaki.

Aikin Gwamnati

[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa Sankara a matsayin ministan bayanai a lokacin mulkin soji a gwamnatin Saye Zerbo a watan Satumba (1981).[25] Sankara ya bambanta kan shi da sauran mutanen gwamnati, ta hanyar tuƙa kanshi a keke kullum maimakon tuka mota.Magabatar shi suna dakile ƴan jarida da jaridu,amma Sankara yana kwadaitar da su,Sankara yana karfafa aikin jarida na bincike ya baiwa kafafen yada labarai damar buga duk abin da suka samu.

[10][11][12][13]