Ummu Ayman
Ummu Ayman | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | unknown value |
Mutuwa | unknown value |
Makwanci | Al-Baqi' |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
Ubayd ibn Zayd (en) Zayd ibn Harithah |
Yara | |
Sana'a | |
Aikin soja | |
Ya faɗaci |
Yaƙin Uhudu Yaƙin Khaybar yaƙin Hunayn |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Barakah bint Tha'alaba larabci بَـرَكَـة}, amfi saninta da Umm Ayman, ta kasance daya daga cikin wadanda suka karba musulunci da wuri. ta kasance yar asalin Habasha ce kuma baiwa ce ga iyayen Annabi Muhammad S.A.W, wato Abdullahi dan Abdul-Muttalib da kuma Amina yar Wahb. mijinta shine Ubayd dan Zayd na Banu Khazraj, wanda ta haifa mai Ayman dan Ubayd, sai ake kiranta da Umm Ayman
Bayan rasuwar Aminah, Baraka ta taimaka wajen renon Muhammad S.A.W. a gidan kakansa, Abd Al-Muttalib bn Hashim. Muhammad S.A.W ya kasance yana ganinta a matsayin uwa. Daga baya Muhammadu S.A.W ya 'yantar da ita daga bauta, amma ta ci gaba da yi ma sa hidima da iyalansa. Ta musulunta da wuri, kuma ta kasance a muhimman yakokin Uhudu da Khaibar.
Bayan samun 'yancinta, Muhammadu S.A.W ya shirya aurenta, na farko da Ubayd ibn Zayd na Banu Khazraj, auren da ta haifi ɗa, Ayman bn Ubayd, wanda ta dalilin shine aka yi mata alkunya da Umm Ayman (ma'ana mahaifiyar Ayman). Daga bayan Mutuwar Ubayd ibn Zayd, an aurar da ita ga dan riqon Muhammad S.A.W, Zayd bn Harithah. Inda ta haifi Danta tare da Zaidu, Usama bn Zaid, wanda ya yi aiki a matsayin kwamanda a sojojin Musulmi na farko, kuma ya jagoranci Yaki tare da Usama bin Zaid zuwa cikin Daular Rumawa.[1]
Fage
[gyara sashe | gyara masomin]Baraka diya ce ga Tha’laba bin Amr, Bahabashe[1]. Ta yi hidima a gidan Abdullahi bn Abdil-Muddalib da Amina bint Wahb. Ta kula da Muhammad S.A.W, bayan rasuwar Amina[2].
Yarintar Muhammadu
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan rasuwar Aminah a Al-Abwa, Baraka ta kula da Muhammad S.A.W, kuma ta koma tare da shi zuwa gidan kakansa a Makka, inda ta yi masa hidima a lokacin yarinta [3] da kuma bayansa,[4] a lokacin girmansa[5]
Ibn Kathir ya ce, Abdullahi bn Abd al-Muttalib kakan Muhammad, ya ce wa Baraka kada ta yi sakaci da jikansa, musamman kamar yadda da yawa daga cikin Ahlul Kiṫâb (Larabci: أَهـل الـكِـتـاب, Ahlul Kitabi) suka yi hasashen zai kasance. Annabin al’umma[6].
Aure da yara
[gyara sashe | gyara masomin]Lokacin da Muhammadu S.A.W ya auri Khadija, ya 'yanta Baraka, kuma ya bada auren ta, ga wani sahabi Khazraj mai suna Ubayd ibn Zaid. Ta hanyar wannan auren, Baraka ta haifi ɗa mai suna Ayman, don haka ake kiranta da "Umm Ayman" ("mahaifiyar Ayman").[7]. Daga baya kuma an kashe Ayman bn Ubayd a yakin Hunaini [8].
Dan renon Muhammad Zaid ibn Harithah daga baya ya auri Baraka. Suna da ɗa mai suna Usama wanda Muhammadu S.A.W ya naɗa a matsayin shugaban runduna kuma ya jagoranci nasarar yaƙi da Usama bin Zaid zuwa daular Rumawa[9].
Hijira
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan Muhammadu S.A.W ya sanar da Annabcinsa, Ummu Ayman ta zama ɗaya daga cikin mabiyansa na farko. Daga baya sai ta yi hijira zuwa Madina. Ummu Ayman ta halarci yakin Uhudu. A inda ta debo wa sojoji ruwa tare da taimaka wa wadanda suka jikkata. Ta kuma raka Muhammad S.A.W a yakin Khaibar[10].
A yakin Uhud, mutane da yawa sun gudu zuwa Madina bayan jita-jitar mutuwar Muhammadu S.A.W. Ummu Ayman ta yayyafa wa wasu 'yan gudun hijira ƙura, ta ba su igiya, ta ce musu: "Ku ba ni takobinku da sandal ɗinku." Sannan ta nufi fagen fama tare da mata da dama[11]. Daga nan sai ta ji rauni da kibiya wadda Hebban binu Araqa, wani sojan makiya ya harba mata[12].
Dangantaka da sauran musulmin farko
[gyara sashe | gyara masomin]Muhammad S.A.W ya kasance yana son Ummu Ayman, har yana tunaninta kamar uwa.[13] Hadisai da dama sun bayyana irin girmamawar da Muhammad S.A.W yake mata.[14] Ya ziyarci Ummu Ayman a gidanta, bayansa kuma halifofi Abubakar da Umar sun yi haka[15]. A wasu madogaran hadisi akwai sama game da falalar Ummu Ayman[16]. Haka nan an yabe ta a majiyoyin Shi’ah[17].
An ruwaito hadisi kadan daga gare ta[18]. Kamar su Anas bn Malik da Abu Yazid Madani da Hanash bn Abdullah San’any sun ruwaito daga gare ta[19].
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ba a bayyana ainihin ranar da Ummu Ayman ta rasu ba. Wasu sun ce ta mutu kimanin watanni biyar bayan rasuwar Muhammad S.A.W [20]. Amma a cewar ibn Sa’ad,[21] tana raye a farkon halifancin Uthman[22].
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Zuhri, p 177; al-Tabarani, vol. 25, p. 86
- ↑ Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223; Baladhuri, Vol. 1, p. 96
- ↑ Ibn Qutaybah, p. 150
- ↑ Baladhuri, vol.1, p.472
- ↑ Ibn Hajar, al-Ithaba, vol.8, p. 380
- ↑ ibn Kathir, al-Bidayah wa al-Nihayah, vol. 2, p. 343
- ↑ Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223; Ibn Sa`d, vol. 4, p. 61
- ↑ mahallati, vol.2, p. 26
- ↑ Baladhuri, vol.1, p.96
- ↑ Al-Waqidi, Vol. 1, p. 241, 250, vol.2, p. 685; Ibn Sa`d, vol. 8, p. 225; Baladhuri, vol. 1, p.
- ↑ Bahr al-Ulum, MuhammadAli, translate by Muhammad Ali Amini,(1979), Woman of early Islam, Hekmat
- ↑ Ibn Athir, Ali (2009). al-Kamil fi al-Tarikh. vol. 2. Beirut: Dar Ihya al-Turath al-Arabi. p. 160.
- ↑ Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223
- ↑ Ibn Sa`d, vol. 8, p. 223-226; Al-Dhahabi, vol. 2, p. 224
- ↑ Muslim ibn al-Hajjaj, vol. 2, p. 1907; Ibn Majah, vol. 2, p. 523-524; ibn Abd al-Birr, vol. 4, p. 1794
- ↑ Muslim ibn al-Hajjaj, vol. 2, p. 1907-1908
- ↑ Al-Kulayni, vol. 2, p. 405; Ibn Babawayh, p. 76
- ↑ Ahmad ibn Hanbal, vol. 2, p. 421; al-Tabarani, vol. 25, p. 87-91; Ibn Majah, vol. 2, p. 1107
- ↑ Ibn Hajar, vol. 12, p. 459
- ↑ al-Tabarani, vol. 25, p. 86; quoted from Zuhri.
- ↑ Ibn Sa`d, vol. 8, p. 226
- ↑ al-Tabarani, vol. 25, p. 86; Al-Dhahabi, vol.2, p. 227